← Book details Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 115

Sashe 30

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Æangaren ALIYU rannan baÆ™iƙƙirin ya kwana dashi koda asubahi ma daya tashi watsa ruwa kawai yay tare da nufar masallacinsu wanda ke cikin harabar gidan.
Ana idarwa ya fito sabida yana son yay sammakon office domin akwai abubuwa masu yawa dake gabanshi.
"Hy mr man barka da asubahi' Yaji muryar usman wanda shima kusan atare suka fito daga masallacin, ɗan dakatawa yay har usman ɗin ya karaso sannan suka jera ciki sabida daman ƙa'idarsu ce duk safiya sesunje gaisar da mahaifansu.
Ahanya usman yake bashi labarin rainin hankalin da zee tai mishi domin ko daya koma jiya tare da dambun nan ya tarar tai barci koda ya tasheta seta saka masa kuka! wai damme tana baccinta mai dadi ze tada ita da ƙyar ya lallaɓata ta koma baccin batare dataci dambun nanba, amman tace yau da safe zata ɗumama taci ya saka mata a frij.
Yaƙarasa gayawa Ali yana dariya, shikam Ali murmushi kurum yay sabida damuwar dake cin ranshi daman ai shima usman ɗin ya saka kanshine amman shikam bayajin ze tsaya mace ta dinga bashi order irin haka.
Sallama sukai cikin babban falon abbansu wanda suka tarar da sauran ƴan uwansu azaune kowanne gabanshi ɗauke da medium cup wanda aka shaƙeshi da ta'tacciyar zuma mai kyau wadda suke shanta aduk wayewar asubahi wannan al'adar mahaifinsu ce tun suna ƙanana yake musu hakan kuma gashi har girmansu basu dainaba domin hatta su ya abbakar dasuke manya suma sesunzo shan zuma kullum ta Allah.
Gaisawa sukai dasu abba sannan suka gaisa da ammi da ya abbakar, usman ne ya miƙa hannunshi ya ɗauki zumar gaban Amina ƙanwarasu wadda take gaishesu cikin respect, shiko Aliyu mikewa yay tare da kallon usman.
"Nifa zanje nai shirin office dan Allah karka mana delay kaga motana har yau tana garage, pls ka shirya da wuri".
Da kallo ammi ta bisa.
"Kai bazaka sha zumar ba kenan É—azuma nahau samanka yadda najera maka abincin nan haka nasaka su hassana suka kwasomin shi baka ko taba shiba".
ÆŠan shafa kanshi yayi tare da kallonta kaÉ—an.
"Ammi banji kai komai bakina yanzu da sassafan nan, sauri nakeyi kinga yau ko morning training ma banje ba sabida nai latti".
Abbane ya cafe maganar.
"To bara a haÉ—a maka break seka tafi dashi office É—in ko? ai baka tafi haka ba".
Cikin sauri usman ya amshi maganar.
"Dan Ammi kubarshi akwai masu dambu wallahi Æ´an gayu kawai ma siya muci".
Hararar da Aliyu ya watsawa usman ita tasaka usman É—in babu shiri yaja bakinshi yayi gum.
Ammi dariya abba dariya ya abbakar dariya su amina da Æ´an biyu ko suna son yin dariyar amman suna tsoro.
Fuww ya wuce samanshi yabarsu anan, seda ya tafi sannan ya abbakar ya dubi usman.
"Kaima kasan wancan miskilin baze iya cin abincin waje ba tsokanace kurum irin taka".
Hirarsu suka ɗan taɓa kaɗan sannan sukaiwa iyayen nasu sallama kowanne ya nufi yin abinda ke gabanshi, ƴan biyu shirin schl amina shirin office, suma su usman nufar part ɗinsu sukai domin suyi shirin fita office.
Ammi da abba kaÉ—ai ne a falon suna kallon labarai a tashar CNN.
Cikin kuzari da zafin nama yagama shirya kanshi cikin fari ƙal ɗin yadin tisue baƙar hular zanna tare da bakin takalmi mai rufaffan sama, se baƙin agogon rolex daya ɗaura a tsintsiyar hannunshi, fitinannun turarukanshi masu azababban ƙamshi yaywa jikinshi ɓarinsu.
Da hanzari ya ɗauki jakar laptop ɗinshi tare da tarkacen wayoyinshi, bai saka komai acikinshi ba ya kullo ƙofar bedroom ɗinshi tare da saukowa zuwa ƙasa yana zuba uban kamshi, bakaramin kyau wannan shigar tai mishiba ta ƙara masa ƙwarjini da haiba tare da tsantsar kyau irin na asalin yaren hausa fulani.
Still ya kuma samun iyayen nashi a falo hankalinsu yana kan TV sabida labaran da suke kallo na safiya.
Ƙarasawa yay gabansu tare da tsugunnawa har kasa yana gaya musu cewar xe tafi office.
Ammice ta dubeshi.
"Aliyu! wai miyasa kakeson jamin magana ne agun mutan gidannan kullum ɗauka suke ninake ɗaure maka gindi hatta mahaifinka gayanan duk sangartar dayake maka amman wataran idan idanunshi ya rufe seyace nike shagwaɓaka".
Ta numfasa sannan ta cigaba da magana.
"Jiya ka dawo daga legos amman ka gaza zuwa ka gaishe dasu yanxu ma haka fita xakai amman bazaka iya zagayen gaishe da mutan cikin gidan nan ba ko?"
Kansa yana kasa yana wasa da carfet É—in falon da hannunshi guda, bai tankawa ammi ba kuma baya tunanin harta gama faÉ—an ze iya tankawa sabida baisan meze ce mata akan hakan ba.
"Ba magana ake maka ba wai babana! É—azunnan Alhaji babba yagama yimin faÉ—a akan yadda kazo bakaje ka gaishe dasu ba, kaga nifa bana son abinda ze dinga kawon matsala da Æ´an uwana".
Cewar abba kenan wanda hankalinshi ke kan tvn gabanshi.
"Ayi hakuri xan gyara insha Allahu".
YafaÉ—i hakan yana jin ransa na suya shifa abubuwan gidan nasu sam sun soma fitar mishi daga kanshi
Mikewa yay yana kuma yi musu sallama batare daya nufi inda ammi ke nausar dashiba.
"Daman nasan wannan shegen taurin kan nashi wallahi bazeje É—in ba yadai faÉ—i hakan ne danya amsa maganar tawa, ya Allah ya Allah ya yayewa wannan yaro wannan kafiya da taurin kai amin".
Cewar ammi tana kallon abba wanda yay kamar baijita ba.
Aparking space ya tsaya suna gaisawa dasu fahad da sauran ƙannenshi waɗanda suke cousins kafin ya ɗauko wayarshi acikin aljihun wandon farin yadin jikinshi yana kokarin niman layin usman sema gashi nan ya fito cikin shigar black suite wadda tai mishi kyau babu laifi.
Batare da ɓata lokaciba usman yaywa motar key suka shige tare da nufar bakin gate.
"Ni wallahi daga yau bazan kuma dropping É—inka ba, nagaji da wannan takurar haka kurum da aurena fitar office a wannan duku, dukun".
Usman ya faÉ—a yana É—agawa masu gadi hannu lokacin yana kokarin fita daga gate É—in gidan.
Har suka hau kwalta yanawa Ali sababi wanda shi sam baima É—ago ba bare usman yasaka ran ze tankashi sema bude datar shi dayay ya shiga face book, abinshi.

