← Book details Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 115

Sashe 36

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da wani iri mahaukacin gudu taga yaja motar yabar wajan kamar ze tashi sama, jan ƙafafunta tayi, waɗanda sukai mata wani irin mugun sanyi ta soma nufar cikin layinsu abinda yay matuƙar bata tsoro shine yadda ta hangi shahid tare da wani babban mutum fari, suna tsaye da alamun magana suke sedai kuma duk hankalinsu yana gurinta,Cikin sanyin jiki ƙalau take sarrafa ƙafafunta, tanajin wani bakon lamari atare da ita, tunda take bata taɓa ganin irin kallon da wannan farin mutum yake mata ba, kallone mai cike da tarin ma'anoni kala-kala, cikin tsananin dauriya wadda tai mata saura ta wuce ta gabansu batare data yiwa kowa magana acikinsu ba.
"Habawa ga irinta nan! ai nafaɗawa su Rabi'u sunƙi ganewa nace daman Aisha ta riga ta nunawa ƴaƴan musa, bariki kai! babana wannan ba Bilki bace ba?".
Wannan farin mutumin ke tambayar shahid cike da zaƙuwa.
Cikin rawar jiki tare da tsantsar mamakin Bebi shima shahid É—in yake É—agawa wannan mutumin kansa alamun Eh itace.
Gefe É—aya kuma ga Æ´an siyan gawayin shahid duk sunyi tsuru suna sonjin meke faruwa, ganin haka yasa shahid ya soma nufar hanyar gida.
Cike da wani irin tsoro Bebi take tura buhun kofar gidan nasu, da mama da hassana suka kusan cin karo, kusan a tare mama da hassana suka sauke wata ajiyar zuciya hassana batai wata  sanyaba ta wankawa Bebi wani bahagon mari a saman fuskarta, cikin kuncin zuciya mama taja hannunta ta wurga cikin gida.
"Daga motar ubanwa kike Bebi na shiga uku! ni aishatu Allah ka dubeni"!!
"Ai bakiga komai ba bala'i da masifa! yanzu kika tsoma ƙafa cikinsu munafukar Allah daman anjima ana kawo mana maganarki munyi biris dakene muga iya gudun ruwanki! to wallahi baze yuwuba dole mu dage akan ƴaƴan ɗan uwanmu, domin baxaki maishe su karuwan gida ba, tabbas yau inda wanine yaga yamin zanyi karya.amman da idona naga Bilki ta fito daga wata sheɗaniyar motar da duk garin nan bantaɓa ganin irinta ba, Dan haka ina son ki tattare dukkan kuɗin karuwancin ƴaƴanki ki sai musu gado dan daga nan zuwa kowani lokaci zamuzo da taron ɗaurin auren su da duk wanda mukaga dama"!!!
Yana gama faÉ—in haka ya baza babbar rigarshi yabar gidan.
Zubewa mama tayi awajan tana kuka! maicin rai wanda yay mugun É—agawa yaran nata hankali.
Cikin gigita hussaina ta fito daga É—aki tana riko mama.
"Dan Allah mama kibar kuka! babu wanda ya isa yay mana abinda Allah bai mana ba, ita kuma Bebin data jawo mana zubewar mutunci wallahi sedai abin ya ƙare a iya kan........", "Kull hussaina kada na kumajin wannan maganar daga bakinki", mama ta faɗi hakan da sauri sannan ta miƙe gaban Bebi taje ta riko hannunta sukai ɗaki.
Su hassana ma ganin haka yasa sukabi maman ciki, Zaunar da Bebi tai agabanta.
Tare da daure fuska tamau wadda bebin bata taba ganin irin haka daga wajan mamar ba.
"Bebi waya sauke ki daga cikin mota, kuma daga ina kike har ƴar uwarki ta dawo ke baki dawo ba?" mama ta buga mata wata shegiyar tsawar data mayar da ita ƙasa babu shiri.
