← Book details Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 60

Sashe 32

Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai take ganin tamkar ana biye da ita a baya saboda inuwar da take gani ta gefen ta... Da ta waiwaya kuma sai taga ba kowa..

Ta dakko wayar ta da niyar kiran Hayateey kuma unfortunately ba service..

Wani hayaki ta fara ganin yana dosar inda take marar dadin shaka... Yana kuma hawa mata kai don tuni idanuwan ta suka fara kawo ruwan hawaye..

Nan da nan jiri ya fara daukar ta.... Ta fara ganin dishi dishin inuwar wasu mata sun doso inda take ga kuma wata mota data taho wajen su

Kokarin komawa take amman ta kasa saboda jikin ta ba karfi..... Tana jiyo hannuwan su a jikin ta suka chusa ta acikin motar...

Daga nan bata sake sanin inda kanta yake ba... Sai farkawa tayi ta ganta akan wata kujera an kulle mata hannuwan ta ta baya sai zugi sike.. kafafunta ma an harde su waje daya an kulle.. hakama bakin da aka nane mata shi da wani abu mai danko..

Kokarin kwance kanta take tana mutsu mutsu ta kasa...gashi duk maganar da take a banza a rufe bakin yake ruf.. ambaliyar hawaye suka fara kwarara daga idanun nata..

*KANDEM ESTATE.....*

Yana zaune a faada anata faadanci wayar sa dake gefen sa tayi haske... Tamkar ba zai dauka ba sai ganin duk yan uwan ne a dabaibaye ba bare hakan ya sa ya janyo wayar tasa kasa kasa... Yafara dubawa...sako ne ya shigo ciki na,

"Na hane ka da waiwayowa kasar gaba daya kaa ki.... Daka dawo ma nache kar ka zauna a kandemi nanma kaki amincewa ka zauna.... Ka kuma amince aka baka abu mafi soyuwa agareni na sarautar birnin Nukaa.. Daman na gaya maka a baya... Sai kayi dana sanin dawowa Nukaa... Tabbas a yau dinnan wani abu mafi soyuwa a gareka ya bar ka kenan har gaban abadan...... "

Yana karasa karantawa ya mike.... Fadawan sa sukabi bayan sa ana tambayar lafiya ya dakatar da su...har ya nufi sashen Hajiya sai kuma ya fasa zuciyar sa na tabbatar masa da ya duba inda yake waswasi akai..

Sashen Hajiya jamila yaje... Tana tsaye zata futo kenan suka hadu.. ta rissina ta gayshe shi cikin kulawa ya amsa,

"Ina zaki?"

"Zan dubo yarinyar nan ne da kai na na aika iya bata sashen su nasa anje islamiya nan ma bata nan..."

Hannun ta ya kama ya shigar da ita cikin parlorn ta....

"Sun dauke ta ko? Sun sache mun amaal ko? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun"

"Ba wanda ya isa ya sache ta, bar kuka" ya fada yana kwantar mata da hankali,

Ta ture hannun sa tana kuka sosai tamkar karamar yarinya tache,

"Ka gaya mun abunda ka sani... Junaidu"

Yadda ta fado sunan sa gatsal ba wasali yasan tana cikin wani hali. Ya sake rarumo hannunta cikin kulawa yace,

"BAKON MUNAFIKI ne..... Tabbas BANA MUTUM DAYA BANE.... Bansan su wa da wa yake hulda ba... Kai bansan ma ko mace bache... Kowa suspect ne.. fatana Allah yasa tana cikin aminci... Ki share hawayen ki Amaal zata dawo lafiya cikin kwanciyar hankali da nutsuwa..."

"Idan suka mata wani abun fa?.. Ina nufin idan aka b....

"Karki karasa m... In shaa Allahu rabbi Allah ba zai bada galaba ba... Kalau zata dawo cikin amincin sa da kulawar sa."

"Toh Allah ya amince..."

"Allahumma Aameen"

Tashi yayi Hajiya jamila itama ta mike tana cewa da shi,

"Zan bika.."

"Faadar zaki bini?"

Ta girgiza kanta tana lankwasa hannuwa.. ambaliyar hawaye na zuba tache,

"Ya maganar amaal to...?"

"Jamila ki kwantar da hankalin ki dan Allah... Zanyi duk mai yiwuwa ganin Amaal ta dawo gidah" ya karasa fada yana dafe da kafadar ta cikin kulawa da ban hakuri...

Fita yayi ya nufi sashen Hajiyan su... Daman jikin sa ya bashi ba Hajiya ko baba aka aiwatar da mugun nufi akan su ba.daman yafi tunanin ko amaal da Jamila matar ta sa..

Yana shiga ya tarar da hajiyan da baba suna zaune da alama sun gama karya karin kumallo ne.. ya durkusa ya gayshe su cikin girmamawa... Yayi matukar mamaki da ya jiyo mahaifin nasa yace da shi,

"Alhamdulillah junaidu...."

Da sauri ya daga kai ya dube shi...

"Baba bakin ka ya bude?"

"Dama baki na a bude yake.. amman ba wanda ya sani sai mahaifiyar ku... Da kuma Maryam yar wajen ka.. yarinyar da Allah ya temaka ta ceto ni daga miyayun da ke son halaka ni..."

