← Book details Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 60

Sashe 36

Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Daman ai ku na dade da ganowa bakwa kaunata.. Kune masu kushe ni a duk sanda yan kwamitin sarki zasu ce wa za bawa rikon kwarya..kunfi haba habaa da Muhammd saboda shi yanada kudi... Yanada tarin dukiya da yake sammuku. Domin kudin kaji ne sai da tsaba. S....

Bappah Maher bai bari Kawu Adamu ya karasa magana ba yadaga hannu ya zabga masa mari.. ya sake daga hannu ya sharara masa a a daya kuncin sa.. hannun sa da jikin sa suka hau rawa yana nuna Kawu Adamu yace,

"Kunji dan iskan yaron nan ko? Ku ku ka haife mu ko mu muka haife ku da zaka tsaya kana gaya mun wadannan maganganun? Idan baka sani ba ka sani yau... Mu ke kokarin fado halayen ka masu kyau muna fadawa kwamitin sarki... Kaf kandemi kowa hakuri yake da halayen ka.. an gaya maka labari bai zo mana ba kana sayar da hatsin masarauta? Ko kuwa dokuna takwas rannan da aka wayi gari babu su ba kai bane? Komai yana dawo mana kunnuwan mu... Ga securities can awaje an gama interrogating dinsu zamu sbjgo muna jiyowa suna cewa kai ne ka biya su kudi da safe kache su bar sashen gaba daya baki na alfarma zasu wuce da dakarun su na presidency don haka an basu awa uku suje su huta... Saboda zaka saka a sace Amaal? Saboda haka ka shiga taitayin ka.. sanyi nayi wallahi. Ka tanbayi wanene maheeru kandemi zaa gaya maka sanda nayi tashen samartaka ta ma ca ake mun mutum me karfin mutane hudu da rabin mutum.. doki bakayi nauyin banza ba.. 'bab'balla mutane nake idan akayi mun shirme... Don haka Ina Amaal?

"Assalamu alimumm sir my apologies.. ga cctv footage din wajen garden din anciro...", Wani maaikaci ya shiga parlorn ya bada wani harddisk ya fita...

"Ina Amaal nache?" Bappah maheer ya sake dakawa Kawu Adamu tsawa

"Tana tsaunin zagayen makarantar mata dake karshen lungun wadawa na unguwar balbelu...."😭

"Kaji bakin mugun ko? Kunji unguwar da take ma? Kai Adamu bakada Imani. Wallahi wallahi baka da Imani. Makarangar matan da ke unguwar balbelu din tun yaushe gwamnati ma tache a dena amfani da makarantar saboda miyagun da ake tunanin suna bibiyar ta da yn shaye-shaye.... " Bappah maheer ya fada yana girgiza kai cike da takaicin Adamun

"Gaskia na kara tabbatarwa ba Allah a ranka... Allah ubangiji ya kyauta..  ka guji bakin duniya. Adduar Wanda aka zalunta wallahi batada hijabi da Allah . Yarinyar nan hakin ta na cutar da ita da kayi wallahi Allah ba zai taba barin kaba.." bappah usayni ya fada yana girgiza kai.

"Nima Kuna nuna mun kiyayya ai... Daman tinda nazo doron duniya nasan bakwa kaunata.. Don haka maganganun ku basa damuna... " Ya kasa kai zai fuce. Dss din sake tsaron kofar sika sake bude kafafun su.

Bappah maheer ya kira sunan sa da karfi,

"Ba magana ake maka ba ne... Wallahi Ina mai tabbatar maka idan aka dakko yarinyar nan akaga an mata wani abun na illa na rantse da kadaitar ubangiji Adamu sai kayi dana sanin samuwar kanka a zuriyar kandemi .."

Kawu Adamu yayi murmushi... Ya nemi gefen stand na tv ya zauna, Cikin muryar ko ajikina dinnan yache,

"Ko kanada masaniyar tsananin kiyayyar da kuke nuna mun che yasa dukkanin ku kuma nabi na toshe wasu ababen farin cikin ... ku kuka fara kamar yadda kuke da hannu a hanewar sarautar da nake da gadon ta .. Bappah maheer ko ka tuno wata kwangila ta mambila da zaka samu miliyoyi kanata murna daga baya aka hanaka aka bawa aminin ka? Ni ne silar hanaka.. Bappah usayni Ina gidajen da akace gwanmati ta bawa ku tsofaffin maaikata Kai da abokan aikin ka gidajen Ikeja da ke Lagos? Ai kaga daga baya aka cure sunan ka aka kore kama ma daga masu karban pension... Bakowa bane sila ni ne nan.. Bappah Hassan aikin da zakaje embassy na Ecuador bakowa bane ya hana asa maka hannu a takardar tafiyar fache ni... Wadannan kadan ne daga cikin abubuwan danayi na ramako akan muguntar da kuma kuka mun kuke kan yi mun..."

