Sashe 99
Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da wani irin mutuwar jiki yake driving ɗin shi kaɗai yasan yadda zuciyarshi take tsananin jin kewar yarinyar da gaske tana da mugun shiga can cikin ran ɗan adam yana jin yana mata wani irin azababban so na fitar hankali, bayajin ze iya rintsawa batare da itaba. Ya jima yana driving kafin ya isa gida, dayake khadija tasan da zuwan nashi tuni ta kammale komai na gida gashi kuma alhamdulillahi ɗan satin dayay bai nan ta samu damar gyara jikinta sosai da magungunan da anty ruma ta kawo mata. Kai tsaye wajan ammi ya nufa ya tadda ita a falo tana zaune waya a hannunta ganinsa yasa ta aje wayar fuska ba sukuni take amsa mai gaisuwar daya ke mata. Kafin ta haɗe rai tahau surfa masa masifa kamar zata ari baki. "Sannu baba nace sannunka da shuka yanzu kai haka adalcin naka ike? kawai katafi masha Allah kabarmu da matarka baka ko leƙo mana ba?" Tafaɗa tana mita sosai. Seda ya jira ta gama faɗanta sannan ya kwantar dakai kamar ƙaramin yaro yana bata Haƙuri. "Ammina kiyi hakuri, wallahi mai sunaki ce batada lafiya shine na zauna sabida babu wani kusa da ita" Yafaɗi hakan domin yasan ta hakanne kaɗai zata rabu dashi. Sosai ammi ta washe haƙoranta. "Masha Allah baba amman dai kunje asibiti ko?" Sosa kanshi yayi. "Ban kaitaba amman inna koma zamuje" Murmushin ta kumayi, sannan ta dubeshi. "To inka huta kaje kaiwa ɗan uwanka barka zainab ta sami Aliyu jiya ta haihu ganin dare yasa ba,a gaya maka ba ubansa yay maka takwara, Sannan ankawo lefen su amina fa harda ƴan biyu abbanku yace sun gama school gwara an haɗa dasu tunda sunada mazajensu a hannu an saka rana nan da two weeks" Ƙayataccen murmushi ya saki yana furta. "Kai dik dai ammi masha ALLAH, Allah ya raya takwarana amman ni usman bai faɗamin ba?" Murmushi ammi tai. "Ance maka dare ne yayi shima fa yayanku umar fa humaira ta haifi mace yau kwana biyar kasan suna can legos ɗin duk se biki zasu tawo" A wannan karon kabbara yake bakinshi ɗauke da far'a sosai yake jan addu'a a bayyane ammi tana amsa mai kana ya mike. "Ammi banaje na gano my boy, wallahi sena ganshi zan wuce kafin na kawo ragon suna takwara ai ba wasa ba" Yafaɗa yana nufar hanyar fita. Da fatan alkairi ta bisa tana yabon haɗinkan zuri'arta sosai take kuma godiya ga Allah akan hakan. A bakin part ɗin ammi ya tsaya yay wa ya umar waya yay mashi barka harda ɗan mitarshi akan yadda bai gaya masa ba hakuri ya bashi sannan sukai sallama ya tafi, bayan yay masa transper kuɗi wai a saiwa takwarar ammi pampers. Cike da annashuwa ya isa part ɗin usman duk yan uwansu suna zazzaune a falo ana yiwa yaron wanka sosai suke kwasarshi yana wani basarwa dayake duk abokanan wasane yasa suke mashi hakan. Bayan angamawa yaron wanka aka naɗoshi a tawul aka mikawa Aliyu shi, addu'a yay masa sannan ya mike suka jero da usman. "Man kai kaga yadda kai wani fresh so masha Allah, amarya ta amsheka" Usman yafaɗa yana dariya. Shima ƴar dariyar yay kaɗan sannan yace mai. "Bazaka gane ba amman dai nina san yanzu nayi aure fa, Alhaji kaikaga yadda ake tattalina" Yafaɗa yana shafo gemunshi. "Dama ai irin waɗannan sunfi daɗi