← Book details Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 115

Sashe 108

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

kuma auren baba Ali yazaman ishara tabbas rabo ma kaɗai ze iya kasheni dan Allah ƴaƴan nan kumin afuwa waɗanda na tursasa sukai auren dole duka kuyi hakuri daga yau najanye wannan al'adar tawa kowa yana da damar AUREN BARE! amman nagartacciya mai tarbiya, tabbas idan har iyaye zamu dinga tilasawa yaranmu auren da basa so tofa za'a iya haifar ɗan da baida idanu, tabbas wannan ma isharace gamu iyaye mu dinga yiwa ƴaƴanmu adalci sabida tsanani tilasawa yaro yana sakawa ya bujirewa mahaifa musamman Aliyu wanda ban taɓa masa magana ya musan ba bantaɓa ganin ɗan albarka kamarshiba baya musu haka nan baya saɓa mana amman yau harni ze duba yace kozan mutu baze saki matarsa ba ya kalli idanun ubansa baiji kunya ba lallai soyayyar shi da wannan yarinya takai ta kawo wallahi inda ba'ai auren bama za,a iya haihuwa a titi, kai idriss karkai fushi da ɗanka maza kai masa afuwa Allah yay muku albarka gaba ɗaya, haka zalika kema bilkisu nasan rankine ya ɓaci har kika jefamin kalamanki na ɗazu abinda baki taɓa min ba tun aurenki agidan nan kikemin biyayya duk tursasawar dazanwa ƴaƴanki baki taɓa ɗaga ido kin dubeni ba sabida haka ban rike ki araina ba Allah ya baki hakuri yayi maki albarka keda zuri'arki Amin" Amsawa dukkan mutan falon sukai gaba ɗaya. alhaji babba yaji jikinshi yayi sanyi, daman shi abba marinma dayay wa ɗan nasa dan dai kar alhajin yaga kamar ya daure masa gindine amman shi tun kalaman alhaji isyaku yaji jikinshi yay sanyi tabbas yayi godiya ga Allah dayasa ba ɗan shege aka kawo masa ba. "Zonan ƴar albarka kiyi hakuri do Allah kada ki rikeni akan nace asake ki kiyi haƙuri ɗiyata" Alhaji yafaɗawa bebi haka yana kallonta wadda tun ɗazu ta raɓe tana jin duk maganganun nasu bata ɗago ba sema kasa data kumayi da kanta domin ita kaɗai tasan a halin data ke ciki. Abba ne ya ɗago kansa batare dayace kamai ba. Yadai zubawa Aliyu idanu yana kallon yadda gaba ɗaya hankalin Aliyun na kan matar tashine data sada kanta kasa taƙi kallon kowa. Addu'a abba yayi tare da sallamar kowa ya kama gabansa amman yacewa iyalinshi su samesa a falonshi harda surukanshi kaf. Kowa tashi yayi yana murna, ammi da kanta tazo gaban bebi ta ɗagata suka wuce can part ɗinta. Abakin kofa dija ta tsaya tana turawa umman ta baki. "Nace ki kwantar da hankalinki ko? wannan marar kunyar yaron tunda ya furta maganar dayaso agaban alhaji wallahi akan waccan ƴar ze iya sakinki kinafa kallo ciki gareta ke bazaki kwanto ki samuba,so kike ki ɗaga hankali mu tashi a tutar babu? akanta fa yau Alhaji ya rusa al'adar da aka gina sama da shekaru ashirin a wannan zuri'a tamu" "Amman umma kishiya fa nidai ina son mijina ina kishinsa" Murmushi umma tayi. "Kamar yaya kenan ban fahimta?" "Ina son ya Aliyu tun farko sabida Allah wallahi umma na yada makaman yaƙina na cewar dan dukiyarshi zan zauna dashi nidai kimin addu'a domin yanzu zan fuskanci ƙalubale akanshi Allah yagani inason sa dukiyarshi bata gabana nagane so yanzu na kuma gane son kuɗi" Mamaki khadija ta bawa, umman tata wadda tsabar zafin maganar yasa umman jan tsaki tabar mata wajan. Part ɗin ammi dija tayi duk tanajin babu daɗi aranta. Gaba ɗayansu ta samu a falon abba,hadda bebi datake raɓe jikin ammi taki kallon kowa ma a falon. Gyaran murya abba yayi sannan ya dubi Aliyu. Cikin tsanaki yagama