← Book details Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 60

Sashe 23

Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dan allah ya isa haka.....Ban taba tanka muku ba sai yau. Ku dai na aibata ni akan abunda bakuda masaniya akai. Yaya aayan first cousin din mu ne haka Kuma Yaya Hisham dan babban aminin abbiey ne dika cikin su ba Wanda muke wata alaka fyace ta Yan uwantaka..Kuma su sika fara nema na ba ni nake musu magana ba. Yaya Al-mustapha da kuke ta kamo sunan sa kuma ko sanin sa ban ba. Ina dai jin sunan sa.. sai wannan zuwan na su ku tambaye su ku ji..Sai wadanne mazan kuma? Dan Allah respect yourselves... Dan Allah na roke ku"

"Ahh iyye..Yaya Hindu kinaji? Ah alle yarinya ta zama ishasshiya"

"Baki ga ma na kasa mayar mata ba? Ai mamaki ne ya cika ni... Kinsanmace idan ta fara sanin maza."

Amaal data juya zata kwanta sai ta fasa. Saboda maganr Hindu ta bata mata rai,

"Haba Yaya Hindu... Gaskia karki sake gayamun wannan maganar."

"Ke ni kike cewa gaskia kar na sake abu?" Tayo kanta zata mare ta.

Amaal ta mike da sauri ta goche,

"Ba magana na gaya miki ba Yaya... Amma ki duba kiga abunda kika ce mun fa"

"To karya nauo?"

"Yo gaskia ni ba haka nake ba.. Allah shahidi"

"Kai Kai Kai wallahi yarinyar nan idanun ta sun bude. Ke kinsan me kike fada kuwa?" Ikram ta fada tana tafa hannuwa.

Hindu ta sake kai hannu zata daketa amaal ta goche...

"Yar iskar kawai..."

"Yaya Hindu... Ina girmama ku duka... Zan iya tabbatarwa kuma kun sani bantaba musayar yawu da ku ba. Amma cin fuskar da kuke akai na yayi yawa. Wadannan maganganun da kuke ta fada dik wanda aka gayawa acikin ku sai inda karfin sa ya karl e. Musanman idan kagaggen zance ne akan ka ba gaskiya bane.."

"Wa ke miki karyar?"

Amaal bata sake cewa komai ba. Ta haye kan gado ta kwanta taja bargo hadi da kashe bed side lamp dake gefen drawer din jikin gadon ta.

"Zan koya miki hankali.... Duk karatun da kika zubar zaki kwashe ki mayar kan ki marar kunya futsararriya."

Amaal na jinsu ta bargo ta sake ja ta lullube kanta.. Ta na jiyo su sunata mayar da zancen suna zagin ta bata sake bi takan su ba . Bacci ya dauke tah..

_______-----------_______------------_______

Da ke mid semester break suke yi... Hakan yasa tana tashi daga bacci ta nufi sashen mahaifiyar ta.

A parlor ta tarar da ita tana shafa kulaccam kamshi ya gauraye ciki da wajen sa.

"Hayateey barka da safiya"

"Barkan mu dai habity... Kin tashi lafiya?"

"Alhamdulillah...... Hayateey kinji kamshi kuwa.. Allah na dauka turaren wuta aka saka."

"Kadan ma fa wai nake lakuta na shafa.. Kulaccam din kayan turaren yerwa incense and more (08095215215) ne .. kinsan kayanta na da kyau ba algus."

"Gaskia kayanta nada kyau Allah kaman kamfanin haramein oud da kin shigo sai kamshin oud"

"Eh ai oudi scent ce wannan... Gashi a rubuce "oud oudi kulaccam by yerwa incense and more..."

"Ma shaa Allah... Ta fruity scent dinma kadan na shafa kaman ka lashe jikin ka wallahi me kamshin vanilla dinnan da strawberry "

"Kya lasowa kanki asibiti kuwa"

Suka tuntsire da dariya gaba daya..

"Ina Yaya Hamid?"

"Ya tafi office ... Tun sassafe"

"Allah sarki Yaya.. Allah ya temaka Amin"

"Aamin Aamin"

"Kinje kin gayda Hajiya?"

"A'ah..."

"Hajiyan taki kuma yau?"

"Wannan Yaya Al-mustapha dinne ya tsaneni Hayateey.kuma kullum yana can."

"Ki dena cewa an tsane ki ba kyau. Bai tsane ki ba. Shi mutum ne kawai marar kwaramniya.. Batun kullum kina ganin sa acan kuma ita ta yaye shi. Yafu shakuwa da ita akan iyayen sa. Dan ko komawar su waje dakyar yabi su sai da akayi da gaske.."

"Hayateey kinsan me ya yace akai na jiya?",

"A'ah...."

"Ana hira da su Hajiya da Yaa Aayan sai can wai Ina kallon sa shi bayason kallo..."

"To ke meye na kallon sa uhm?"

"Allah Hayateey bakisan da yanayin daya bafada ba..Kuma shi ya fara kallo na ina daga kai muka hada ido.. sai kuma yace banda kunya... Wai akan menene ma yauwa akan yana nunawa Hajiya saban office dinsa a laptop. Hajiya tace nagani? nace nagani."