yar shila malam amman da ana baka kana ƙin amsa" Murmushi yay mai kana yace. "Bazaka gane irin son da nakewa beby ba wallahi usman ka gama min komai a rayuwata Allah kaima ya faranta maka kamar yadda ka faranta min" Sosai usman yake dariya ganin yadda ƙanin nashi ya zarme da yawa tab daman akwai ranar da Aliyu ze iya sauke jida kanshi yace yana son mace lallai so ba wasa bane ba. Ganin usman ze mayar dashi sauna yasa ya wuce part ɗinshi shima bakinsa kunshe da dariyar yabar usman dashe a wurin yana dariyar ƙeta. Sosai ya sami tarba a wajan madam dija kuma shima ɗin bai mata irin Wannan shariyar da yake mata daba sabida yana son ya kwatanta adalci gudun fushin ubangiji. Da taimakonta yayi wanka ta tayashi ya kintsa, se wani maƙele mai take ajiki shikuma yana wani basarwa abinci ta haɗa masa mai rai da lafiya, kaɗan yaci ganin tana wani irin mirmir da idanu ya gane mai take nufi ɗaukarta yay cak ya nufi ɗakinsa da ita sosai ya ruɗa mata jikinta da salonshi kafin ya kama hanyar dayafi kauri. Babu laifi baiji wannan azabar dayaji kwanaki ba sedai ko kaɗan bai sami ɗanɗanon daya samu wurin bebi ba domin ita bebi kusan haukacewa yake inya tare da ita. Bai wani jimaba ya rabu da ita ya mike yaje ya tsarkake jikinsa yazo ya shirya kanshi cikin wani marun boyel mai manyan zane, yana fesa turare ya dubi dija datake kwance kamar gawa bama ta da niyar tashi. "Dija ki tashi mana ki tsaftace jikinki" Taji amon! muryarshi acikin kunnenta da ƙyar ta mike tana ware ƙafafu ta fita daga ɗakin tanajin kamar an mata shegen duka domin ta gurzu. Dariya yay afili kana ya furta. "Tabb lallai kinada aiki banyi good 30 mnt ajikinki ba kike wannan gandar, lallai dija raguwace, waccan yarinyar semu wuni muna abu ɗaya bata taɓa gajiya ba sedai intaji yunwa taci abinci mu koma, amman ke daga sau ɗaya se ragwanci tabb,itako umminah ka daɗi ga dauriya wayyo i miss" yafaɗa yana dafe jikinshi da hannunshi, a gaggauce ya shirya ya nufi masallaci sukai sallar azahar sannan ya ɗauki mota ya nufi gidan mama sabida tunda yaje sau ɗayama bai koma ba. Sosai yay mamakin yadda aka ƙere gidan bayan haka kuma masu aikin sunyi mugun sauri. Harda ɗan gate a kofar gidan ga wani uban fanti mai azabar kyau da aka yima gidan. Parking ya gyara yana neman wanda ze aika. Kamar daga sama sega shahid akan lifan dinsa da Aliyun ya sai masa sabida zuwa makaranta. Yana washe baki ya ƙaraso gabansa ya rissuna yana gaisar da shi. "Yaya Aliyu barka da rana, yanaga ka tsaya a waje yakamata ka shiga ciki aikaima ɗan gidane" Murmushi yayima shahid sannan yace. "Kai dai shiga kacewa mama ina waje" "Tom bara na sanar da ita daman lefensu hassana aka kawo fa ɗazu, ansaka biki nan da sati uku" Murmushi ya kuma sauke masa. "Kai shahid da sauri haka za,a ɗebewa mama ƴaƴanta?" "Wallahi yaya da ai shekara aka saka to kuma su yaya nuran sesuka ce tunda sun gama gininsu kuma sun sami aiki su kawai suna so ai da wuri" Zaro idanu Aliyu yayi kaɗan wanda yake kara masa kyau kana yace. "To Allah ya nuna mana lokacin Amin" Shahid seda ya sanar da mama wadda tahau shi da faɗa damme baze ce ya shigoba sebarsa a waje. "Mama fa