← Book details Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 60

Sashe 50

Bakon Munafuki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru Amaal tayi kawai tana sauraron sa.. dik wata haddar dake cikin kanta ya goge mata su... Aina ya samu wadannan kalaman haka.. wane irin kauna yake mata da har yake neman illata kansa haka? Ta sake jiyo shi yana cewa,

"Zai iya kasancewa, niba ajin ki bane, ba irin namijin da kike so bane, amma inaso ki saka a zuciyar ki cewa nayi alkawarin zama irin namijin da kike mafarkin samu a rayuwar ki, nidai dama na ke bukata awajen ki... Domin awaje na kece muradin rayuwata ..Maryaam, You are my answered prayer, my fulfilled wish and my realised dream… You are not someone I want to be with. You are someone I cannot be without... Maryaam ki yafe mun please... Ki karbe ni amatsayin miji na tabbata bazaki dana sanin amincewar hadakar auren da aka hadamu ba kuma zamu yiwa iyayen mu godiyar aurar da mu da sukayi nan gaba...Kinji?"

Ita fa gaba daya bai sani ba ya gama kunce mata notinan kanta gaba daya...Ya sake langabar da kansa ya kwantar da kansa sosai akan cinyar ta.. ya zame hannuwan ya riko ta ta baya.... Tana jiyo tururun dukan numfashin sa akan tafukan hannuwan ta da dumin hawayen sa... Cikin rawar murya mai tattare da ban roko yace,

"Maryam Allah daya haliccemu ma muna yi masa lefi wani kan wani kuma yace mu roke shi ya yafe mana. mu fa yan Adam ne masu tarin lefuka maryam... Nasan ni me lefi ne awajen ki Ina rokon alfarma da kokon barar yafiya daga gare ki...Dan Allah kinji..?"

Ajiyar zuciya ta sauke ta danyi dan murmushi... Ya daga kansa da sauri ya kalleta,

"Kin yafe mun?"

"Allah ya yafe mana gaba daya.... Bacci nake ji Yaya Al-mustapha"

Gabas ya juya yayi sujjaada ya daga hannu yana yiwa Allah godiya. Batai aune ba taji yayi sama da ita a hannu yana zagaye dakin da ita.. yanata hamdala kamar wanda aka biya masa wani gagarumin abu..

Ya ajiyeta dakyar yana tallabo fuskar ta. Ya saka labban sa akan goshin ta ya yi mata kiss yace,

"Nagode..Nagode Allah ya miki albarka maryaam..."

Juyawa tayi ta shige bandaki da sauri ita dai..wanka tayo hadi da sabon tsarki.. tayi kan gado da sauri taja bargo ta lullube,

Shima bandakin ya shiga ya tsaftace jikin sa.. ya haye kan gadon bayan yayi addua. Ya janyota jikin sa tana ta tirjewa,

"Dan dai hugs and kisses dinnan Maryaam ki kyaleni mana... Babban darasin mu barshi zuwa gobe bayan kinyi test inshaa Allahu ba daga kafa."

Batace da shi komai ba.. tana jinsa yanata neman magana ajikin ta tayi masa shiru..Hakan datayi ba karamin dadi yaji ba yayita budurin sa yadda yaso daga baya ya rungumeta tsam yana cewa,

"Ina so kiyi mun wata alfarma guda daya, inaso fuskar ki ayayin da kike murmushi ta zama fuskar da zan gani karshe kafin na dinga kwanciya kamar yau, haka zalika fuskar da zan gani bayan na tashi daga bacci duk safiya. Zaki iya bani wannan damar?"

Shiru tayi masa dariya ma ya bata ta sake cusa kanta kawai a pillow. Tana jiyo shi ya zame pillow din ya mayar da kanta kan kirjin sa... A haka bacci ya dauke su..

***

Tun asubah masu aikin Hajiya maryam suka kawo musu abun karin kumallo don haka da safe wajen bakwai Maryam tayi warming dinsu taci tabarwa Al-mustapha nasa tanata sauri... Ta leka har yanzu bai tashi ba tun bayan daya dawo daga sallar asubah. Don haka ta harhada handouts dinta direba ya kaita makaranta karta makara saboda test.

