← Book details Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 115

Sashe 62

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Aliyu tunda ya shiga ɗakinshi bai fitoba seda akai sallar azahar yay sallah sannan ya wuce part ɗin ammi anan ya sami nusaiba tana parking kaya yau zata koma abuja, sallama sukai ya wuce ɗakinshi na sama, wanda iya kayanshi kawai ya ɗauka amman yadda ɗakin yake haka yake ba,a sauya komaiba, Coffee ya haɗa tare da fitowa falonshi ya xauna yana kallo yana kurɓar abinshi.
Har xuwa sallar la'asar sannan ya sauko kasa lokacin ya sami ganin ammi suka gaisa da ita sannan ya wuce wajan abba suka gaisa suka wuce masallaci tare, atare sukai sallah suka fito, sannan shi ya wuce part É—inshi.
Lokacin daya shiga cikin falonshi na sama, ya tarar da daining table shaƙe da manyan fulasai har wata fulawa aka saka ta decoration.
A tsakiyarsu sannan ga wani sassanyan kamshi dake dukan hancinshi bude kofar room É—inshi yay ya shiga ya watsa ruwa duk yanajin kansa a takure sabida ya saba ayyukanshi a office wannan dalilin yasa hutun dayake yanzu bai masa daÉ—i, shirya kanshi yay cikin milk jallabiya mai dogon hannu, amman daga ciki ya saka black jeans, ya fesa turare ajikinshi ya taje sajenshi da gemunshi, sannan ya fito falo, wanda yay dai dai da lokacin da madam khadija ta fito daga nata É—akin.
Jikinta sanye cikin wani ƙaton wando tare da amrless wandon jane amrless ɗin kuma baƙa, seta ɗora wata irin hula akanta wadda ta bawa dogon gashinta damar ɗamewa dayake dija tana da gashi babu laifi.
Cikin É—anjin haushin daÉ—ewarshi kaÉ—an take masa barka da zuwa batare da É—aukiba.
Sannan ta nufi gaban daining tana faÉ—in.
"Gafa abincinka tun É—azu nake jiranka shuru wai yo ina katafi?".
Shareta yay kamar wata uwarshi tana tuhumarshi amman seya basar yana rabeta ya wuce saman seater ya zauna.
Cikin sanyin jiki ta buÉ—e fulas É—in ta É—ebo sakwarar data sha wuyar haÉ—ata wadda tai masifar murzuwa tai daÉ—i ta zubo guda É—aya tare da zuba miyar agushin datayi ta manja wadda taji bushashshen kifi, da ganda ta zuba masa gefen sakwarar, wadda miyar take É—aukar kamshin kayan haÉ—in dataji.
Lemon kwakwa wanda yaji madara da kwakwa ta zubo masa, a glass cup tare da É—auko plate É—in sakwarar ta nufo gabanshi dasu ta aje agabansa tare da komawa ta É—auko cokali mai yatsu ta saka aciki tare da kallonshi wanda yake rike da wayarshi yana latsawa.
"Na haÉ—a maka abincin".
"Nagode"
Yafaɗa yana saukowa daga saman kujerar ya zauna ya tanƙwashe ƙafafunshi ya janyo plate ɗin gabanshi.
Aranshi yana ayyana.
Baya son khadija ko kaÉ—an amman kyautatawarta gareshi yasa ya soma jin tausayinta acikin ranshi yanajin ze dinga bata farinciki kodan yadda itama take kokarin ganin ta kula dashi.
Bisimillah! yay tare da daukar cokalin ya soma kai abincin cikin bakinsa ya yaba da tsaftar khadija wannan dalilin yasa yaji bayada haufin cin dukkan abinda ta sarrafa sabida khadija irin mutanan nan ne masu tsabtar gaske Æ´ar gayuce ta gasken gaske.
Baƙaramin daɗi sakwarar tayi mashi ba haka nan ya cinyeta tass lokacin daya ɗauki lemon kwakwar yasha jiyay kamar ya sautu dan garɗi da daɗi amman dayake gogan boss ne yasa ya kanne.
