Sashe 39
Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
soma zuzzuba musu abincin da sukazo dashi acikin flate, koda ta mikowa Aliyu girgiza kanshi yay bai amsa ba, sema saɓar ƴaƴan nusaiba da yay yabar musu falon. Zama sosai su ammi sukai suna hirarsu tare da yaransu kamar wasu abokai daman wannan ce al'adar abba yana son yaga ya tara yaranshi tare da ƴan jikokinshi sun xauna suna hirarsu kamar babu gobe, haka xalika suna da kyakykyawar fahimta da surukansu matansu ya abbakar waɗanda suma suke kyautata musu sosai musamman anty zee matar usman wadda take ƴar ɗakin ammi. Sun jima kafin mazan suyiwa su abba sallama suka bar falon suko su nusaiba zama sukai suna hirarsu da abba da ammi har zuwa wani lokaci kafin suyi sallama sabida dare yaɗan ja. Aliyu yana fita bedroom ɗin ammi yaje kwantar da ƴaƴan nusaiba yay sannan ya fito cikin falonta ya xauna ƙafafunshi zube bisa table, hannunshi ya ɗora akanshi. Har tsawon lokuta yana xaune seda yaga shigowar su ammina sannan ya ɗaga kai ya dubi agogo wajan karfe goman dare dan haka ya mike ya koma falon abba. lokacin dayay sallama ammi tana zubawa abba black tea a cikin cup, da hannu abba yay mishi alamun dayazo gareshi. Babu musu ya nufi gaban abba ya ɗanja baya kaɗan ya zauna yana tanƙwashe ƙafafunshi. "Babana waya taɓamin kai naga tun ɗazu ran ƴan mazan a haɗe yake gajiyar office ce ko?". Abba ya faɗa cikin kulawa. Sunkuyar da kanshi yay kasa yana ayyana damuwar auren nan tafi gajiyar office dubu amman sabida tsabar zurfin cikinshi seya cewa abba. "Naxo muyi wannan lissafin wallahi baccine a idanuna abba daman na jira kane harka nutsu". Murmushi abban yay. "Kai wannan baban nawafa akwai tsabar kaf kaf da kudi wato ashe kai zaman jira kai to maza ina jinka". Abba ya faɗa yana mayar da hankali kansa lokacin ammi ta mikowa abba cup ɗin tea, sannan ta kuma haɗo wani ta miko wa ali. "Amshi maza shanye ban kofin domin nasan bakaci komai ba ka tsaya bakin rai". Cikin damuwa ya amshi kofin yakafa bakinshi tass ya shanye sabida babu zafi sosai. Sannan ya mike tsaye mintuna biyu yaje gaban frij saman yaɗan laluba ya ɗauko white papper wadda ya ajeta gaban abba yazo da ita dalla dalla yake zayyanewa abba abinda yake cikin takaddar wadda babu komai cikinta face tsantsar lissafi na cigaban da aka samu acikin kamfaninsu na wannan watan. Abba yay farin ciki yaji daɗi sosai wanda murnar harta kasa buya. Duk yaranshi babu wanda yakejin daɗin tafiyar da business ɗinshi kamar Ali sabida yasan kanshi abba yana jin dadinshi yana kuma alfahari dashi over. "Haƙiƙa ina godiya ga Allah daya azurtani dakai babana Allah yaywa rayuwarka albarka kaji". "Amin abba sedai kuma......., yakasa karisawa. "Sedai me? faɗi mana komeye zan maka matukar baifi karfina ba, kuma matukar ba zancen fasa aurenka da khadijaba domin kasan wannan aure babu fashi sedai idan babu raina kona alhaji babba". "Abba seda safe Allah ya bamu alkairi". Yana faɗin hakan yay saurin tashi yabar wajan ranshi na suya. "Amman Alhaji yakamata fa aduba lamarin yaronnan". Muryar ammi ta karade falon cikin nutsuwa. "Dakata! Balkisu banson zancen banza duk duniya bamuda kamar alhaji babba tunda ya bada umarni bamu isa muce damme ba, dama naga take takenki wallahi harda hannunki wajan kara tunzurashi a ƙin wannan