Hawaye suka cika idanun sarki junaid ya tuno Amaal dai an saceta bai san sanda yace,

"Baba... Sun dauke Amaal.... Sun dauke mai sunan Hajiya..."

Alhaji Muhammad ya daga kai da sauri ya bude baki zaiyi magana Alhaji jalaludden ya shiga parlorn yana gayshe da su .. ya daga masa kai kawai hade da kakaro murmushi,

Sarki junaid yayi shiru... Abunda ya faru alokacin ya sake daure masa kai.. to meyasa baba bai bude bakinsa agaban yaya jalaludden ba?

Kenan mahaifin na su ma ya gano jalaludden shine bakin mugun BAKON MUNAFIKIn da BANA MUTUM DAYA BANE dake assassa tuggu da makirci da mugunta a zuriyar Ardo kandemi?

___

#Ya labarin Amaal?su waye suka sache Maryaam Amaal??? ...
# BAKON MUNAFIKI....
(BA NA MUTUM DAYA BANE)
#A love Soo pure 💞
Love conquers All❗

_ADVERT👇_

_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*

_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥
[9/14, 9:03 PM] Hafsaat💞: _BAKON MUNAFIKI_
_(BA NA MUTUM DAYA BA NE)_

_NA:_

_NANA HAFSATU_

_PAGE: 32_

_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._

___

"Yaya! Barka da safiya ........" Sarki Junaid ya danne zuciyar sa ya gayshe da yayan nasa cikin ladabi duk kuwa da tsantsar bacin ran da ke lode a ransa..

Jalaludden ko kallo Junaid bai ishe shi ba... Ya cigaba da danna wayar da ke hannun sa kawai yana mai gyara zaman gilashin dake sakale a fuskar sa..

Hajiya Maryam ta juya ta kalli mai gidan nata Alhaji Muhammad da shi din ma ita yake kallo...

Gyaran murya tayi ta dan dagaata yadda kowannen su zai jiyo ta sosai tace,

"Bappana..... Bakaji yana gayshe ka ba ne?" Hajiya Maryam tache da Hon.. Jalaludden.

Ya dan juya ya fuskance ta yana gyada kai yace,

"Ya rike gaisuwar sa Hajiya...."

"Bangane ya rike gaisuwar sa ba? Wai kai dan Allah me yake damun ka ne? Menene hakan kake yi ne saboda Allah?"

"Hajiya duk abubuwan da yake har yanzu bakya ganin laifukan sa sai ni?"

"Ni kake gayawa haka? "

"Kiyi hakuri Allah ya huci zuciyar ki.. kawai dai ya kamata ache kowa ya gama sanin halin wannan MUNAFIKIn me fuskoki biyu..."

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun.... Yaya wai dan Allah me na tare maka a rayuwa?"

"Ya isa hakanan... Ya ishe ku.. Yanzu neman inda yarinyar nan take zaa saka a gaba..."

'wacce yarinya?" Jalaludden ya tanbaya yana duban mahaifiyar ta sa da kallon  karin bayani..

"Maryaam yar wajen ku mana..."

"Wacce Maryam kenan?" Ya sake tanbaya don baki daya ta bache masa akan sa.

"Maryam 'yar junaidu ta karshe yar wajen Jamila matar sa"

"An dauke ta fa kuka ce... Ya zaai azo har cikin gidan nan a dauke mutum?"

"Kana nufin baka da masaniya?" Sarki junaidu ya samu kansa da tanbayar dan uwan na sa..

Wata harara mai cike da dimbin mamaki jalaludden yayiwa junaid,

"Lalle baka da hankali.."

Hajiya Maryam ta daga musu hannu...hadi da janyo wayar ta ta lalubo lambar kawun su Adamu ta kira shi bugu biyu ya dauka bayan sun gaysa ne ta gaya masa abun da ke faruwa ta karkare da,

"Kazo bangare na..."

Tana gama waya dashi ta kikkira sauran iyalan nata... Ba jimawa kuwa duk hallara a sashan nata, har surukanta matan da 'yayan su...

"Hajiya wani abun ne yake faruwa?"

'muna cikin tashin hankali... Mun wayi gari da rashin Amaal... Ma'ana an sache ta bata nan"

Kawu Adamu ya bude baki cike da kidimewa da tsantsar tashin hankali yace,

"An sace Amaal kuma? Yaushe? Ba nan jiya harda ita mukayi ta hira ba?"

"Yau aka dauke ta"

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Innalillahi wa inna ilaihi rajiun " bappah Nuraddeen ya shiga maimaitawa

Baki daya parlorn suka dimauce.. Aka shiga sallallami anata jajanta lamarin. Cikin kankanin lokaci aka baza labarin batar ta cikin filin cigiya.,

Kafafen yaada labarai... Gidajan rediyo, gidajen talabijin, jaridu da sauran tashoshi na yanar gizo sai haska batan Amaal suke yi.. Wanda Allah yasa ya gano inda take zai samu rabo mai tsoka na kyauta... Sannan ana neman barar addu'oi daga bakunan mutane masu albarka kan Allah ya bayyanata cikin aminci.
Chapter 32 · 0% Book details