masa nasiha tsaf sannan ya nusarshi kuskuren dayay akan maganganun shi na gaban alhaji daga karshe ya ce masa lallai koyau ko gobe yaje ya bawa alhajin hakuri. Itama ammi nasihar yay mata tare da cewa taje ta bawa alhajin hakuri sannan yahau ya abbakar da faɗa sosai akan kuskuren da sukai shida usman itama khadija nasiha yay mata sannan ya kirawo bebi itama kamar yadda yaywa khadija nasihar zamansu lafiya haka yayi mata, daga ƙarshe yahau yima su usman tsiya harda cewa daman rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya ta mai kaya. Addu'a akai aka shafa daga karshe kuma aka hau hirar bikinsu amina tashi abba yayi yana duban Aliyu. "Babana tashi muje asibiti zanga likita nifa nagodewa Allah dayasa ba ɗan shege aka kawon ba Allah yay muku albarka ya ƙara haɗa kanku ami" Dariya suka saka gaba ɗaya sukwa ƴan biyu saka bebi agaba sukai suna damunta da surutu. Watsewa akai daga falon dija ta kama hanyar part ɗinta tana nanata maganar abba na cewa. "Amina dasu hassana zasuje part ɗin khadijan sauran extra room ɗin dake saman za,aiwa bebi jere zuwa anjima gobe zata koma can da zama domin yafison ya haɗe iyalanshi waje ɗaya daga yau maganar rabuwa ta kare" Yanzu shikenan zata zauna guri ɗaya da kishiya damma Allah yaso kowa da toilet ɗinshi amman kicin a haɗe falo a haɗe damma dai kowa da falonshi a bedroom ɗinshi spare guda ɗaya, yanzu yakama su suka saka Aliyu a tsakiya kenan domin ɗakin bebi yana gefen na Aliyu na dija na ɗaya gefen shima. Haka ta koma ɗaki duk jikinta sanyi kalau. Ammi da kanta ta haɗawa bebi ruwan wanka tanayi ta kwanta saman gado ba jimawa bacci ya kwasheta. Shima daya dawo daga kai abba asibiti wajan sayyyar kayan ɗaki suka wuce da amina wadda ita taiwa bebi zaɓen kayan ɗaki white colour masu kyau. Daga nan can tokarawa ya wuce yaywa su goma bayani akan sun bar nan ɗin kayayyakin shi mai amfani ya ɗauko da nata sauran tarkacen kayan abinci kuma ya bawa su goma haka ya baro tokarawa yana kewar gidan domin anan yasan bebi a cikakkar mace anan sukai rayuwa mai tsayuwa arai tabbas wannan gida ya shiga kundun tarihinshi na rayuwar shi da bebi. lokacin daya dawo gida part ɗinshi ya wuce anan ya tarar dasu amina da ƴan biyun ammi da sauran cousins ɗinshi sunata faman gyara ɗakin da bebi xata zauna sun jera kayan ɗaki yanzu falon suke haɗa mata sosai tsarin wajan ya burgeshi wajan khadija ya wuce wadda ta yada fushinta ta zage ta ringa basa kula ta musamman anan yay sallah yaci abinci ya kwanta saman gadonta wanda shine farko tun aurensu. Har su amina suka gama basuga gilmawarshi ba haka nan dijan bata fito ba itama sauka sukai suka fita lokacin magariba tayi falon ammi suka yada zango. Lokacin bebi ta tashi tana zaune a carpet tana cin taliya. Ammi tana zaune saman kujera tana jan carbi. "Washh Allah ammi yunwa mun gama amman munci ubanmu" Da mamaki ammi ta kallesu. "A,a kar ku gayan zancen banza tun wajan 2;00pm ku tafi jere amman dija bata baku abinci ba? ina baba Alin yake naga abbanku tun ɗazu yana falon shi?" Dariya hussaina ta saki. "Taɓɓijan ammi tunda fa muka bar gidan nan muke aiki dasu hidaya,wallahi anty khadija bata leko ba shima yaya Aliyun daya shigo tun la'asar yace mana sannu ya shige ɗakinta har muka fito basu leƙo muba sun kulle kansu a ɗaki" Hussaina ta faɗa cike da wauta. Dum! dum!!dum!!! gaban Bebi yay wani irin faɗuwa wani irin zazzafan kishine...................
Chapter 108 · 0% Book details