Sashe 113
Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yasa ba,a gaya mata ba dariya mama tai tare da ce mata ai mijinta ne yace kada agaya mata ga sadiya nan ma bikinta sauran wata ɗaya, sosai Bebi take dariya ganin yadda su hassana sukai wata kiba wadda kallo ɗaya xakai musu kasan sunada shigar ciki. Shahid ta tambaya wanda mama tace mata ai yana ta zuwa aikinshi wajan Aliyu yana kuma zuwa makaranta, sosai bebi take mamakin zurfin cikinsa ko kaɗan bai taba gaya mata dukkan waɗannan lamura ba. Bata tsinke da lamarin bama seda mama take bata labarin case ɗin khalifa da rasuwar mahaifinshi dakuma belinshi da Aliyu ya karbo sabida tausayin daya basa, yanzu haka wai khalifa ya shiryu daman can babansa ke ɗaure masa gindin rashin mutunci. Kuma yanxu haka an mayar da auren shi da ladi tunda daman saki biyu yay mata kuma Aliyu ya ɗaukeshi aiki a kamfaninshi haka nan ta zayyane mata zancen shirinsu da dangin mahaifinsu tare da gabatar mata da waɗannan matan inna suwaiba kanwar abbansu dakuma matan su kawu tasi'u sosai bebi ta sake dasu tana kuma gaisarsu domin tasan baka mayar da sharri ga duk wanda yay maka shi kuma nagaba ai yayi gaba na baya se labari. Mama ta kara mata da nasiha. "Dan Allah bebi ki rufa mana asiri ki zauna lafiya agidan ki duk da naga sauyi sosai atare dake kuma ki kara yi masa godiya bakiga gidanmu ba yanzufa sekin ɓata in kikazo gaskiya Allah ya sakawa da wannan yaron da alkairinshi amin" Sosai jikin bebi yakuma yin sanyi takuma jin kaunar Aliyu har ranta wanda yazama HASKE gareta yazama HASKE ga ahalinta bata da abinda zata ce masa sedai fatan addu'a da kuma fatan nasara arayuwarsu. Har dare su mama suna gidan sosai ta sake dasu hassana sunata hirarsu,anan taji labarin tafiyar hussaina abuja sabida transper da ya nura ya samu zuwa babbar kotun kasa dake birnin taraiya. Har kuka bebi tai dataji irin dadin da ƴan uwanta da mahaifiyarta suke ji lallai rayuwa babu tabbas kuma dukkan tsanani yana tare da sauƙi komai nisan jifa dole ƙasa ze sauka ada sun taso a kunci amman da sannu komai ya koma tarihi. Yanzu mama bata da wata matsala su ihsan ma suna ta makarantar su batare da wata matsala ba. Da kansa ya zuba su mama a motarshi ya kaisu gida wanda tun a mota suka tsinke da daular da sukaga Bebi acikinta lallai Bebi ta taka ƙasa ta shiga jerin manyan mata, washe garima sega wata tawagar nan daga wajansu kawu tasi'u domin ilahirin zuri'arsu seda sukazo gaisuwa harda khalifa da ladi wanda seda ya saka aka kira mai bebi yayta mata godiya har yana ce mata ba daban Aliyu ba da sun shiga taskun rayuwa sabida bashin bankin da mahaifinshi yaci wanda hatta gidansu seda aka ɗaga aka siyar duk yana gidan yari bai saniba rayuwa taiwa mahaifiyarshi da kannenshi zafi cikin hukuncin Allah da taimakon Aliyu ya sai musu gida yay belinsa harya samu ya ɗaukeshi aiki har zuwa yanzu da komai yake warware musu,yanzu haka suna zaune gida ɗayane shida mahaifiyarshi da kannenshi da ladi matarsa inda shi kuma yake zuwa tokarawa aiki a karkashin kamfanin Aliyun. Haka nan su kawu tasi'u suka hau neman afuwarta tare dayi mata godiya akan hidimar mijinta garesu abin har kunya ya bata