← Book details Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 60

Sashe 56

Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Banason shiga damuwar ki ko ya ya ne Maryam.. yadda bugun zuciyar ki ya sauya ya sani shiga cikin wani muwuyacin hali dan Allah kiyi hakuri da kalaman dana fada.. Maryaam ki yafe mun kaunar ki ce sanadi.. Dan Allah kiyi hakuri babbar kyauta da muhimmanci a gareni shine samun ganin kyakykyawar fuskarki. burina shine naga bayyanar fitar murmushi akan kyakykyawar fuskarki. Kuma ace nine sanadin yinsa . Inaso ki fahimci cewa burina a koda yaushe ki kasance cikin farin ciki... Dan Allah ki gaggawar cire damuwar hakan a ran ki... Wasu lokutan in ina tinanin ki Maryaam hatta sunana ban iya tunawa, soboda a sanda nake tunanin ki, babu abunda ke da mahimmaci kuma agareni sai ke... Maryaam bar sa damuwa a ranki... Ba don haka na ke kaunar ki ba ke din nake kauna ba wai kwadayin ki nake ba...Masoyiyata, ina son ki fiye da yadda kike tunani. Ina son kasancewa tare da ke domin kina farantawa zuciyata ko da murmushin ki ne kawai. Kallon ki kadai kan sanya in samu kuzari, duk wata kasala da lalaci in ji ta gushe. Ke ce farin cikina.. Maryaam har yanzu bakya so ko ya ya? Uhm...? Wifey..."

Fashewa tayi da kuka sosai ta kankame shi tamau.... Baki daya ita kanta haushin kanta take data kasa bayyana masa yadda take jin sa a ranta. Tana kaunar sa daidai misali ita din wacece da har zata hanashi abunda yake dole akanta? Kullum har sai ya rike ta amince dashi tukunna? Bai taba mata dole ba. Bai taba tauye mata hakki ba' Bai taba hantarar ta ba. Bai taba ko da bata ransa akan lefin tane. Adadin soyayyar sa yake bayyana mata zalla kullu yaumin..

"Here and now, let love express on my behalf what I feel for you. I love you more than love itself can offer. There are many ways to be happy in this life, but all I really need is you.. Maryaam kuka? Lle bakya so na dan Allah Maryaam ki bari na sallame ki kamar yadda kike muradi banason tauye miki hakki maryaam s...

Bai karasa ba ta kamo bakinsa ta sanya cikin nata. Sunbatar sa take cikeda nuna masa irin kaunar da ita din take masa ... Hawaye nabin kuncinan dukkanin su.. Ta janyo hijabin ta tazare gaba daya ta jefar da shi... Al-mustapha zai yi magana ta hana shi ta hanyar saka masa dan yatsanta tace,

"Kaine mafi tsuma zuciya da nishad'i mafi 'karfin kore damuwar zuciyata basu kasance a tare da ni ba sai bayan da na had'u da kai. Kai ne ka zamo tauraron da hasken sa yayi sanadiyar raba zuciyata da ba'kin duhun da ta dad'e a ciki. Had'uwa da kai ya kawo canji mai yawa a cikin rayuwata. .Tunda nake a rayuwa ta, ban taba zaton zan shiga irin farin cikin da nake ciki yanzu ba. Soboda kai, na daina shiga damuwa, Har ila yau ina kara godewa ubagiji da ya hadani da miji wanda na dade ina mafarkin samu. Na dade ina rokar ubangiji da ya nuna mun irin wannan rana da zan sami miji wanda zai soni irin soyayyar da bazai iya misaltuwa ba kuma nasamu...When I look into your eyes, I can see a reflection of the two of us and the life I hope we’ll share. I know you’re the only one I want to share the rest of my life with... Ina kaunar ka irin kaunar da baki yayi kadan wajen furtawa. Ina kaunar ka irin kaunar da alkalami yayi kadan wajen rubutawa.. Ina kaunar ka irin kaunar da zuciya keyiwa rai.. rai keyiwa gangar jiki. Ina kaunar ka sosai Al-mustapha na...."

Gaba daya ya gigice zaiyi magana tayi saurin sake hade bakunan su waje daya... Ta kashe side lamp ta zare kayan jikin ta ta jefar. Ta fara zare nasa, Al-mustapha kamar almara yace,

"Maryaamu..."

"Sssshh I have the right"
Ya taya ta ta cire nasa kayan ... Taja musu bargo ta rufe su suka bude sabon shafin soyayya. Ranar dai Al-mustapha ya tabbatar maryamun sa dagaske tana kaunar sa. Domin ta nuna masa zallar kauna daren ranar.. ya samu gamsuwa fiye da yadda yake tunani. Sai shi mata albarka ya dinga yi. Domin daren ranar sun gurji soyayya tsmkar cin Kwan makauniya. Lamarin sai fatan Allah ya basu zaman lafiya da kaunar juna da yalwar arziki.

