← Book details Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 115

Sashe 90

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiya soma shiga cikin shagon kafin shahid ya bi masa baya,Bakinsa ɗauke da sallama, da sauri mai shagon ya taso gami da basa kujerar ƙarfe ta zama, yana faman dashare mai haƙora. "Ah yau muna da babban baƙo Alhaji Ali Mai atamfa,ne a shagon namu kai maza kuje ku siyo masu kayan sanyaya maƙoshi". Mutumin da baze gasa shekarun Aliyun ba ke faɗin hakan wanda shine ma mallakin wannan shagon se yaransa dake ciki suna faman haɗa ledoji masu uban yawa. Murmushi Aliyu ya saki yana mai ɗaga mai hannu. "Haba mai shinkafa nifa ba baƙo bane wallahi ahanya nake ma, yawwa kayan abinci nakeso komai da komai seka saman mota ƙarama da zata ɗauka dan Allah kai sauri sekai min total na kuɗin kaimin msg ta watsapp zan maka sending ɗinsu ta account". Yafaɗa yana mai duba agogon dake ɗaure bisa tsintsiyar hannunshi. Cikin mintuna da bazasu gaza talatin ba mai shinkafa yadda naji Aliyun ya ambaci sunanshi ya shiga wani ɗaki wanda nake tunanin kamar store ne ya kira wani daga cikin yaransa suka soma fito da buhunan kayan abinci hatta su semo ba,a bari ba katan na indomie shinkafa taliya cous-cous da dukkan wasu kayan sarrafawa domin aci, Shidai shahid sakin baki yayi yana kallon ikon Allah lallai inda ake arziƙi ba,a tsiya, zama da mutumin arziki kuma akwai daɗi a rayuwa, wata ƙwallace tazo mai wadda bai bar kowa ya ganiba ya share kayarsa. Cikin ƙanƙanin lokaci suka kammala dukkan haɗa kayan abincin daya buƙata aka samo irin ƙurƙurar motar nan ta ɗaukar kaya seda mai shinkafa ya zuba kayan ya biya drivern sannan ya dawo shagon. Ya miƙawa Aliyu bill ɗin kuɗin dukka acikin wata ƴar takarda. Sannan sukai musabaha kana ya bar shagon yana ce mai. "Zakaga saƙo anjima insha Allah nagode" Yafaɗa kana ya fita wajan motarsa ya koma inda ya adanata, ya buɗe irin ɗan akwatin nan na ajiyan cikin mota rafar ƴan dubu ɗaya ya fiddo dasu ya bawa shahid. "Amsa ka kaiwa umma sekuyi cefane kaje ka zauna kusa da drivern waccan motar kuje gida tare, insha Allah wani satin kaima zanyi kokarin ganin na sama maka school kabar yawon nan na anguwa". Dariya shahid yay "lah wallahi ban yawon unguwa gawayi nike saidawa fa tunda nai neco". Murmushi yayi "To masha Allah, shahid naji daɗin yadda kake neman na kanka baka tsaya ɗaukar na wani ko maula domin abaka ba, sabida dukkan waɗannan suna kawowa mutum ƙasƙanci da raini ka zauna ka nemi guminka komai wuya kaji ƙanina nima ɗinnan daka ganni babu irin wuyar da mahaifinmu bai shaba kafin yazama haka harmu ma mu gajeshi ka ganni nan sena wuni tunanina yaɗauki zafi a office sabida tsabar lissafin shigar kayanmu da fitarsu da sarosu, kada ka yarda ka ɗauki na wani koka zauna cikin abokai marasa aikinyi sabida zama da mutanan banza shike kawo tunanin banza harma a aikata aikin banza kaji ko ƙanina". Sosai shahid yaji daɗin nasihar da Aliyu yay masa sabida tunda yake baitaɓa zama da wanda ya zauna yay masa faɗa kamar haka ba. "Nagode yaya Aliyu insha Allahu zanyi aiki da nasihar ka" Buɗe motarshi yake ƙoƙarin yi sannan ya juyo. "Zan duba takaddun naka zaka koma school insha Allahu tun yanzu zan sama maka aiki acikin kamfaninmu koda a ƙaramin section