Al-mustapha daya tashi yasha mamakin ganin bata nan ya kalli agogo.. ashe shine ya makara.?.. Ta tafi test kenan? Yayi murmushi yace,

"Allah yabada nasara da sakamako mekyau Maryamu tahh..."

Bandaki ya shiga yayo wanka yaci abinci ya sauya kaya ya tafi office kai tsaye..

Ko da ya dawo wajen 12 kai tsaye ya nufi sashen su bata nan... Yanata tunanin inda take . Kawai ya tafi bangaren Hajiya Maryam dake bayaan su. Inde bata nan to fa kunya ba zata barshi ya duba bagaren hajia Jamila ba ko na su....

Bakin sa dauke da sallama ya shiga parlorn Hajiya... Tare da hannuwan sa dake zube cikin aljihun wandon jeans din dake jikin sa... Ya dora riga ja me ratsin baki da dogon hannu ta kamfanin dkny... Bakadan ba yayi kyau sai wani annashuwa yake ji a tattare da shi..wai shi Al-mustapha angon Maryam Amaal.

Yana shiga idanun sa na kan Maryaam Aamaal dake zaune tana jotting rubutu daga wayar ta. Sanye take cikin doguwar rigar atamfa datayi matukar amsar jikin ta..mayafin kayan ta ta rufa shi daga gefen ta .

"Ahh wa'alykm salam... Dan yaye ka dawo?" Hajia maryam ta amsa shi tana murmushi

Gogon naku sam bai ji maganar da hajiyan ke yi masa ba. Ya nufi inda Amaal din take ya ja mayafin ya lullube mata jiki gaba daya.. ya durkusa agaban ta yana cewa,

"My baby♥️yaushe kika dawo???"

Maryam da duk kunya ta dubibiyeta tace,

"Haj... Hajiya na maka magana..." Ta fada harda wata yar in'inar data taho mata alokacin...

Ya mike da sauri yana sosa keyar sa..

"Hajjaju mutan makka...Barka da rana...

ZAFAFA BIYAR WRITERS♥️
[10/2, 5:13 PM] Hafsaat💞: _4_
_6_
____

***Hajiya Maryaam tayi murmushi. tace da shi,

"Alhamdulillah dan yaye.... Ya aikin?"

"Lafiya kalau Hajia.."

"Toh Ma'shaa Allahu... Allah ya kara temakawa"

"Aameen Aaameen Hajiya"

"Ka ci abinci...? Ko da yake an kai muku na rana ma sashen ku"

"Mungode Allah ya saka da alkhairi Allah yakara arziki"

"Aameen,.. Nasan baka ci ba. Wato har yanzu ba zaka dena wasa da cikin ka ba ko?"

"Tuba nake hajjaju makkatun... Zanje naci yanzu inshaa Allah"

"Yauwa ko kai fa..."

Aaayan ya shiga parlorn Hajiya bakin sa dauke da sallama.... Ya nemi waje ya zauna bayan sun gaysa da su Hajiyan

"Dan wahala... Kana nan ashe?" Aayan ya dubi Al-mustapha yana tsokanar sa

"Ni da kai ansan ko waye dan wahalar ai... Wawa"

"Oho dai... "

Mikewa Al-mustapha yayi yana sosa keyar sa... Ya dan saci kallon Amaal dake cigaba da rubutun ta.

Aayan ya dube shi ya dubu Amaal din yace

"Menene? Ka zuba mata idanu kuma ka kasa cewa komai?"

"Ina ruwan ka? Maryam kinci abinci?"

Amaal dake rubutu ta daga kai ta dube shi kafin ta mayar kan wayar ta tace,

"Sai anjima.."

"Toh " ya amsa a sanyaye yayi hanyar fita

Hajiya maryam ta dube ta ta ce,

"Je ki zuba masa abincin.. Kamar karamin yaro sai an saka shi a gaba ai kullum.."

"Tohm" Amaal ta fada tana zura wayar da littafin hannunta a jaka..

Aayan ya dube su ya sheke da dariya yace,

"Wallahi Hajiya ki dena shagwaba katon mutumin nan... Kina wani ce masa dan yaye kullum kansa yana girma"

"Ina ruwan ka? " Al-mustapha ya harare shi.

