← Book details Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 115

Sashe 26

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Cikin mintunan da basu gaza ashirin ba usman ya parker Motarshi a bakin layin gidansu Æ´an biyu.
Ɗan kallonshi Ali yayi tare da cewa"Malam sefa ka ɗaga ƙafafu sabida naga garin akwai hadari sosai, murmushi usman yayi tare da kallonshi.
"Ai fitowa zakai mu ƙarasa tare wallahi unguwar babu nepa nikam tsoron layin nake yacika duhu, bazanje a sokan makami ba".
YafaÉ—i hakan da iyakar gaskiyarshi, cikin zuciyar Aliyu dariyace fall tayaya usman ze daina bashi dariya a rayuwane.
"Kaga malam nifa daga nan babu wani inda zanje, to inda babuni yaya zakai? waikai kullum kamar ba namiji ba".
YafaÉ—i hakan yana jan site É—in kujera ya jingina kanshi, yana lumshe idanunshi yana jin jikinshi yay mugun gajiya sosai.
"Plsssss É—an uwa kaiwa girman Allah mu karasa wallahi tsoron layin nakeji bazan iya shigaba, idan kuma bazaka rakani ba, mutafi kawai na hakura".
Usman yafaɗi hakan tare da haɗe hannayenshi waje ɗaya alamun roƙo.
"Wuce muje amman gaskiya ka takurani",yafaÉ—i hakan yana balle marufin motar ya fice.
Wata sassanyar iska ya shaƙa wadda take gab da zubo da ruwan sama.
Gaba yayi yabar usman yana wa motar key shikanshi lokacin daya shiga cikin layin yayi mamaki sosai sabida yadda sekai da gaske zakaga abinda ke gabanka seda ya fiddo da wayarshi ya kunna tourch ya haska yana ƙara mamakin manyan kwatocin dake layin, cike da zafin nama yay tsalle ya tsallake kwatar gabanshi yay gaba tare da juyowa ya haskawa usman, shima ya ƙaraso wata kwanar suka kuma shiga a ƙarƙashin direction ɗin da usman yake masa, Abakin wani ƙaramin gida usman yaja ya tsaya tare da riƙe ƙugunshi yana ayyana wanne ne gidan, domin a kwatancen da mama tayi mishi, wannan gidan ya gane shima dai dan yanada mugun kai ne da baici ace ya shigo layin nan ya gane ba.
"Kaga wai ina ne nifa nagaji ka saman a mota", yaji muryar Aliyu a saman kunnenshi.
"A,a dan Allah kada ka barni a wannan layin wallahi bazan iya fita ba", yafaÉ—a cikin sauri tare da fito da wayarshi ya shiga neman layin mama, cikin mintuna biyu tace mishi bara shahid ya fito seya ganshi, shagon shahid ta shiga na soro ta sanar dashi sannan ta koma gaban dambun wanda ya kusan karasawa kaÉ—an.
Ƙarar buɗe ƙofar da sukaji ya basu tabbacin, ainihin gidan, baki ɗayansu baki suka saki suna karewa gidan kallo shikam Aliyu tsananin mamakinsa yahanashi ma ɗauke kanshi daga wajan.
Gidan dake gabansu ne ashe ma bawanda suka tsaya agaban nashi bane, sosai yake mamakin tayaya mutane zasu rayu acikin wannan ɗan ƙaramin gidan wanda ko girman store ɗinshi na aje lemo bai kaiba,sallamar ɗan matashin yaron daya bude wannan gidan shine ya dawo dashi daga duniyar tunaninshi.
"Ina yininku wai mama tace ku shigo daga ciki kafin a gama". muryar yaron ya faÉ—a musu cikin nutsuwa.
Ƙura mishi ido usman yayi yana ganin kamannin ƴan biyu a tare da yaron sannan yay murmushi.
"A,a jeka ce xamu É—an tsaya anan ta karasa dare yana kumayi".
Babu musu shaheed ya koma ya sanar da mama wadda take tsaye a bakin gaushin tana firfitawa.
Ɗan tsaki Aliyu yay kaɗan tare da kallon wayarshi, ƙarfe goma da kwata lallai dare yasomayi.
Tsaiwar mintuna biyar sukai a wajan kafin iska mai karfi ta soma tashi mai ƙasa-ƙasa.
Hannunshi ya saka ya kare fuskarshi yana jan tsaki akai akai sabida yadda usman ya ɓata musu lokaci akan shirmensa.
Ganin garin yana kuma narkewa yasa mama ta yafo mayafinta, waje ta leƙo cikin nutsuwa ta ƙarasa gabansu.
"Assalamu Alaikum".
Sukaji muryar babbar mace a cikin kunnuwansu.
Cikin sauri suka É—ago atare suna kallon matar wadda duhun wajan bai saka sun tantance ainihin kammaninta ba.
Cike da mutuntaka suka gaisa da mama konace suka gaisa da usman wanda ya saki fuska sosai amman shi Aliyu tunda ya amsa mata gaisuwar bai kuma cewa ƙala ba.