::::::

Ko da safe ma hakan ce ta kasance. Al-mustapha mamaki ya cinye shi gaba daya. Domin yadda maryaam ta saki jikin ta da ranta tamkar ba ita ba. Ya sharara son ransa..

Tare sukai aikin gidan gaba daya suka gyara ko'ina gwanin ban sha'awa tamkar da can din masoya ne.

Tanada lectures din rana... Direbobi kuma kowanne an aike shi. Gashi yanada meeting na gaggawa a lokacin. Sai Hamid ne ya temaka ya kaita makarantar har bakin department dinsu......

_ADVERT👇_

_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*

_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

_*BAKON MUNAFIKI!!!*_
_(BA NA MUTUM DAYA BANE)_
_👺🏡👩‍👩‍👦‍👦_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
_®️NANA HAFSATU (MSS XOXO)_

_AREWABOOKS:MSSXOXO_
_WATTPAD:MISSXOXO00_

_PG:50.. (FINALE/KARSHE)_

_________

***Har bakin department dinsu Hamid ya kai hancin motar sa ya sauke Amaal.

"Nagode sosai Yaya Hamid... "

"Allah ya bada sa'ar karatu kanwata. "

"Aameen Yaya... Sai na dawo"

"Toh sai kin dawo"

Fita tayi daga cikin motar bayan ta gyara zaman laffayar dake naade a ajikin tah.

Ta shige cikin department din nasu tana daga masa hannu yana daga mata.. Bai bar wajen ba sai da ya tabbatar ta shige ciki, sannan ya juya kan motar ya koma kan titin da zai sadakaa da wajen makarantar...

Dai dai wani garden bayan ka wuce department din su Amaal ya hango bayan wani namiji da wata mace. Namijin yana daaga wa macen hannu cike da faada yadda yake nuni da ita zaka san masifa yake yi sai watsa hannu baya yake yi..

Rage gudun yayi ya shiga tafiya a hankali da motar yana muskutawa gaba sosai... Kamar Hindu? tabbas ita din ce dai da wannan malamin na su Amaal don ya zo shi daurin auren ma.

Kafin Hamid ya karasa dai dai saitin su Habibi Talba yabar wajen bayan ya sake gaggaasawa hindun bakaken maganganu.

Ta tsugunna ta kife kanta da cinya tana kuka sosai harda shessheka.. Hamid ya samu zuciyar sa da karaaya don baki daya baya son sauraron kukan mace. Bayason yaga mace na zubar da hawaye musanman akan 'da namiji...

Ya fita daga cikin motar sa ya nufi inda Hindun ke tsugunne tana kuka..

"Hindu...." Ya samu kansa da kiran sunan ta karo na farkon a rayuwar sa. Domin basu taba magana ba.

Da sauri ta daaga kai... Duk azaton ta ko Habibi ne ya dawo ya bata hakuri. Kallon su ya sarke dana juna... Ta samu kanta da kasa dauke idanun ta daga kansa... Sanye yake cikin kananun kaya ya dora blazer akai. Ba karamin kyau yayi ba.. ita kuma tana cikin doguwar riga ta atamfa ta yafa dan karamun mayafi

Handkerchief ya zaro daga gaban rigar sa, ya saka yatsu biyu saitin fuskar ta ya murza su suka bada sauti ganin tayi kamar mutum mutumi,

"Snap outta it.... Ungo rike ki goge hawayen ki kinji...?"

Tabi hannun nasa da hankicin da kallo...

"Malam Ina ruwan ka da ni?"

"Wooo. I mean no harm Hindu... Daga temako? Haka kike dama?"

"Ni banason munafurci saura kaje ka gayawa su Abbiey kace ka ganni a haka.. Daman kun saba ai halin gado kuka dakko. Yi sauri kafi ruwa gudu kaje ka fada... Mtssss! Aikin kawai"

Hamid yayi murmushi yana girgiza kai yace,

"Na gano ma ba lefin gayen daya barki bane kece me lefi"

"Dalla Malam ware ka bani waje.. Ina ruwan ka? Kawai saboda shisshigi . Wait biyo ni kayi kenan tun daga gidah dama dan ka dau rahoto ka kai musu?"

Hamid ya sake yin dariya har yana rike cikin sa, Hadi da saka dayan hannun sa ya dafe bishiya.

Hindu ta kalle shi ta dalla masa harara tana yamutsa fuska ta cigaba da cewa,

"Naci dubu sai ceto. Kurwata kur wallahi nan gani nan bari... Wanda yayi gaba yayi gaba na baya sai labari. Shi zakaran da Allah ya nufa da chara ko ana muzu ana shaho sai yayi s....

Hamid ya sake fashewa da draiya. Ya tsugunna a saitin da take yana dubanta sosai yace,
Chapter 56 · 0% Book details