← Book details Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 60

Sashe 57

Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Akan me zan ke bibiyar ki Hindu...? Ina tunanin wannan shine karo na farko a rayuwata da magana ta fatar baki ta taba hadamu.... Amaal na kawo tanada lectures, An rasa direbobi kowanne yanada aiki... Menene hujjar biyo ki fisabilillahi kema inde ba zuciya da kika biyewa ba, Mai sake sake akan wani dalili gotai gotai da ni zan dinga bibiyar ki, Meye hadani da ke Hindu? Kamar wanda suka saba da har haka zata shiga tsakanin su?look! Abu na biyu wucewa nazo yi zan koma gidah sa sauketa da nayi kenan na taho kan titin nan na hangi bayan mace da namiji kamar suna fada dubada yadda ta baya naga yana watsa hannu yana nuni da yatsa... Macece tanada rauni kuma zubar da mutunci ne ace mace budurwa baliga suna sa'insa da namiji a bainar jama'a akan titi...."

"Toh Ina ruwan ka? Ba sai ka wuce ka tafi ba? Da kai akeyi? Wannan ai shisshigi ne da kankanba... Sai kayi wucewar ka kama hanyar ka na meye zaka tsaya har ka tako kafafu kazo saboda tsabar gulma....?"

Hamid ya sauke katuwar ajiyar zuciya ya sake gyara tsgunnen da yayi yace da ita,

"Koma meye hada ku kiyi hakuri... A matsayin ki na mace be dace kizo nan ki tsugunna kina zubar da hawaye akan wani da namiji ba, Shawarar da zan baki a matsayina na namiji shine ki dena zubar da hawayen ki akan namiji. Duk namijin dayaga kin damu dashi fiye da yadda ya damu dake Allah wulakanci zaki ta gani kala kala...."

"Toh Ina ruwan ka?"

"Shawara ta rage ga mai shiga rijiya hindatullah... Na bar ki lafiya"

"Dan shisshigi kawai"

"Allah ya baki hakuri... Kiyi hakuri ki yafemun shisshigi na ne yaja mun kam.. Amma fa ni haka nake bana gani nayi shiru"

Mtscew... Hindu taja tsaki tana tabe baki.. Hamid ya mike daga gurfanen da yayi ya nufi motar ya shiga ya tafi. Hindu tabi bayan motar da kallo tana hararar ta, Tamkar itace ta mata lefin...

"Dan Allah ki fita daga rayuwata wai ana dole ne? Wallahi bana son ki, Ba zan taba son ki ba. Karki kara kuskura ki zo waje na kina mace sam baki da class ba kida kamun Kai. Ki sani ke din bakya cikin jerin irin matan da ni Habibi Talba nake so... Wallahi da nayi soyayya dake ko auren ki gwara na mutu ba aure akai na kinji Allah ... Kuma wannan rana ta zama itace ta karshe da zaki sake zuwa ki neme ni Allah idan kika sake ko kika kirani a waya sai na zo wajen mahaifan ki na gaya musu su ja miki kunne ki fita a harkata.. Dumbass " ta shiga tunano kalaman da Habibi Talba ya gaya mata tana runtse idanu hawaye masu dumi suka shiga zuba daga idanun nata.

Jikinta duk ya mutu... Ji take inama a dauki ranta ta mutu kawai a lokacin saboda tsananin duniyar data mata zafi shikenan itada Habibi Talba ba haske ? Ba zatayi soyayya dashi ba kenan har ta kai ga sunyi aure?

"Wayyo Allah na" ta fada tana hawaye sosai..

Kiran direba ne ya shigo wayar ta ta dauka ya sheda mata da yana bakin department yana jiran ta...