ne inyaso ranar da bakada lecture sekai tafiyar ka can kuma duk wata zamuna baka salary". Yafaɗa yana shigewa motarshi. Shahid jiyai kamar ya zuba ruwa a ƙasa yasha sabida murna, dan haka da sauri ya juya motar kayan abincin nasu ya shiga nan da nan drivern ya kama hanyar kwatancen da shahid ɗin keyi masa suka ɗauki hnyar sharaɗa ɗoɗar mota fall kaya. Kai tsaye motar su shahid a bakin layin gidansu ta dakata da taimakon matasan bakin layin aka soma fito da kayan ana, shigar dasu tsakar gidan mama waɗanda nan da nan mama da ƴan biyu sukai cirko cirko suna bin kayan da kallo cike da mamaki, sabida lokacin iya da sadiya sun tafi gida saka makon magaribar da aka soma kira. Seda suka kammala aje komai hatta jaekokin mai, seda suka ajiye sannan mama ta shiga ɗakinta ta ɗauko gudar dubunta datai ragowa tai zuciyar dogarai ta bawa matansa tana musu godiya, shahid kam komawa yayi yaywa mai motar godiya sa'annan ya dawo gida. "Masha Allah, Allah muna godiya gareka". Cewar mama cike da farin ciki suke ɗiban kayan abincin suna shigar dasu ɗaki suka jera su a can karshen ɗaki sannan shahid ya zaro kuɗin da Aliyu ya basa ya miƙawa mama yana mata bayanin dukkan yadda sukai da Aliyun a kasuwa. Mama dan murna kuka ta saka haka nan ƴan biyu suna yiwa Aliyu fatan nasara a rayuwarsa shiya soma taimaka musu acikin rayuwarsu tabbas Allah baze bar duk wanda ya share hawayen maraya ba, sakamakonsa babbane a wajan ubangiji,sallah sukai tare da saka Aliyu acikin addu'arsu sannan sukaiwa ƴar uwarsu fatan zaman lafiya agidanta. "Shahid amsa wannan dubun kaje ka siyo mana kifi, hassana kunna gawayi ki ɗora mana dafa dukan taliya mai daddawa da kifi muma muci daɗinmu Allah ka ƙarawa annabi s.a.w daraja amin". Sosai su arfa suka saka dariya suka miƙe ita da ihsan suna tsalle. Mamace ta share hawayenta tana kallon ƴaƴan nata kana tace. "Tabbas ayau Allah kaɗai yasan ɗunbin ladan da wannan bawan Allah ya samu dukkan wanda ya saka ɗan uwansa musulmi cikin farin ciki yana da lada bare, kuma acikin zuciyar maraya wanda Allah kaɗai yasan adadin ladan daze bashi, ya Allah ina roƙonka daka sakawa da dukkan mai kyautatawa maraya da gidan aljanna firdausi amin". Dukkansu suka amsa mata da amin, sannan hassana ta mike domin ƙaddamar da umarnin da mahaifiyar tasu ta bata shi kuma shahid ya fita. "Hussaina muje cikin ɗaki na fitarwa da iya da gidan malam suma kayan abincin da kuɗin ki miƙa musu suma su dandali arziƙi" Tashi sukai suka shiga cikin ɗaki. ******** Bai jima da barin kasuwarba yaji ana kiraye kirayen sallah sabida haka cikin sauri yay parking ya tsaya a wani masallacin gefen titi alwala ya ɗaura a bakin famfo kana ya shiga yabi sahun jam'i, seda ya gama lazuminshi kana ya fita zuwa mota seda ya biya ta magaji rumfa ya siyo musu wani nama wanda ake masa laƙani da suya, tare da kayan sanyi danginsu lemo da sauransu sannan ya zuba acikin mota ya kama hanyar tokarawa lokacin wajan ƙarfe takwas na dare. Babu abinda yake buƙata a wannan lokacin kamar yajishi cikin ruwan ɗumi yasha yay wanka dashi, tafiyace mai azabar nisa yayita wadda bata kaishi can ɗinba se wajan taran dare, da kansa ya sauka daga cikin motar ya buɗe gate ɗin. Cikin sauri goma dayaji ƙarar buɗe gate ya fito daga nasa part ɗin tare da