aure". Yafaɗa yana huci. "Allah ya baka hakuri ni ban isa na hanashi aure ba tunda nima fatana kenan kullum Allah ya sanya alkairi amin". Tana faɗin haka ta mike tabar falon sabida tasan halin abba yanzu se iya rufeta da faɗan tana ɗaurewa Aliyu gindi. Ɗakinta ta koma tai kwanciyarta tana addu,ar Allah ya basu zaman lafiya. Washe gari dawani irin ciwon kai aliyu ya tashi wanda ya hanashi fita office sannan ya kulle kanshi a ɗaki, sabida hayaniyar ƴan biki da suka soma cika gidan. Se wajan dare ma ya kunna wayoyinshi anan yayta cin karo da sakon taya murna wanda abokanshi da sauran jama,a ke mishi wanda yasan usman ne yayta yawo da zancen auren nashi. Wajan taran dare gidan yay tsit saukowa yay xuwa falon ammi wanda babu kowa ciki se masu aiki,yana kokarin fita sabida tun jiya da daddare rabonshi da wajen ko sallah ma yau a ɗaki yaytayin abarshi wayarshi dake cikin aljihun wandon jeans ɗin dake jikinshi ce take faman ringing dubawa yay yana kokarin fita ganin bakuwar number yasa yay banza da ita haka aka cigaba da kira kamar babu gobe. Khadija wadda taci kwalliya ta alfarma tana gidan make up tana jiran angon nata yazo su wuce wajan event ɗin da tun ɗaxu suka ɗai ake jira ita ke faman doko mashi kira da ɗayan sim ɗin nata, gefe guda ƙawayenta na familyn su, sun zagayeta suna faman zuba mata hotuna sabida khadija ita sam bata da yawan kwashe kwashen kawaye yawanci ƙawayen nata ƴan gidane sa'anninta na familynsu. Ido jajur take kallon jawa ɗiyar alhaji babba. "Jawahir kinga yaya bai ɗauka ba kodai bazeje vane tun ɗazu su umma kemin waya". Murmushi jawahir tai tana cewa. "Haba dai yayafa usman ya bamu tabbacin xuwansa kinga kawai mukira ko yaya fahad ne yazo muwuce tunda time yana ja kawai ma hade acan". Tura baki khadija tai. "Nikuwa nafison naga gani gashi muna tafe ana ƙyasamu a hoto". Tafaɗa tana lumshe idanu. Seda jawahir tai da gaske sannan khadija ta yarda suka kira fahad yazo ya daukesu lokacin da sukaje waje ya cika makil da ɗan adam. Hotuna akaita faman yiwa amarya da kawayenta. Zama tai a high table tana kuma kiran layinshi sedai wannan karon swich off usman ma bata sami damar ganinshiba sedai matarsa zee take faman barin kudi, haka akai taron aka gama khadija na kukan zuci. Ganin an dameshi da kira se kawai ya kashe wayar ya koma ɗakinshi tea ya haɗa daɗan biscut ya zauna yasha sannan yay wanka ya kwanta. Rana bata ƙarya sedai uwar ɗiya taji kunya. Yau ta kama ranar juma'a ɗaya ga watan ɗaya dubban manyan mutane na cikin kasarnan dama kewayenta suka shaida ɗaurin auren ALIYU IDRISS MAI ATAMFA! DA KHADIJA YUSUF MAI ATAMFA! cikin sadaki mai daraja can na hango usman yana faman baza babbar riga kamar angon, se faman baje baki yake ransa fess kamar shi akewa bikin. Sanye ike cikin ɗanyen boyel royal blue anmasa ɗikin half body, se hular daya saka wadda tai marching da kayan jikinsa yay mugun kyau duk da rannan yana haɗe amman bai gaza fita da tsantsar kyawunshi ba. Zamewa yay sabida kanshi daya soma ciwo yabar usman da tarin abokanshi ya gudu gida samanshi ya hau yasha magani ya kwanta. Sosai akai taro na bikin wanda ya cika da manyan mutane ammi ma tai rawar gani sosai wajan kawata bikin ɗan nata sedai hankalinta yan wajanshi sabida ta jima bata ganshiba. Se dare Jama,a suka ɗan lafa sosai umman