Hajia ita dai dariya tayi.... Amaal ta musu sallama ta fita. Al-mustapha yabu bayanta har yana tuntube garin sauri.

Ya saka mukullin hannun sa ya bude kofar suka shiga bakunan su dauke da sallama...

Daki ta wuce ta ajiye jakarta... Ta zare kayan ta ta saka rigar wanka ta shige bandaki bakinta dauke da addua. Wanka tayo hadi da alwala.. ta sauya wasu kayan marasa nauyi.. irin rigar nan yar kanti mai gajeran hannu sai ta yafa wadataccen mayafi bayan ta shafa turaruka..

Yana zaune a parlorn ta wuce wajen socket ta jona burner ta saka turaren wuta nan da nan gidan ya gauraye gaba daya da kamshin turaren sandal munawwara na kamfanin turaren yerwa incense and more...

Al-mustapha ya lumshe idanun sa ya bude saboda tsananin kamshin turaren daya mamaye shi gaba daya kamar a kamfanin haramein oud.

Wajen dinning ta nufa ta dauki plate ta zuba abincin, waina ce ta shinkafa sai miyar ganye data ji naman kasuwa. Ta zuba soup din kazar shima a cikin wani karamin plate taja kujera ta zauna bayan ta dauki kofi ta tsiyayi kunan ayan dake cike da madara da kankara har wani kamshin flavor ne ke tashi acikin sa.

Ya jawo kujerar kusa da ita ya zauna... Ya tallabe habar sa da hannun sa yana kallon ta cike da kaunar da yake mata mirar misaltuwa..

Ta dan kalle shi ta kauda kanta kasa kasa tace,

"A zuba maka?"

"Na koshi...." Ya fada yana kwantar da kansa akan hannun sa ya mayar da kallon sa gaba daya kanta. Har wani lumshe idanu yake

"Amma Hajiya tace ka ci fa"

"To zan ci wannan nakin"

"Tohm gashi" ta matsar masa da su gefen sa zata bude kulolin ta zuba nata ya saka hannun sa ya riko nata da sauri

Wani electric shock ya ziyar ci dukkanin su.. Amaal ta janye hannun ta da sauri tana matsawa gefe,

"Muci nakin mana tare please.... Kinji maryaam?"

Ba yadda zatayi ta koma ta zauna... Al-mustapha yayi murmushi yasake matsar da kujerar sa daf da ita har suna shakar numfashin juna..

"Feed me.... "

Ya wani bude baki yana lumshe ido.. dariya ma abun ya bata ta dangwala da miyar ta saka a bakinta tana taunawa ahankali...

"Baki bani ba fa?" Ya marairace yana narkar mata da idanun sa..

"Yunwa nake ji. Kaci da kanka mama"

"Uhm uhm...ni ke nakeso ki bani" yana langanar da kansa a kafadar sa cikin muryar shagwaba

Ita dai ta share shi ta cigabaa da cin wainar ta... Daya tabbatar dai ba bashin zatai ba sai ya saka hannu shima yana gutsira ahankali yanaci.

"Ya test din?"

"Alhamdulillah"

"Komai kin rubuta yadda ya kamata?"

"Eh...."

"Ma shaa Allah... Allah ya sa mu ga sakamako mekyau"

"Aamin.… Ka ci abinci mana"

Dadi ya kama shi yau Amaal ce da kanta tache yaci abincin mana... Ya dashare hakora ya shiga zura loma yana korawa da ruwa..

Mikewa tayi ta wanko hannun ta. Bayan ya gama ta tattare komai ta kai kitchen. Ta hada ruwan kumfa ta fara wankewa sai ga shigar sa yana nannade hannun rigar sa,

"Kawo na dauraye"

"Ka barshi"

Yatsan sa ya saka akan lebenta alamar tayi shiru... Ya rankwafa saitin kunnenta ya rada mata,

"Banda musu Maryaamu.... Ki wanke sai na dauraye.. kinji?" Ya karasa fada yana hura mata iskar bakin sa acikin kunnenta. Ya Kuma sumbaci gefen kunnen yana dan jan kasan sa a hankali
Chapter 50 · 0% Book details