hasko wajan da tourch light sabida lokacin basu rufe gidanma saka makon ragowar jama'ar gidan basu gama shigowa ba. "Au oga ashe kaine barka da shigowa yaya dare?". "Ina zuwa goma just give me a two minutes" Yafaɗa yana komawa da baya yaje ya shigo da motar ya gyara mata zama a driving in ɗin gidan kana ya kasheta ya fito hannunshi dauke da kular dambun mama da kuma babbar ledar dayay musu siyayya a magaji rumfa. Ƙarasowa yay gaban goma ya basa hannu suka gaisa. "Ka gannifa goma se yanzu na sami damar shigowa, amman yanaga gidan babu wutar lantarki?". Sosai kai goma yayi. "Wallahi oga basu bamu nepa yau ba, amman gobe zan saka a kawo mana gen kodan madam amman mukam bama kunnawa sabida ana samun nepa sosai". Murmushi kawai yay kana yace. "A daure a haɗa kam komai ka sanar min,ya maganar kayan nan daza'a kawo mana Jibi? amman zuwa gobe zamuyi magana". Murmushi shima goma yayi sannan yace mai. "Allah ya kaimu lafiya oga ai babu matsala na rigama na tura musu samfir ɗin da muke so da kuma adadin dilar amman kayan naji yace ta cikin jirgin ruwa zasu zo mana". "Okey babu matsala Allah ya shigo mana dasu lafiya kasan na narka dukiyata cikifa". "Amin oga Allah ya tashemu lafiya". Sukai sallama kowa ya nufi nasa part ɗin. Key ya saka ya buɗe kofar gidan, wanda seda ya haska da fitilar wayarshi kafin ya sami zarafin ganin hanyarshi sabida tsabar duhun dake da akwai a gidan. Kafin kuma ya juya ya rufo gidan da key ya xare ya shiga cikin tsakar gidan wanda babu komai na sauti dake tashi face na kukan ƙwaron nan gyare. Da taimakon fitilar wayarshi ya haska kofar ɗakin ya buɗe labule ya shiga bakinsa dauke da sallama seda ya aje kayan hannunshi duka a waje ɗaya sannan ya saka hasken wayarshi yana, haska ko ina bai ganta ba,seda ya haska can saman sopa sannan ya hango ta kwance da alamun tayi bacci duk ta cure cikin hijabi kana kallonta kasan acikin alhinin tsoro tai wannan bacci. Cikin yanayin tausaya mata ya ƙarasa gabanta ya saka hannu yaja yatsarta na ƙafa. Aikwa da sauri tai wata irin hantsilowa wadda bata dire a ko ina ba se a saman faffaɗan kirjinshi daddagewa tayi zata zunduma mai ihu fahimtar hakan yasa ya yarda wayarshi mai uban tsada a ƙasan carpet kana ya riƙota sosai bisa jikinshi. Ya matseta acikin kirjinta yana faman hura mata iskar cikin bakinshi. "Shiiiiii matsoraciya nine Aliyu" Yafaɗa yana daɗa matseta ajikinsa. Zamewa tayi daga riƙon dayay mata sabida aciki take dashi "To naji nika saken mana". Tafaɗa tana fincike jikinta. Ɗaukar wayarshi yayi tare da ɗorata a saman sopa wadda ta bawa ɗakin damar karaɗewa da haske. Cikin miskilancin sa ya shareta gami da wucewa cikin ɗakin batare daya kuma tanka mata ba. Komawa tai saman sopa ta harɗe tana huro mai hanci. Mintuna kusan biyar ya ɗauka a ɗakin kafin ya fito jikinsa sanye da ɗan guntun wando, Taɓɓ abinda baita ɓayi ba kenan a gaban wani. Wuceta yayi ya fita toilet yaje babu tsoro aranshi ya sakarma kansa ruwan ɗumi sannan ya ɗauro alwala ya fito. Tsuka yaja sabida babu extra kayansa agidan dole tasa ya mayar da kayansa dayazo dasu. Falon ya dawo hannunshi ɗauke da darduma ya shinfiɗa wanda adai dai nan akwa kawo nepa haske da iskar fanka suka haska falon tarwai. Babu alamun sassauci a saman
Chapter 90 · 0% Book details