← Book details Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 115

Sashe 25

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Sanye yake cikin fara ƙall ɗin shirt mai gajeren hannu se bakin trouxer, tare da wata jarket mai tsaho domin tsayin nata har kusan gwaurinshi yakai, mai kalar baƙin itama dai sabida yanayin sanyi yasa ya ɗorota akan kayan nashi, cikin nutsuwa yake saukowa daga step ɗin jirgin hannunshi ɗaya rike da ƴar medium troly dinshi, se ɗayan daya riko wayoyinshi cikin nutsuwa yagama saukowa yana shakar kamshin jaharshi wadda yakejin yay missing ɗinta na two days.
Seda yay setting É—in komai sannan ya fito harabar airport É—in yana kunna wayoyinshi.
Number usman ya kira domin yaji yana ina?.
Cikin sa'a shima kuma usman É—in a lokacin yana gyara parking É—inshine domin yama riga daya karaso.
Sam baya son delay aliyu shiyasa ya dakatar da usman É—in akan daya jirashi a motar gayanan zuwa.
Cikin lokaci ƙalilan ya karasa gaban motar usman ya bude side ɗin baya ya wurga jakarshi sannan ya dawo kusada na driver ya bude ya shiga tare da furta "Alhamdulillahi". yana haɗe yatsunshi duka ya matsa suka bada sautin ƙas! ƙas!! ƙas!!!.
Sannan ya É—an É—ago ya dubi usman wanda yake kokarin tayar da motar tare da cewa.
"Majinyaci barka da dare?".
Cike da É—unbin mamaki usman ya dubeshi.
"Kamar yaya fassaramin da hausa, kasan nifa aduniya nafison komai aimin dalla-dalla musamman da yaren danafi so wato hausa harshen uwa abin alfaharina".
Dariya yayi sosai wadda tai matukar ƙara mishi mugun kyau! domin ko har sedama dimple point ɗinshi ya lotsa fararen hakoranshi masu kama da ƙanƙara dan haske suka buɗe gwanin sha'awa.
Hannunshi yasa ya cire jarket É—in dake saman kayanshi ya wurgata can baya sannan ya dubi usman har yanxu face É—inshi É—auke da murmushi sannan yace.
"Haba man ai kowa ya kalleka yasan kana jinya".
Nisawa yayi kamar yadda ƙa'idar maganarshi take yakan ɗan ɗauki lokaci kafin ya ɗora wata idan yay ɗaya tamkar wani basarake ( niko nace ko ABDUL-NASEER ! bayayin haka shida yake jinin sarauta *DA IZZATA* littafin dana gama kafin na ɗora wannan ).
"Ɗayan biyu, kodai madam zee ta riƙe maka wuta koko aikin office ya sakaka gaba domin nasan kai ɗin ragone kamar kasa".
YafaÉ—a yana dariyar mugunta , wadda tabani mamaki matuka daman Aliyu yana dariya haka?, aiko yanayi amman fa ba kasafai ba shiyasa idan yayita take mugun yi mishi kyau.
Kamar usman zeyi ihu! ya tada motar yabar harabar airport É—in, seda ya É—auki hanyarshi sannan ya dubi Aliyu.
"Kai dai bari ɗan tuzurunmu ango wani satin, wallahi ina cikin tsaka mai wuya da wannan matsin na zee wallahi gwara fitar office ƙarfe shidan safiya".
Wayyo my fans zokuga miskilinku yadda yaja seat baya ya dafe bakinshi yana dariya kamar babu gobe.
Seda yay mai isarshi dama ya kwana biyu bai dara ba, sabida nisantar usman dayay na kwana biyu domin usman commedies ne badai bada Dariya ba.
Sannan ya É—ago tare da kallon usman É—in.
"Tofa yaya akai yanzu kuma sau nawa ta koma maka?".
YafaÉ—a yana kunshe dariyarshi.
"Inaaaaa, ai yanxu an wuce wannan wajan kasan Allah ƙuguna baya hutawa nidai wannan cikin wannan cikin yana wahalar ni, yanzu kuma tsirfar dambu ce ta motsa".
Tass........Usman ya bawa Aliyu labarin halin dayake ciki, su dama basu da abokai su biyu ne abokan juna duk wani sirrin usman Aliyu ya sani gwarama shi Aliyun miskilanci kan hana shi faɗawa usman ɗin wani abun, amman kuma duk da haka usman yana da matukar kusanci ga Aliyu sosai dan yana iya gaya mashi maganar da baxe gayawa ammi ko abba ba sedai yana ƙwaɓarshi akan kada ya faɗa sanin ɗan banzan surutun usman.
Hatta yadda sukai da mama da bayyanar Æ´an biyu a kamfani da mutunci da maman tai masa seda ya kwashe ya gayawa É—an uwan nashi.
Halin zuciyar Aliyu mai rauni yasa ya dubi usman cikin tausayi sannan ya soma bashi baki akan lamarin ganin duk usman É—in ya soma karaya.
Amman yana masa maganar yana kunshe dariya.
Da lallaɓi usman yaja Aliyu zuwa sharaɗa karɓo dambu lokacin har goman dare ta wuce.
Ganin yadda usman É—in yay kalar tausayi yasa ya yarda ze rakashi amman bada ban hakaba da baya tunanin nufar ko ina idan ba gida ba sabida gajiyar dake cinsa ga yunwar dayake ji fatansa yaje gida yay wanka yaci abinci marar nauyi yay nafilarshi ya kwanta ya huta.
Amman yadda usman ya takurashi da magiya yasa yace masa suje ɗin amman da ya karɓa ba jira saboda sanin halin usman idan yaga wuri tofa seya tsaya hira koya kalota da kanshi.
Hanyar sharaɗa kai da ƙafa usman ya karya kanshi tare da bin kwaltar unguwar ɗoɗar...............

_DAN ALLA DAN ANNBI S.A.W KU SANI CIKIN ADDU'ARKU BANI DA LAFIYA_ ðŸ™ðŸ™ðŸ˜­
11/14/21, 3:06 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
    {  _HOT LOVE_  }
           

         NA
*AUTAR MANYA*

*Alhamdulillahi dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah buwayi gagara misali, haƙiƙa naga ruwan ƙauna a wajan masoyana, yadda naita cin karo da saƙonninku ta ko ina wasu na kirana wasu na turomin ta watsapp akan rashin jin daɗin danai na kwana biyu, nagode nagode! Allah yasaka da alkairi, HAIDARA YACE AGAI SHEKU* 😜

_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._
                            

                       *33&34*
Chapter 25 · 0% Book details