Sai data sake bude sabon wani shafin kukan tayi mai isar ta, kafin ta katse hawayen ta ta nufi motar ta shiga yaja su suka koma gidah

Hamid yana tafiya a mota yana dariya. Shi gaba daya ma Hindun dariya take ba shi. Gefe daya Kuma maduakakin tausayin ta ne ya kama shi... Tabbas Habibi Talba bai kamata ya dinga wulakanta ta ba tunda tana kaunar sa... Akace ka so me son ka.. sannu a hankali sai ya bita da sigar lallashi ya rabu da ita cikin ruwan sanyi...Amma hayaniya da hargagiya sam babu dadi... Ita kuma yakamata ace ta san itadin macece akwai limit dinta. Babu namijin dake son mace marar kamun kai da bibiyar diddigi.. Son ma so wani sam bashi da dadi. Ka so a so ka shine magana.... Na turawa sukance one sided love/ unrequited love....

_______

*MARYAAM-AMAAL*

Central mosque suka je suka yi sallah, Sannan suka koma theatre don halartar dayar lectures din data rage musu..

Lectures din was boring... Gaba daya ba dadi. Wasu daga cikin daliban hira kawai suke, Wasu na ciye ciye, wasun su kuma mafi yawa bacci suke yi... Yayin da wasu ke ta latse latsen wayar su. Amaal na daga zaune tana jujjuya wayar hannun ta. kawayen ta kuma sun kifa kan su akan benci suna bacci...

Tunanin ta ya lula duniyar Al-mustapha... Idanuwan ta Al-mustapha kawai suke so su gani, Kunnuwanta daddaad'ar maganar sa kawai suke so su ji, Gangar jikin ta na son kasancewa da shi... Zuciyar ta na bugun rashin sa akusa da ita... Ran ta na kewar sa..

Message ta shiga ta rubuta masa sako da,

"Habiby...♥️Fatan kana lafiya? Ka ci abinci kuwa? Ina class lectures din very boring...Ina son ka. Ka kula min da kanka. kasantuwar mu a raye cikin ruhi guda d’aya ya sanya zuciyoyin mu bugawa cikin lokuta makamanta juna.. Honey bunny na♥️ Ina nan zaune cikin class amma zuciya ta tana tare da kai. Kai ne kawai nake gani na ji sanyi a cikinta. Ina nan ina jiran dawowar ka nayi kewar ka sosai..."

Tana gama tura masa ta shiga gallery. Hotunan su kawai ta shiga kalla tana zooming fuskar Al-mustapha... Murmushin fuskar ta sai fadaaada yake yi.

"Banza uwar son miji...." Cewar Zaarah kawarta da ta tashi daga kwanciyar da take ta leka tana kallon Amaal na zooming fuskar Al-mustapha.

Amaal tayi dariya kasa kasa kar malamin su ya jiyo su tace,

"Ai ba haram bane... Halaliyata nake kallo.. Nayi missing dinsa ne ba zaki gane ba"

"Kwata kwata fa 2 to 4... 4 to 6 ne damu amma wannan awoyin kadan har kinyi missing dinsa? Sannu Juliet matar Romeo"

"Ke... Ba zaki gane ba ne... Amma duk second daya sai na tuno Habibi na... Ina kaunar sa fiye da yadda kalamai da baki zasu bayyana miki..."

"Matsalar ku ce"

"Ahhh! No vex mana.. Zaki shiga daga ciki keda Uthman zaki bamu labarin zallar kauna"

Zaarah ta tabe baki tana yamutsa fuska... Suka fashe da dariya baki daya..

Al-mustapha na zaune a ofishin sa yana danna na'urar me kwakwalwa ta computer da ke gaban sa. Karar shigowar sako ya shigo wayar sa.. Janyo ta yayi ganin Amaal ce wadda ta turo hakan yasa shi yin murmushi tun kafin ma ya karanta.. Ya kwantar da kansa ajikin kujerar ya bude sakon yana karantawa yana lumshe idanu hadi da sakin tattausan murmushi, Yaja kasan leben sa yana hango hotan fuskar ta a zuciyar sa...