"Kuyi haƙuri ku shigo ciki kuɗan jira ai bai kyautu ku tsaya daga waje ba, layin namu akwai sauro ga iska".
Tafaɗa tana ƙoƙarin juyawa.
"Tom mamanmu mungode fa ƙwarai".
Usman ya faÉ—a tare da fusgar hannun Aliyu yay gaba.
Agarin kokarin su shiga gidan seda Aliyu ya bige ƙeya sabida tsahonshi yaywa kofar soron yawa, sannan sukai sallama suka shiga ciki.
Tabarma ta baxa musu a ƙasa suka zauna, konace usman ya zauna danshi gogan tsaye yay yana naɗe ƙafarshi ajikin garu.
Yana mamakin kankantar tsakar gidan sedai kuma akwai ainihin tsafta wadda ita ta bashi damar tsayawa domin inda baiga tsaftaba da bazai tsaya bama.
amman cikin ranshi yajawa usman tsaki yafi dubu tabbas agarin kwashe kwashen usman wallahi seya kai kanshi inda baze fitaba.
Mama É—aki ta shiga saman siff ta saka hannu ta É—auko babbar kular abinci sabuwa data saiwa su hassana ta tari guda biyu, É—ayar ta É—auka sannan ta fito hannunta dauke da fitila wadda ta bawa tsakar gidan damar gauraya da haske.
Kallo ɗaya Aliyu yaywa mama yay ƙasa da kanshi sabida tsananin mamakin ganin ainihin kyau ɗan gaske a tare da ita, sosai yaji tausayinta ya kamashi mace kyakykyawa amman sedai babu wadata, sunkuyar da kanshi yay kasa yana ayyana lamarin wannan rayuwa, shima usman lokacin da haske ya bashi damar ganin fuskar mama yayi mamakin madarar kyawunta sedai rashin wadata atare da ita amman jajur mama take tabbas dole ƴan biyu suyi kyau wannan kyanta su sami wadata a tare dasu da babu abinda ze hana murjewarsu tafi ta da.
Akan kujera ta aje fitilar tare da cewa.
"Waini kam dawa nai waya acikinku ne har yanxu ban shaida É—an nawa ba?" tafaÉ—a tana karasawa gaban rariya ta zuba ruwa cikin kular tana wanketa.
"Nine mama bakiga muna kama dake ba? nifa farine wancan kwa ƙanina ne yanxu na ɗaukeshi daga airport" usman ya faɗa yana dariya, takaicine ya kama Aliyu wannan zubda mutuncin na usman har ina, amman bai ce komaiba sema wayarshi daya fiddo jin sako ya shigo, khadija ce ta turo mishi msg wai akan tana jiranshi bai shigoba tsaki yaja tare da mayar da wayar aljihunshi.
Murmushi mama tayi tare da nufar gaban gaushin da dambun ke kai tana furta"To Allah ya muku albarka baki É—ayanku".
Tare da bude murfin tukunyar tana duba dambun.
Sosai usman kewa mama labari akan yadda xainab ta rike mishi wuta akan son dambun nan yana daga zaune yana mata bayani tana amsa masa yadda ya kamata cike da kulawa gefe guda kuma tana mamakin sabo irin nashi amman kuma tana daɗa mamakin miskilancin ƙanin nashi wanda tundaga gaisuwa bai furta komaiba dantaga ma yanayin shi kamar a takure yake da gidan nasu ma baki ɗaya.
Gefen Bebi wata mahaukaciyar yunwace ke cin cikinta domin har wani irin murÉ—a mata yake tun tanajin dadin barcin harta dira aguje tayo tsakar gida, jikinta sanye da É—aurin zani se Vest É—in data saka tun lokacin da tana ciwon marar É—azu kanta babu É—an kwali se kitson kalabar daya zubo mata wajan keyarta ya rufe mata fuska sabida kasancewarta bamai yawan sumar kaba.
Bakin rariya taje ta É—ebi ruwa ta wanko fuskarta sam idanunta bai ga wasu mutane a tsakar gidanba...................
11/14/21, 3:06 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
{ _HOT LOVE_ }

NA
*AUTAR MANYA*

_Albishirinku iyayen yara dama yaran baki ɗaya, shin ko kinsan shararriyar tashar nan ta youtube mai suna *Abdur-rahman* ta shirya tsaf domin baku gudunmawa wajan tayaku bitar karatun ƴaƴanku cikin sauƙi?, Kai dai/ kedai maza garzaya wannan shararriyar channel ɗin domin ki dannawa yaranki dansu karu da zazzaƙar ƙira'ar da *Abdur-rahma* ke gudanarwa wajan bitar karatun alkur'ani mai girma acikinta daman sauran littattafan addinin islama kada ki manta da danna *SUBSCRIBE* tare da ƙararrawar sanarwa mungode_
https://youtu.be/PFTnz8JGFfQ

_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._

*35&36*
Chapter 26 · 0% Book details