khadija tai mata huduba wadda sam khadija bata hau kan ko guda ba, haka anty karima kanwarsu abba tazo taja hannun khadija har part ɗin alhaji babba yay mata nasiha mai ratsa jiki, sannan aka kaita wajan abba shima, zaunar da ita sukai, gabansu sannan abba ya dauki waya ya kira gogan. Yana zaune ya dafe kanshi yana mamakin waishi akawa auren dole, kiran abba ya dawo dashi daga duniyar tunaninshi. Babu yadda ze haka ya zira black jallabiya akan boxern jikin nashi, sannan ya ɗauki wayoyinshi ya sauka zuwa falon abba. Ammi da abba zaune se wadda yagani tana zaune gabansu ta rufe fuskarta. Sallama yay tare da zama gabansu kana ya gaisarsu. Cikin tsanaki abba ya dubi Aliyu tare da fara yi mishi nasiha mai ratsa jiki wadda rabinta akan rayuwar aure take tare da rikon amana na aure, daga karshe ya riƙo hannun khadija ya damƙawa Aliyu. "Ka riken ita amana da mahaifinta dani uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya ka rikemin ɗiyar yusufa da kyau! domin katayamu rike amanar daya rasu yabar mana kaji babana". Abba yafaɗa idanunshi yana kawo ƙwalla. Sannan ya juya ga khadija itama yay mata nasiha sosai wadda babu abinda take se faman kuka! Yana kammalawa ya dubi Aliyu. "Tashi kuje ɓangarenku akwai key jiki komai yana kintse office daman nace ka huta duk sanda kai ra'ayi ka koma". Haɗe ranshi yay tamau. "Abba ko kayana banyi parking ba pls ta kwana anan gobe insha Allah semu koma can ɗin". A zafafe ammi ta ɗago kanta. "Ban amince da shiga haƙƙin iyaliba,a matsayina na mahaifiyarka wadda take da hakki akanka wallahi idan yau baka saukewa marainiyar nan ta gabanmu hakkinta na auratayyaba ban yafe maka ba, sabida nasan halin taurin kanka ƙila yadda zaka jeda ita haka xaka barta ko kallo". Dum! Dumm!! yaji gabanshi yay mugun faɗuwa akanta mahaifiyarshi ke faɗin haka. Amman ammi ta ɗora mishi mugun nauyin daya xama dole ya saukeshi. Ita kuwa ammi ta faɗi hakanne sabida kwaɗayin kota dalilin hakan Allah ze karkata hankalinshi kan khadijan su zama masoya na hakika amman har cikin ranta kawai tafaɗi hakanne da wannan manufar bada wata ta daban ba. Shikanshi abba yay mamakin furucin ammin amman baice komai ba. Itako khadija shiwa ammi albarka take sabida ta matsu matuka. Da sauri yace. "Zanyi ammina kimin gafara karki sake dan Allah kimin mugun baki". Nisawa tai. "Allah yay maka albarka maza tashi kaja matarka kutafi Allah ya sadamu da alkairinshi amin,". Wuff ya mike yabar falon yana tafe yana hada hanya. Ta kofar baya yabi sabida har yanzu akwai ƴan biki. Daga part ɗin ammi zuwa nasu akwai tafiya yana tafe kamar marar lakar jiki. Ita kuma tana bin bayanshi kamar cingam ranta fari fess yau xata kwana kan faffadan kirjinshi datake mugun marmari. Ƙayataccen part ɗinsu ya tura gate ɗin ya shiga da sallama sannan ya karasa gaban katuwar kofar glass ɗin da aka kawata, babban falonsu ya shiga yana sallama abakinshi. Sosai yay mamakin yadda aka kashewa part ɗin kuɗi ba kaɗan ba,sama ya haye inda bedroom's ɗin gidan suke still tana biye dashi abaya. Cikin bedroom guda ya shiga tare da faɗawa daman babban bed ɗin dayaji white bedshit yay mugun kyau. Akanshi ta tsaya tana xare idanu batare data xauna ba. Zumbur ya mike ya nufi hanyar bathroom alwala ya dauro tare da fitowa sumar kanshi jike da ruwa. Tsareta