seda na gaya mai shikuma yace nadai sanar dake" Sannan ya fita wajan suka tawo tare da Aliyun Sosai gidan ya burgeshi babu dai wani girman kirki sabida wanda aka siya ɗinma bawani babba bane sedai tsarin fasalin gidan ya ƙayatar kana shiga tsakar gidane da bayi. Se ƙofar falon mama da aka zuba mata kujeru ma dai daita da ƴar tv ta bango harda ƙaramin frij, se kicin acikin falon se ɗakuna guda uku na shahid ɗaya na mama ɗaya na su hassana kuma duka da toilet cikinsu,se ƙaramin store sosai aka ƙayata gidan kamar ba shiba, kuma badaga wajan kowa wannan sauyin yake ba sedaga wajan Aliyu domin shiya wakilta wani yaronshi akan komai na gidan hatta saitin kayan ɗaki na kicin dana sakawa duk an kawo musu sabbi domin ɗakin mama gadone da sif da madubi hakama sauran ɗakunan su shahid ɗin bakaramin kuɗi fa gidan ya lashe ba, amman shi baiji komai ba sabida bebi ta bashi abinda yafi wannan daraja. Sallama yayi cikin nutsuwa ya shiga falon iskar fanka tanata kaɗawa. Mama wadda take zaune saman kujera tai saurin amsa masa tana gyara zaman hijabinta yatsunta jajur da lalle. A ƙasan center carpet ya zauna yana gaisar da ita. Tana amsa masa itama cikin kunya sannan ta mike taje frij ta ɗauko mai pure water ta zuba a plate ta kawo mai kicin ta wuce ta zubo masa alkubus da miya acikin kwanuka wadda miyar tasha naman kaji sabida yadda Aliyu ke sakawa a kawo musu kayan bukata akai akai. Gabansa ta aje sannan ta wuce ɗaki. ta ɗauko carbinta ta dawo ta zauna. "Mama yaya gida yasu ihsan? mama kozaki bamu arfa ne na kai mata sabida gidan yay mata faɗi ba kowa ni kuma na tawo nan" Yakai maganar kansa a sunkuye. "Kadai ci abincin tukunna bara na baka waje" Tafaɗa cikin kulawa ta mike ta nufi ɗakinta. Janyo plate yayi ya zuba alkubus ɗin guda biyu ya zuba miya bai saka nama ba. Bisimillah yayi ya soma ci ai ina tuni Aliyu ya manta a ina yake sabida azabar daɗin da abincin yayi masa, seda yaci sosai yasha ruwa sannan yay hamdala kana ya koma gefe ɗaya yana jin cikinshi ya cika damm. Zamansa da mintuna biyar su hassana sukai sallama falon jikinsu sanye da hijabi har ƙasa,daga ganima daga unguwa suke. Ganinshi yasa suka tsugunna suka gaishe shi sannan suka wuce ɗakin mama da kallo ya bisu yana yaba nutsuwar yaran. Arfa ya janyo da hannunshi yarinya ƙarama mai mugun kyau tana matukar kama da bebi. "Ajinki nawa a makaranta?" Basa amsa tayi da cewa. "Primary one ita kuma ihsan three" Sabida su daman tun asali a wata private school mama ta sakasu mai saukin kudi. "A islamiyya kuma munkai izifi sha biyar" Zaro idanu yay yana cewa. "Kai masha Allah" "Su yaya Bebi kuma sauka zasuyi fa aka mata aure anma kusa shine da aka mata aure tai ta yiwa mama kuka" Tafaɗa da suffar yarinta. "Suma su anty hassana ma aure za,a musu sunata yiwa mama kuka, kuma yanzu mama bata saida dambu kullum inaji tana yiwa wani yaya Aliyu addu'a intayi sallah muma tace kuma muyi masa waishi ya mayar mana da gidanmu sabo yake aiko mana da abinci" Tafaɗa batare data san cewar shiɗin bane. Dariya yakewa yarinyar sabida yaga irin yaran nan ne masu faɗi ba,a tambayekuba. Cikin haka mama ta dawo falon "Aliyu harka gama ka