"Mama wallahi babu abinda ya faru kawai..............", tas ta kwashe komai daya faru ta gayawa mama, amman bata gaya musu cewar ga wanda yay mata hakan ba, kuma bata nuna cewar Aliyu É—an uwan usman bane ba, sannan duk bidirin da sukai nan ma bata faÉ—a ba, sabida gudun zargi wanda ita dakanta tasan cewar bawai da gangan komai ya faru ba face tsabar son jikinta daya ja mata baccin daya kaita ga faÉ—awa cikin wannan matsalar abinda yasa kuma bata nuna É—an uwan usman ne yay mata hakan ba nan ma gudun wata matsalar wadda tasan mama xata iya yin wani tunanin na daban akanta.
"Idan banda sakarci da wawanci ina ke ina bacci a wajan sana'a yanzu shiɗin bada ban na Allah bane ba kina tunanin baze iya yin lalata dake ba?" ta inda mama take shiga bata nan take fita ba seda tai wa bebi faɗan da bebin da sauran basu taɓa zaton mama nadashi ba.
Kallon Æ´an biyu tai tace suje su gyara tsakar gida ita kam zancen fita tallen nan ma tana tunanin zata É—agashi.
Suna fita É—akin ya rage daga mama se bebi, kallon bebi mama tayi tare da cewa.....
"Zonan Bebi".
TafaÉ—a fuskarta babu alamun wasa bare sassauci.
Tasowa tai jikinta yana wani irin rawa tana ayyana cewar ita kam taga takanta yau am!
Tsira mata idanu tai tare da nazarinta cikin hikima.
Tagama caje jikin Bebi bataci karo da komai ba seda mayen ƙamshin daya sa tajawo Bebin saman cinyarta babu shiri, hawayene ya soma zarya a saman kuncin mama.
"Bebi waya rungumeki? wannan sauyin ƙamshin bansan shiba daga jima wannan turaren daga duk inda yake na manyan mutanene dawa kika haɗa jiki a kamfani?".
Mama ta faÉ—a tanajin tsoron kar wani abu ya sami É—iyar tata wanda bata fatanshi insha Allahu.
"Nacewa ƴan uwanki su fitane sabida gudun sumiki kallon bai bai! nai miki bahaguwar tambaya a gabansu domin na karkatar dasu ga mugun zargi kinsan zuciya, a wannan karon Bebi kada ki ɗauke ni a komai face mahaifiya mai fahimtar ƴaƴanta kiwa girman Allah ki gayamin dukkan abinda ya faru nai miki alkawarin zan miki fahimta mai kyau! Bebi bana son rayuwar waninku ta sauya daga irin tarbiyar danai muku bani da uwa bani da uba babu yaya bare ƙani mahaifinku danake so Allah ya rabani dashi kune kaɗai sanyin idaniyata idan wanin ku ya shiga matsala ina ganin bazan dena zubda ƙwalla ba, kina kallon irin sharrin da ɗan uwan mahaifinku yazo yay muku wanda ni bata tasa nakeba a ɗazun face ta rudewar fitowarki daga cikin motar damuka ga kinyi a ɗazun nida hassana mun leƙo muna hangen dawo warki".
Tafaɗa idanunta still dai yana ɗigar ƙwallah.
"Mama wallahi baimin komai ba, wannanfa É—an uwan wanda suka zo jiyan nan ne É—aukar dambu, shine hussaina ta bani alale na kaiwa wancan É—ayan, to ban saniba naje ofishin sa.............." komai seda ta gayawa mama bata rage ba, hatta faÉ—an dayay mata harma da buge mata bakin dayay akan rashin kunyar datai mishi bata rage ba.
"Alhamdulillahi!, cewar mama sannan ta dubi Bebi da kyau.
"Kiramin hassana da hussaina duka har shahid ma naji muryarshi a waje".
Sum sum ta mike taje tazo dasu dukkansu sunka zube gaban mama suna sauraranta ganin ta tsaida hankalinta garesu.