haka dai aka rabu cikin jin dadi da farin ciki. Har tsayin kwanaki bakwai ana faman karbar gaisuwa acikin gidan wanda ƴan uwan bebi sukai mata kara wajan zuwa kullum kuma da kular abinci abin mamaki kuma arana mutum kusan goma ke zuwa. Ranar da akai bakwai da yamma shahid shima yazo sabida suna exams bai sami damar zuwa ba sosai bebi tai mamakin yadda shahid ya zama magidanci yay wani irin girma da kyau, a falonta suka zauna suna hira duk farin ciki ya cika Bebi se wajan magariba ya tafi washe garima sega hassana hussaina ihsan da arfa anan suka wuni ihsan an zama ƴan mata se wani iyayi take wai ita likita zata karanta ita tai musu girki. Ran bebi wasai gata cikin ƴan uwanta nanfa hira ta kaure musu koda Aliyu ya dawo daga office shiya ɗaukesu ya kaisu gida ya haɗasu da shatara ta arzki. Adaren ranar Bebi taci adonta na bam mamaki daman ranar ita ce dashi soyayya mai tsayawa arai ta nuna masa tana mai kuka akan abinda yaywa danginta daga karshe tace. "Tabbas kacika masoyi na hakika Allah ya bani ikon faranta ranka" "Karki damu mai sona komai nai maki ban faɗiba" Yafaɗa yana haɗe jikinsu wuri guda aranar sunyi soyayya mai narkar da zuciya. Tsayin kwanaki ana amsar gaisuwar alhaji babba har zuwa sanda komi ya lafa rasuwar ta xama tarihi. Cikin wannan lokaci cikin bebi ya shiga wata na bakwai. Alokacin kuma Allah yaywa malam shima rasuwa sakamakon mura dayay fama da ita wannan karon seda Aliyu ya kai bebi gida. Anan gidan malam akaita amsar gaisuwa ammi tazo abba yazo da sauran ƴan uwanshi. Ranar bakwai da yamma bebi ta koma gidansu sosai tai mamakin yadda aka ƙere musu gidan nasu abin yay matukar burgeta adaren ranar Aliyu yazo suka wuce gida. Abin mamaki kaca kaca suka tarar da falon kamar anyi barin kayan falon wucewa ɗaki bebi tayi Aliyu kuma ya wuce ɗakin dija, tarar da komi yay a watse kanshi tsaye sauka yayi kasa ya wuce part ɗin ummnta anan ya tarar da ita a zaune tana kuka umman ta na bata baki. Tambayar mai yake damunta yaywa umma, amma ga mamakinsa se umma tahau tijara tana aibatashi sosai ransa ya ɓaci amman seya mike baice mata komiba ya wuce wajan abba anan yake masa bayani cewar ya dawo baiga khadija ba ya bita part ɗinsu ummanta tai masa rashin kirki. Abbane yasa aka kira abban bauchi tare da umman khadija da ammi koda sukazo abban bauchi ya tambayi khadija shin Aliyu yana mata wani abunne. Buɗar bakinta tace. Ba rashin ci bana sha ita dai haihuwa takeso. Kallonta abba yayi. "khadija aure da haihuwa da mutuwa lokacine na Allah sabida haka ki kwantar da hankalinki in Allah ya yarda kema zaki haihu" Amman ga mamakinsu se umman tace. "Kaga ya idriss nagaji ya sakarmin ƴata kawai ai wadda yake so yaywa ciki amman ita gata har yau ko ɓatan wata" Kunyace ta kama Aliyu ya sada kansa a ƙasa baice komiba. "Abba nidai ya sakeni kawai bana bukatar xamana dashi" "To kai Aliyu kanaji fa" Cikin kwantar da murya yace. "Khadija kiyi hakuri har yau aurenmu bai shekaraba kema zaki haihu insha Allahu" Duk yadda abba yaso su fuskanci komai amman sunki hakan yasa abban bauchi ya fusata. "wato ke khadija daman ba domin Allah kike son baba Ali ba? in bada wata manufa kike sonshiba