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Adamu! Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Daman ance makashin ka na g* ka . Allah ubangiji ya kyauta.. "

"Kwarai kuwa... Rama cuta ce ga macuci... Kunmin na muku... Da da ran iyayen mu duk haka ba zata faru ba... ai kamar jalaludden ne... Dana dinga amfani da na'ura mai kimiyya Ina sanya nasa kiyayyar dan uwan sa a ransa.. Baya kaunar sarauta amman na dage na dinga tura masa sakonni masu jan raayi har ya amince.. da niyyar sanya zazzafar kiyayyar idan tayi tasiri ku kwamktin saka sarki zakuu tsaidani a sarautar kujerar Nukaa amman kuka ki.. Da hanyoyi na bi na saka aka saka hannu akayi stamp amatsayin junaidu ne yasa aka zartar aka hana jalaludden babban mukamin da yakeso na matemakin shugaban kasa... Tun daga nan na fara saka kiyayya a tsakanin su.. Na kuma koma kan junaidu shima, Na sanya aka kara masa wa'adi aka ki dawo da shi Nigeria, Ina kuma tura masa sakonni masu tsoratarwar amman shi ban gama nuna masa jalaludden bane sai dana bari ya dawo Nukaa gaba daya. alokacin dana saka aka dauke yaran sa acan kasar na awanni nayi hakane da...

"Dakata hakanan Adamu na tabbatar kai din BAKON MUNAFIKI ne Kai din Kuma BANA MUTUM DAYA BANE... Kana bin kowa na cikin mu kana cin dudduniyar sa kana kuma saka kiyayyar juna a tsakanin yan uwa.. Dan uwan ka ma baka barshi ba da kuka fito ciki daya ballantana mu da kuma yayan yan uwan ka.. "

"Kwarai.. ko matan gasunan ni ke raba kansu dik dan su bujire junaidu kar ya waiwayo kasar ma amman ya dawo. Ban kuma dena dinba na cigaba fiye da abaya ma.. " yakara sa fada yana nuni da su Hajiya Hadiza

"Musanman ke da ke bada gundunmuwa sosai... Duk da dai tun kafin na fara turo sakonni dama can bakya kaunar jamila..kuma kin amince a salwantar da rayuwar Amaal din.. junaidu ko ka tuno sanda kake gaya mana ka bawa Hamid gashinan ragamar asusun bankin kandemi? ... A ranar na kara tabbatarwa da sai na illata zuriyar ka da mafi soyuwar abunda ke ranka tunda naga alama ka bada himma sosai kana kuma kaunar abunda nake muradin son samu.."

"Ya isa dakata.... Illa ce kayiwa kowannen mu kai da Allah mahallicin ka. Yanzu dai muje a dakko yarinyar nan daga nan Kuma sai a yanke maka hukunci dai dai da Kai" bappah maheer ya fada hadi da saka hannu ya janyo Kawu Adamu da karfi ya tura shi awajen kofar fita, ya dubi yan parlorn yace,

"Ina masu motoci a kusa? Muje ko"

Al-mustapha ya tashi da sauri .... Hakama Aayan daya mike shima ya bi bayan Bappah maheer. Sai sauran bappanin na su suka dunguma sukai waje. Hamid da Hajiya jamila ma wajen sukai. Ta shiga gaban motar hamid da sauri..

Motoci suka shisshiga aka chusa keyar Kawu Adamu agaban mota. Suka tafu a jere kusan motoci bakwai suka dauki titi, A convoy zuwa inda amaal take a boye....

Parlor ya zama sai Hajiya Maryam da Alhaji Alkali Muhamamd da su Bappah Abdullahi, Haj Aisha matar Alhaji Abubakhar mahaifin Hisham, da Hisham din kansa, da su Hajiya hadiza daketa raba idanu musanman datasan ta bada gudunmuwa na kason lefi a dauke Amaal... Sai jimami suke... Tu'ajjabin maganganun da Kawu Adamu ya fayyace ya bayyana a fuskokin su cike da dimbin tarin mamaki marar misaltuwa..

============

Har bakin kofar makarantar suka faffaka motocin... Kallo daya zakai wa makarantar ka tabbatar ta zama fankoo (unwanted building) Ga juji nan a gefe an mayar da wajen reshen zuba shara...

_ADVERT👇_

_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*

_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥
[9/18, 5:43 PM] Hafsaat💞: _BAKON MUNAFIKI_
_(BA NA MUTUM DAYA BA NE)_

_NA:_

_NANA HAFSATU_

_PAGE: 36_

_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._

___

 Maryaam-Amaal na cikin ajin makarantar data zama kango kuma mafakar yan shaye shaye da zuba shara.

Wani aji ne aka kulle ta aciki akan wata yarkacacciyar kujera...Ba komai acikin sa sai kwalaban shaye-shaye da ledoji na datti da wani kare a yashe a gefe an daure shi da igiya. Kamar yunwa zata kashe shi saboda tsabar ramar sa..

Hawaye ne suke gangara ta kyakkyawar fuskar ta... Cikin zuciyar ta take nanata,

"La'ilaha Illa Anta Subahanaka Inniy Kuntu Minaz Zalimeen.."
Chapter 36 · 0% Book details