← Book details Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 60

Sashe 17

Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kamar yadda kowannen ku ya sani....Sarautar birnin Nukaa ta mu ce tun tale-tale... Tsatson mu ne suka kafa yankin har ya tumbatsa ya zama birni... Kaka da kakannin mu ke karagar mulkin sarautar birnin Nukaa.. kamar yadda kuka sani mu duka nan ciki harda Adamu ba wanda zai iya rike karagar mulki. Shekaru sun ja bugu da kari ba ishasshiyar lafiya... Sannan kowannen ku anan idan aka tsame matan dik zaku iya rike karagar mulkin birkin Nukaa. Nasan Kuna mamakin maganganun da nake ko?"

Duk suka yi shiru. Tamkar ruwa ya cinye. Alhaji jalaludden ya kasa shiru yace,

"Bangane ba Bappah.....Kai na ya kulle."

"Abunda ya fada haka zancen ya ke.... Mun saa ni kun sani kowa ya sani. Muhamamd mahaifin ku ne zai rik karagar mulkin Nukaa. Tun shekaru masu tarin yawa sai sabani yayiyyi ta afkuwa da kuma lokaci da Allah bai amince ba. Hakan bai yi ba. Ya zamto sai rikon kwarya aka bayar har ya zuwa sanda jikin sa zai warware. Astagfirullah lokaci bai yi ba har yanzu Allah bai amince ba...

"Mutanen gari na ta magana. Abu nata tafiya ya zamto sauran sarakai na kawo sukar hakan da sauran masu rawani..dik kuwa da abayan idanun mu sike fada. Don masarautar kandemi kaf Nigeria ba masarautar da ta Kai ta a komai na, Sarauta, ilimi, dattako, karamci, adalci, kyautatawa da sanin mutuncin dan Adam. Wannan kyawawan halayen anche tun Ardo kandemi haka ake yabon mu..

"Jikin Muhamamd har yanzu sai godiya ta mai duka kawai... Muna Kuma fatan Allah yasa kankarrar zunubai ce. Allah ya tashi kafadun sa ya bashi lafiya mai dorewa Amin.."

"Aamin" suka hada baki wajen amsa shi.

Alhaji jalaludden ya kasa zama sosai sai mitsil mitsil ya ke. Musanman da yake da tabbacin shi zaa bawa sarautar domiin shi yafu vancanta a nasa ganin

Bappah Imran ya shiga nazartar su yadda kowanne yake sakawa da warwara a cikin zuciyar sa. Ya sauke kallon sa ga Alhaji jalaludden da shi ma shi yake kallo,

"Bappah na amince...." Alhaji jalaludden ya fada cikin rawar jiki da dimbin farin ciki.

"Ka amince da me fa jalaludden?"

"Da zama sarkin birnin Nukaa..."

Bappah imrana ya juya ya dube su Bappah Usayn. Kafin yace,

"Jalaludden! Na yaba da hankalin ka kwarai da kake son karbar sarautar nan ba tare da an tursakaka ba. Sai dai Ina mai sanar da Kai cewa mu bamu da damaar da zamu nada ka sarkin Nukaa... Ku sani cewa ni da su bamu da iKon bawa kowacce iriyar sarauta ba tare da amincewar su ba. Sai sun tankade sun tache Wanda yafi cancanta tukunn sannan ake gaya manw mu ma mu bada Karin haske,

"Don haka ku bani hankulan ki duka Nan, Dan Allah kada ku bari mulkin sarauta a duniya ya zama silar rabuwar kawunam ku. Bayan an fitar da sunan Wanda zai hau kujerar mai martaba. Akwai nukamai da zamu bawa sauran ku. Daga kan sarautar waziri.. Nuraddeen, Abdullahi, Jalaludden, Junaidu... Ina fatan kuna sauraro na?"

"Eh Bappa"

"Tohm Alhamdulillah....Dukkanin ki iyali daya ne... Kuma Muna da tabbacin babu wata hasuniya da zata taso dubada kawunan ku a hade su ke.. Nuraddeen Kai ne babban 'da ga Muhammadu. Baka da wasu halayen na ki da zaa ce ba zaa baka sarautar Nan ba.....

"Bappah wai ni ne zaa nada sarki? " Alhaji Nuraddeen ya tambaya yana mai girgiza kan sa.

Bappah imrana ya grigzia masa Kai alamun a'a..

Alhaji jalaludden ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yana hasaso irin zaman kasaitar da zai yi idan aka dora shi a kan karagar mulkin birnin Nukaa..

Bappah Imran ya cigaha da cewa,

"Nuraddeen saboda tsananin kyawawan halayenn ka da kyautatawar ka ga iyayen ka yasa idan aka baka sarautar nan lalle an tauye maka hakki hakama iyayen na ka. Zamu so ka cigaba da kulawa da mahaifan ka."

Aljski Nuraddeen yayi murmushi yace,

"Godia nake bappah Allah... Allah ya kara hade kawunan mu.",

"Aameen..."

"Sannan Abdullahi tun a baya ma kana fada baka da raayin sarauta ko kuwa?"

"Hakane bappah... "

"Yauwa sai Kai Jalaludden.... "

"Bappah na amince....."

"Da me fa?"

"Sarautar..."

Bappah Imran ya juya ya dubi su Bappah Usayn. Ya musu alama da hannu. Bappah Hassan yayi gyaran murya yace,

"Kai da ka ke da political appointment"

"Bappah ajiyewa zanyi."