tayaya zaki nuna ke haihuwa kike so in sonki domin Allah ne ai bazaki dage sekin haihuba wannan maganar banza ce kai baba ali saketa nace ai ba tare kukazo duniya ba Allah ya gani baka shiga hakkinta ba" Atake anan Aliyu yay mata saki ɗaya wai kuma seta saka kuka abban bauchi tsaki yay yabar wajan shima Aliyun tashi yay duk baiji dadi ba haka yabar falon. Koda ya koma bai gayawa bebi ba haka yasa aka gyara falon kamar da sukaci gaba da zamansu seda ta matsa masa da tambaya sannan ya zauna yay mata bayanin komi. Har ranta bataji dadi ba amman addu'ar alkairi taiwa dijan sannan ta cigaba da harkokinta. Soyayya mai kyau suke gudanarwa ita dashi lokacin da watan azumi yazo cikinta ya shiga wata na tara gashi zasu tafi umara shida ammi da usman harda mamanta, hakan yasa baba matar malam tazo suka zauna tare, tunda ya tafi kullum addu'arshi akan Allah ya raba bebi da cikin jikinta lafiya take. Ranar sallah suka dawo da asuba kuma aranar nakuda ta kama bebi wadda bata wani sha wuyaba Allah ya sauketa lafiya a part ɗin ammi. Ta haifo ɗanta namiji mai kama da Aliyu sak sedai farar fatar bebi daya ɗauko, zokuga farin ciki wajanshi kamar ze mayar da ɗan nan ciki gyarata akai kana aka wuce da ita part ɗinta anan baba tacigaba da kula da ita. Ranar suna yaro yaci suna Musa sunan babansu bebi sosai akai shagali a wannan rana kamar babu gobe. Washe garin sunan dija tazo ganin yaron harda ummanta cikin mutunci suka gaisa sun jima anan kafin sutafi. Haka baba tacigaba da kula da bebi da sahib,har tsayin kwanaki arba'in ranar kwana na arba'in da biyar bebi ta tafi gida bayan sun aje baba agidanta sun cika ta da kayan abin arziki. Kwanan bebi biyar a wajan mama ta zaga dangi taje gidan hassana husaina tana abuja taje gidan sadiya taje gidan iya ta zaga ko ina har gidan ladi taje anan ta wunima washe gari a gidan kakan ninta na ƴan kusa ta wuni gidansu kawu tasi'u kenan wanda aka gyara gidan yazama na zamani sabida yanzu haka duk samarin gidan suna aikine a kamfanin Aliyu sosai taga gata dangin mama ma na nan ɗin ta kai musu ziyara sabida daman su tun fil azal basu wulakanta suba kuma suma sun mata godiyar hidimar da mama ke musu domin duk abinda mama ta samu bata taɓa mantawa da danginta ba suma tana musu yadda ya kamata. Bata dawo gidaba se dare ita da ihsan duk sun gaji basu sami mama agida ba tana wajan kayanta dasuka zo sabida mama mai neman na kanta ce wannan dalilin yasa bata rabu da ƴan buga bugarta ba yanxu haka shinkafa ake kawo mata ƴar hausa take rabawa mata masu abinci da masu awo a wata su haɗa mata kudinta, sannan tana saida kayan yaji agidanta. Bayan mama ta dawo zagewa tai tasoma gyara bebi ciki da waje na tsayin kwanaki biyu hatta fatar bebi seda ta sauya, tunda yazo ɗaukarta yake ɗaukinta dan haka koda suka koma gida sahib wajan ammi aka barsa ya dauketa se master room. Sosai ya gigice ya susuce akanta ya shiga rudu wanda harda yi mata kyautar kujerar hajji a wannan rana sabida yajita xam zam kamar bata haihuba. BAYAN SHEKARU BIYAR. Abubuwa masu dadi da rashin daɗi sun faru. Rasuwar abban Aliyu data girgiza kowa rasuwar kawu tasi'u da kawu sani rasuwa baba matar malam.Waɗannan