"Ina son dukkanku kujini da kyau! Ke hussaina ban yarda daga yanzu idan kunje wajan talle da wani acikinku kice masa yaje kaiwa wani abinci office ba, kina jina duk wanda yakeso ze iya zuwa ya siya idan kuma baida lokacin karba ku aje mishi harya gama abinda yake yazo ya É—auka, tabbas inda inada yadda xanyi wallahi baku kuma tallah amman babu komai ina mikawa Allah lamuranmu baki É—aya...........Se abu nagaba kuma bana son kuyiwa yar uwarku bahaguwar fahimta kunsan dai halinta da sakarcin tsiya ke ashe dataci dambun É—azu kwanciyar ta tai a bayan masallaci tai sana'ar tata ta bacci shine fa lokacin da usman yazo shigewa ya ganta anan yasa aka tasota ya bawa drivern sa makullin mota ya kawota gida, kunsan ita bebi bata rabe da usman ba seda taimin kwatance yanzu na gane nima, dafan kun fahimta insha Allahu yadda na baku tarbiya ina fatan kujewa mazajenku da ita in sha Allah".
Mama tafaɗi hakan domin ta kuma wanke bebi cikin ƴan uwanta gudun zargi kunsan zuciya ba ƙashi.
"Insha Allahu mama zamu kiyaye".
"Gobe ma ku zauna kawai bazamuyi ba ku huta hakan nan inada shinkafata harta jibi insha Allahu babu wani inda xaku kuma zuwa, ni babban tashin hankalina ma wannan dangin mahaifin naku Allah yay mana tsari da sharrinsu".
Sannan ta juya gaban shahid.
"Ina ka haÉ—u da tasi'u sannan kuma waya nuna mishi nan unguwar ma?".
TafaÉ—a cike da mamaki.
Sosa kai shahid yay kana yace.
"Wallahi mama yadda kika ganshi haka naganshi É—azun yazo wajena ina bawa wani gawayi sedai alamun ma bashi É—aya bane, seda na gama sannan yazo yana cewa wai ban ganeshi ba sabida uwarmu bata nuna mana suba, murmushi nayi sannan nace masa haba baba naganeka mana sedai ban san sunanka ba sabida rabona daku tun ana goyon bebi, shine yake tambayata wai inane gidanmu nikuwa na nuna mishi to muna tsaka da magana bebin ta fito daga mota shine ya kureta da idanu yana kallonta harzata gifta yake cemin wacece nace masa bebi ce shine fa ya biyo bayanta haryay miki wannan cin zarafin".
Shahid yakai maganar yana kallon mama.
Murmushi tayi sannan ta dubesu.
"Tabbas yau naga tasi'u gobe ko anjima xanga sani da rabi'u kuma zuwan nasu babu alkairi sedai sharri ina fatan Allah ya tsallakar damu ai daman yanxu kun zama mutane na tabbata akwai wata a ƙasa zuwansu akwai lauje cikin ɗani, maza kumu fita muyi aikin gabanmu".
Mama tafaÉ—a cikin dakewar zuci.
"Mama mekuma yay saura seda muka zama mutane sannan zasu nememu nifa ko a hanya na gansu bazan shaidasu ba"..
"Kull hussaina banson maganar raini ta shiga tsakaninku da Æ´an uwan mahaifinku iko akeson nunan na dangin uba nikuma zan nuna musu Ni uwace maba da mama"!!!
Mama tafaÉ—i hakan tare da mikewa.
Seda takai kofa sannan tacewa Bebi taje tai wanka ta sauya tsumman jikinta sannan tazo ga abincinta kana suka fita suna cigaba da mai maita maganganun da baba tasi'un ya gayawa mama.
Suna fita bebi ta koma ragwaf ta kwanta baki É—aya tunaninta ya tsaya cak!
Abinda ta iya faÉ—a shine.
"Duk inda xanyi sena nema ka na gaya maka magangun son raina É—an iska kawai babu gaira babu dalili yazo yajazamin masifa".
TafaÉ—i hakan tare da shafa gefen bakinta wanda ya kumbura sumtum.
"Bebi gafa ruwan wankan nan kada ya salance".
Tajiyo muryar mama wadda yasa tai maza ta tube kayanta tare da fita tsakar gidan a É—arare.

Shikuwa Aliyu dawani irin mugun gudu yaja motar...............
Chapter 36 · 0% Book details