Itako Bebi babu laifi ta É—an samu baccin da tai fashinsa jiya, muryar ihsan dake faman kiranta itace tai mata caa a dodon kunnenta É—ago idanuwanta tai waÉ—anda sukai jajur sukai wani irin girmaÉ— sabida bacci tana makawa ihsan harara"dan ubanki ubanme zan miki dazakizo kina tashina?" bata karasa ba taji muryar mama daga tsakar gida wadda takejin yadda bebin ke zagin ihsan É—in"Ubanki zatai miki maza tashi daga wannan baccin ga dambu ya hadu ki É—auraye fuskarki kutafi da hussaina"..................

_Wallahi har yanzu ina zazzaÉ“i bana jin daÉ—i dan dai nai alÆ™awarine ma amman da bazaku samu update yauba amman gashi nayi da Æ™yar Allah ya bamu lafiya amin_ ðŸ™
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
{ _HOT LOVE_ }

NA
*AUTAR MANYA*

_Albishirinku iyayen yara dama yaran baki ɗaya, shin ko kinsan shararriyar tashar nan ta youtube mai suna *Abdur-rahman* ta shirya tsaf domin baku gudunmawa wajan tayaku bitar karatun ƴaƴanku cikin sauƙi?, Kai dai/ kedai maza garzaya wannan shararriyar channel ɗin domin ki dannawa yaranki dansu karu da zazzaƙar ƙira'ar da *Abdur-rahma* ke gudanarwa wajan bitar karatun alkur'ani mai girma acikinta daman sauran littattafan addinin islama kada ki manta da danna *SUBSCRIBE* tare da ƙararrawar sanarwa mungode_
https://youtu.be/PFTnz8JGFfQ

_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._

*43&44*
Chapter 30 · 0% Book details