Sai da ya maimaita sakon data turo sau shida, yana yi yana komawa farko yana tisawa kamar wata hadda... Tukun sannan ya mayar mata da reply,

"Habibty.... My whole world ♥️♥️ Alhamdulillah, Na ci baby na, wani snacks bar aka bude kusa da office... My poor baby.. Allah yabada sa'ar karatu kinji? I love and miss you soo much...Tausayi da tausasawa su ake kira “so” kowa yana da wacce yake so, Ni ke nake so.... Na ke kuma kauna fiye da kalmomi... Da akwai miliyoyin furanni a cikin lambun masoya a wannan duniya. Da a ce zan tsunko kowanne fure na baki shi a hannunki, hakan bai isa ya bayyanar da adadin yadda nake son ki ba...Ke ce murmushi na, kuma ke ce farin-ciki na. Ina kaunar ki sosai...Zan zo na dauke ki da kai na mun karasa meeting din Ina compiling details dinne kawai.."

Tana daga wayar ta taga reply din sa.. Nan da nan ta karanta tana murmushi...Ta manna wayar a kirjin ta tana lumshe idanu hadi da sauke zuciya... Farin ciki ya bayyana a fuskar ta ji take inama yana kusa da ita kawai...

Lecturer din yana gama lectures dinsa ya fita... Daliban kowa ya dinga hamdala saboda baki daya babu dadi lakcar ranar...

Suna zaune da su Zaarah su ma kafin direbobin su suzo daukar su. Chan sai ga tunkarowar motar Al-mustapha department din na su..

A hankali ya karasa parking motar ya bude ya fita... Tana ganin sa ta mike ya nufeta da sauri yana murmushi, daliban nata kallon su suna admiring din su.

"Ina wuni?" Su Zaarah suka hada baki wajen gayshe shi

"Alhamdulillah... Sannun ku...muje ko love?"

"Yeah... Bye!! Ladies" Amaal ta daga musu hannu tana musu gwalo suna dariya.

Bude mata gaban motar yayi ta shiga, daliban kowa nata,

"Awwwwwnnnn"

Sannan ya koma mazaunin sa ya zauna ya tashi motar bakin sa dauke da addua,

"Sannu Baby love..."

"Sannun mu Boothang"

"Me kike so ki ci yanzu?"

"A koshe na ke"

"Banason musu... Abincin school me ze miki? Bari mu karasa la comida corner sai muyi takeaway"

"Tohm..Allah ya saka maka da alkhairi ya kara maka budi me albarka"

"Aameen zumaa taa"

Yar dariyar data rike ta saki sosai tana kallon sa,

"Bana ce ka dena fadar sunan nan ba? Haba baby"

"Akan me zan dai na fada? Ai banyi karya ba, Ke kin ma fi zumar... Allah dai ya karawa daadi daadi"

Amaal ta rufe fuskar ta da tafukan hannuwan ta.. duk sanda ya fadi haka kunya ce take mata dabaibayi..

Haka dai suka cigaba da tafiya a motar suna hirarrakin su na soyayya kamar wasu saurayi da budurwa.. Daga nan suka biya wajen sayar da abincin sukayi ordering favorites din su suka kaama hanyar gidah..

Amaal ta dube shi tana rau rau da idanu, duk sanda dama take son wani abun da haka take farawa,

Ya dubeta yana gimtse dariyar data taho mai, Yasan abunda zata fada... Yace,

"Ya akai? Uhm? Waya taba mun rabin rai na?"

"Kai ne mana..."

"Ni kuma? Da nayi me lover?" Ya tambayeta cike da kulawa.

Ya gangara bakin titi yayi parking motar, Ya juya baaki daya yana fuskantar ta ya sake cewa,

"I'm all ears.... Banason fushin ki Boo, Meya faru? Uhm? Menayi? Uhmmm?"

Tana lankwasa hannuwanta cike da turo bakin ta gaba cikin shagwaba tace,

"Ka 'ki ka kai ni gidan Yaya Yusra, Ta zazzo ita har tace tayi fushi mun ki zuwa... Kace zaka kai ni, ko yaushe idan na maka magana, sai kace abari sai gobe, sai jibi ranakun nata wucewa"
Chapter 57 · 0% Book details