"Bakyau yiwa babba rashin kunya. Nasan dai ba halin ki bane. An kuma sheda bakya yi. Aman dai bana nan akayi wannan don haka bazan tabbatar da kinyi masa ba ko ba kiyii ba"

"Allah ki tanbayi Yaya aayan shine ma yai ta ban hakuri da zan shigo wajen ki sai kawai na wucs bangaren mu. Inata kuka fa. Naje can ma kuma suka taru akai na suna gasamun magnganu marasa dadi ... Yau dai na kasa hakuri nache banaso su dena mun"

Hajiya jamila ta dan daga Kai ta kalleta sai kuma ta saukar da shi kan robar kulaccam fdn hannunta tana dubawa tace,

"Allah ya kyauta.... Nide na gaya miki ba sa'oinki bane... Ki dena bi ta kan duk abubuwan da zasu biki da shi"

"Har fa mari na ya Hindu zatai ... Sunata fadar magana maza maza.. Ina kulaa maza waye waye. Walahi Hayateey ko a school bana bi ta kan course mates dinmu mazan. Anan gidah Yaya ayaan ne shima kuma shike kira na awaya ko chat . Sai Yaya Hisham wallahi shima shi ya karbi number na ai na gaya miki tun Ina ssce yana coaching dina wasu abubuwan..Yaya Al-mustapha dinnan kuwa wlh bansan shi ba. Na san dai sunan sa"

"Allah ya rufa asiri... Ni dai na gaya miki a ko'ina kike ki tsare nutincin kan ki ... Baki da muharraami sai wanda kuka fito tsatso daya...Allah ya cigaba da kare ki ya tsare miki mutuncin ki har gaban abadan"

"Allahumma Aameen Hayateey.."

"Bari na duba Hajiya"

"To sai kin dawo. Ki gayshe ta"

"Tohm"

Fita tayi... Wata bakar mota ce ta fita daga sashen kakan su. Mutanen nan biyu na rannan wadanda take da tabbacin likitoci suka fita daga bangaren..

Gabanta ya tsananta bugawa. Ta waiwaya sashen hajiyan sai kuma ta mike wajen kakan na su tanata waiwaye waiwaye..

Shiru ba kowa kamar rannan... Ta karasa bude kofar dakin a hankali. Tayi mamakin data ganshi akwance idanun sa a abude.

"Kakaaaa..Assalamu alaikum..." Tayi har sau uku bai ce komai ba.

Ya kasaa magana yayinda yaketa Mata nuni da idanu ta Karin ruwan dake shiga hannun sa.

Da sauri ta karasa kusa da shi idanun ta taf da hawaye. Hanun ta na rawa ta bude drawer dataga rannan sun saka allurar nan. Ta dakko da sauri ta saka wata leda data gani a gefen gadon.

"Sannu kaka..."

Hawaye na zuba a idanun ta. Haka shima nasa idanun sunata kwaranya. Dik nunin da yake mata da idanu na karin ruwan ta kasa fahimta..

'idanun ka ne ke ciwo?" Ya lumshe idanun ya bude

Dakyar ya jya fitar da harshen sa dake masa zafi da radadi da nauyi ya karkata shi yana mata nuni da Karin ruwan.

Jikin ta na rawa ta daga Kai ta kallo ruwan. Wasu abubuwu ne acikin sa, Nan da nan ta zare masa ta cire ruwan ta saka a wannan ledar.

Da sauri ta bude kofar ta fice da ledar a hannun ta... A kofar gate din bangaren ta hadu da Bappah Nuraddeen da Bappah Jalaludden da Aayaan da kuma Al-mustapha zasu shiga ita Kuma zata fita...

_ADVERT👇_

_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*

_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥
[9/5, 9:49 PM] Hafsaat💞: _BM_

_NA:_

_NANA HAFSATU_

_PAGE: 25_

_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._

___

Jaa tayi baya da sauri... Ta tsugunna akan ledar..

"Barkan ku da safiya...." Ta fada hannun ta a kasan ta tana mai chusa ledar...

"Barkan mu dai.... Mai sunan Hajiya" Bappah Nuraddeen ya fada fuskar sa kumshe da murmushi marar misaltuwa.

"Na'am Bappah..."

"Favorite cousin sissy.."

"Yaya Aayaan.."

Bappah Jalaludden yayi gaba abun sa Al-mustapha ma bai bi ta kan ta ba yabi bayan mahaifin sa.

"Babaa kika zo dubawa ne? Sannu da kokari."

"Eh....Amma ban ma ganshi ba"

"Sannu angode.... Allah yayi albarka"

"Aameen Bappah"

Sai data ga sun shige cikin gidan sannan ta mike ta dau ledar da sauri ta fiche.

Gabanta na tsananta bugawa ta wuce sashen mahaifiyar ta. Bakin ta dauke da sallama ta shiga...

"Hayateey...."

"Bata nan Amaal."

"Sannu da aiki iya..."

"Yauwa Amaal.. Ga abinci can kan dinning"

"Tohm iya.. Nagode"

Sama ta hau da sauri..... Dakin da yake a matsayin nata wanda ba kwana take ba ta shiga. Ta ajiye ledar ta bude da allurori a kwali da sirinji da wasu ruwan allurorin , Gefe daya kuma ruwan karin ruwan ne shima aciki bakikkirin da wasu abubuwa acikin sa da karare...

Tsayawa tayi tana bin su da kallo...Ta sauke nannauyar ajiyar tana cije kasan leban ta.
Chapter 23 · 0% Book details