Bappah Hassan ya girgiza kai yace,

"Kafi karkata a harkar siyasa jalaludden. Bamu ce wai baka cancanta ba.... Ka cancanta kwarai matuka.. duk cikin ku Nan ba Wanda Bai cancantaba. Kuma wannan sarauta da zaa bayar kamar rikon kwarya ce kafin farfadowar jikin mahaifin ku."

"Bangane ba Bappah..."

"Ina nufin yan majalisar sarki da mu da sauran masu ruwa da tsaki....An dauki dan uwan ku a sunan Wanda zai rike sarautar birnin Nukaa... Wato Junaidu... Dan uwa Kuma karamin Kani agare ku baki daya................

..
_ADVERT👇_

_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*

_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥
[8/25, 10:43 PM] Hafsaat💞: _BM_

_NA:_

_NANA HAFSATU_

_PAGE: 19_

_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._

___

Gaba daya kowannen su mamaki ya cika shi. Musanman Amb Junaid da ya sandare a zaune. Ji da ganin sa suka dauke na yan wasu dakikai...

"What nonsense....!!!" Jalaludden ya fada yana mai mikewa tsaye... Da alama ya mance su waye agaban sa.

"Jalaludden meye haka?" Alhaji Adamu babban wa agare su ya tashi ya riko shi.

"Kyale ni Yaya.... Bappah ku duba lamarin nan ya za'ai abawa junaidu sarkin Nukaa? Ya zaai ache shine asaman mu kaf kandemi ? Ban amince ba gaskia. Ban goyi ba. Bai cancantaba Kuma ba zai taba zama sarki agare ni ba gaskia..."

"Magana zaka mayar mana jalaludden?" Cewar bappah Usayn.

"Bappah ba haka bane kuyi hakuri .... Ran sa ne abace." Cewar Alhaji Abdullahi Dan uwa agare su.

"Toh sai me idan kai baka amince ba wanene kai din? Adamu ka amince da zamantowar Junaidu sarki agare mu gaba daya?"

"Na amince.."

"Abdullahi Kai fa?"

"Na yarda Bappah."

"Indo... Fatima ku fa?"

"Na yadda Bappah..."

"Na aminta Bappa.."

"Toh kaji sauran yan uwan naka duk sun amince. Don Kai daya tilo kaja da maganar da mika yanke ai ba wani abun bane."

"Bappah Dan Allah kuyi hakuri ba a hayyacin sa yake ba"

"Kasan Allah Adamu idan ka sake cewa ba yin kansa bane sai na sharara maka mari. Jini daya kuke tsato daya kuma . Kani ne agare ku. ... Menene a sarauta Dan an dauka an bashi? Sarautar da rikon kwarya ce Kai ko da ma dindindin dince sarauta ai wahala ce. Idan aka maka iya takunkumi ce. Sannan dik wahalar alumma akan ka ta ke.. Wallahi ko da me zaa hadani ba zan iya sarauta ba.. Duk nan zamu jya cewa zamuyi tunda gadon mu ce. Amman aka duba cancanta aka zabi junaidu. Ba gamon kan mu mu kai ba.. Manyan mu da Yan majalisa ne Hadi da wasu daga cikin alumma ne sika hada Kai suka Zabe shi. Don haka amincewar ka ko akasinta duk ba a damuwar mu bace .... Junaidu shine sarkin birnin Nukaa da yardar Allah s...

Bai karasa ba amb Junaid ya fashe da matsanancin kuka mai tsuma zuciyar dik wanda ya saurara...

"Junaidu kukan me kake?" Bappah imrana ya tambaye shi.

Amb Junaid ya daga kansa, idanuwan sa sun kada sunyi jajir... Wata jijiya ta tashi daga goshin sa tayi radau.

"Lafiyar ka junaidu?" Bappah Usayn ya tambaye shi cike da kulawa

"Bappah....Kuyi hakuri amman ba zan iya karbar ragamar sarautar Nukaa ba. Bajda sani banida ilimi na Sarauta, kamar yadda Yaya jalaludden ya fada ban cancanta na zama sarki ba wallahi... A bawa wani daga cikin su Bappah. Su din manya na ne Kuma sunfini ilimin sarauta zasu Fi iya rikon kandemi...Musanman Yaya jalaludden zai fi dacewa"

Bappah Imran yaja dogon tsaki, Cike da hasalewa yace,

"Asabar satin sama kenan da safe za'a yi taron nadin a babbar fadar yamma. Katin gayyatar zasu fito gobe da safe inshaa Allah zaa fara rabawa. Zakuma a aikowa kowannen ku kasonsa ya rabawa abokanan arziki. Kaje ka fara shiri. Sannan Yan majalisar sarki ma zasuyi zama da Kai. Allah ya taya ka riko... Allah ya baka sa'a ya yi riko da hannuwan ka yasa kayi Mulki me adalci... Allah ya hade kawunan ku da Yan uwan ka ya kauda dik wata baraaka... Ku tashi muje Usayn"

Yana gama magana ya mike .. su Bappah Usayn suka bi bayan sa.....

Jalaludden ya buga tsaki ya fita daga dakin taron ransa a matukar Bache..

Sosai junaidu ya ke kuka tamkar wani karamun yaro. Alhaji Adamu da su Gwaggon court suka dinga bashi hakuri suna kwantar masa da hankali.
Chapter 17 · 0% Book details