Amman ya dubeta tare da ce mata.
"Nagode na yaba tabbas kin kware wajan iya girki nagode".
Wani farin ciki taji aranta wanda ya wanke laifinsa wanda take gani na daɗewar dayayi dakuma wanda yay mata na halin ko in kula tabbas kowa yana son yabo musamman macen data kyautatawa mijinta tofa tanajin dadi matuka gaya inya yabeta, rashin yabo kwa kan saka tsana da ƙosawa acikin kowani abu.
Lumshe idanunta tai ta budesu tarr akanshi tare da cewa.
"Hakika naji dadin yadda mijina ya yabi girkina tabbas na shaida kai mutum ne nagari mai adalci yadda baka sona baka kaunata, inda wanine da dawannan damar ze musgunamin azamantake war auranmu yakuma gasani, amman kai dayake kana da adalci bakaimin hakaba, duk da bana hango soyayyata a idanunka amman ina hango tsantsar adalci acikinsu nagodewa Allah daya azurtani da mijin ƙwarai ina rokonsa daya saka soyayyata azuciyarka yakuma sa dagani bazaka kuma kallon wata mace da sunan aure ba"!
Kallon kasan idanu yay mata tare da jan kanshi gefe yana mamakin zafin kishinta akanshi.
Kwashe kwanukan tayi daga wajan ta tsaftace gun sannan tai cikin É—akinta sabida tana tunanin baya da yawan son magana kota zauna wajanshi zata wahalane kawai amman baze tankata ba.
Tashi yay tsam ya bita cikin É—akin.
tana gaban madubi a tsaye tana kallon kanta
Ya shigo a bayanta ya tsaya ya dafa gadon bayan nata.
"Dija miyasa dana kusance a first night É—inmu naji zafi sannan kuma ragowar kinfini saninsu tunda ke mace ce?".
YafaÉ—a yana kallonta ta cikin madubin.
Idanunta ne ya ciko da ƙwalla.
"Idan na cigaba da kallonki ahaka zan iya cutar dake sabida bansan irin halittar bukatarki ba nikuma ga yanayin dana keji in ina having sex dake"
"Yaya badagani bane ba, wallahi amman insha Allah zanyi kokarin ganin na kauda matsalar"!.
"Dagani ne kenan?"
YafaÉ—a idanunshi cikin nata.
"A,a kaga baki É—ayanmu a wannan karon mukai yin farko to anty tace dole zamuji zafi kafin kuma muzama Æ´an gari".
"How muzam ƴan gari dija najifa ana faɗin irin runbun daɗin da ake shiga in ana having sex toni miyasa banjiba se tsabar azaba da zafi daya addaben ina rokonki akan kije ki nemi maganin sanyi sabida nayi serching akan abinda yake kawowa ma'aurata irin wannan matsalolin, niba azzalumin mutum bane bansan irin bukatarkiba dan haka bazan kalleki hakaba inƙi biya maki bukatunkiba sabida banason jefaki cikin wani hali, sabida haka xan miki transper na kuɗi masu yawa akan kinemi maganin matsalarki tunda ance na ku mata kunfimu sanin kan komai hakan yay maki?".
YafaÉ—a yana riko west dinta.
wani zullo tai tare da kwanto mishi tana yaba halinshi na ƙwarai dan in wanine bafa ze lura da wannan matsalolin nataba sema dai yay amfani dasu domin munana mata.
"Nagode da fahimta kuma zan nema ALLAH ya saka maka da aljanna amin".
Kiss ya manna mata a gadon bayanta sannan yabar dakin da sauri.
Tsalle tai ta faÉ—a saman gado tana É—aukar wayarta domin kiran yaya ruma.......................
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *PART* 2

NAKUÆŠINE

                              *70*
Chapter 62 · 0% Book details