← Book details Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 115

Sashe 107

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rana ɗaya kuma ta mai kaya inji bahaushe, zama yayi a bakin katifa tare da saka hannunshi guda ɗaya ya dafe saman kanshi gaba ɗaya tashin hankali yagama mamaye zuciyarshi arayuwa baya son ɓacin ran mahaifinshi ko kaɗan tabbas yasan a wannan karon sesun sami gagarumar matsala da abban nashi, sharce zufar data karyo mashi yayi tare da furta. "Innalillahi wa'inna'ilaihirrajun, ubangiji ka kawomin sassauci acin wannan cakuɗaɗɗan lamarin" yafaɗa tare da mikewa tsaye. Ya soma shirya kanshi cikin wani brown boyel mai yankan manyan sukari tare da ɗora hula a saman kanshi takalmi ya saka mai kalar kayan jikin nashi, turare ya fesa mai daɗin kamshi tare da ɗaukar wayarshi da makullin motarshi ya fita daga ɗakin. Bebi tana falo a zaune tana shan tea wanda ko sugar babu acikinshi sabida yadda bakinta yake babu ɗanɗano ko guda dan ko abincima a wannan lokacin se Ali yayi mata jan ido take turawa tana kuka! wanda baya minti ɗaya kuma seya dawo tass. Akanta ya tsaya tare da kallonta fuskarshi babu sukuni. "Tashi ki ɗauko hijabi zamu fita" Da kallo ta bishi tana nazarinshi amman ganin yadda ya haɗe girar sama data ƙasa babu alamun wargi yasa tai maza ta janye tea ɗin daga gabanta tana yatsine fuskarta daman tunda taga suna tare an kirashi a waya ya tashi yabar falon ya koma ɗaki tasha jinin jikinta abinda yasa bata bishi ba dan karyace tana masa bin diddigine. "Lafiya dai ko? naganka ba kamar ɗazuba?" Tafaɗa cikin kwantar da murya kamar yadda umman mufida ke gaya mata aduk sanda zakaiwa mijinka magana yazama ka tausasa lafazinka tare da kwantar da muryarka. Agogon dake ɗaure bisa tsintsiyar hannunshi ya kalla. "Kinga 1:00pm dan Allah kiyi sauri ina mota ina jiranki" Ya fita da saurinshi. Cikin mutuwar jiki ta mike zuwa bedroom wani coffee hijab ta ɗauka har ƙasa ta ɗora saman doguwar gown ɗin material ɗin dake jikinta tare da saka plate shoe ta fito cikin sauri tana tafiya kamar iska zata ɗebeta cikin tsanaki ta mika hannu ta bude marufin motar ta shiga wanda shi harya ma kunnata domin ita kaɗai kawai yake jira. Revars yayi kana ya nufi wajan gate ya fita daga gidan. Redion motar ya kunna batare daya mata magana ba, ta kula yau ƴan shariyar nashine suka motsa masa kokuma akwai abinda ke damunshi acikin zuciyarshi. Sosai yake falfala gudu a saman kwalta har ya sami zarafin barin arean unguwar ganin ya ɗauki hanyar da gidansu yake yasa komai nata ya tsaya cak. Har lokacin daya ƙarasa cikin unguwar tasu, abakin gate ya dakata tare da danna horn masu tsaron gate ɗin sukazo suka bude masa suna masa barka da zuwa. A harabar wajan adana motoci ya parker motar ya kashe tare da balle murfin ya fita. Haɓa ta riƙe tare da gyara zamanta batare datayi yunƙurin binshi ba, har ya kusan ɓacewa daga gurin ya juya yaga bata biyosa ba tsaki! yaja a fili tare da komowa kansa ya zira ta cikin glass ɗin motar. "Kifito mana ya kike ɓata min lokacina" Da sauri ya saka hannu ya buɗe murfin motar yana tsaye ta fito a wannan karon yaɗan sassauta saurin nasa suna jerawa tare sedai bai ce mata komaiba. part ɗin alhaji babba ya nufa dukkan ilahirin jikinshi yayi sanyi amman dayake shiɗin namijin duniyane babu ta yadda zakai ka gane halin dayake ciki sabida ko saman fuskarshima bata nuna hakanba. Kofar babban falon alhajin ya bude wadda daman anan ake tattauna dukkan wani important issues na cikin zuri'ar tasu. Zare idanunshi yay lokacin dayay katari da mutanan dake falon domin babu wanda bai sami zarafin halartar wannan wuriba hatta zee datake jego seda ta amsa kira, sedai su umar da basa gari. Sallama yayi kanshi sunkuye ya kutsa cikin falon wanda ƙannenshi suka sada kansu ƙas sauran iyayenshi kuma suka zuba masa idanu. Bebi na biye a bayansa wadda ilahirin jikinta yake rawa musamman yadda taga idanun kowa yayo kanta caaaa akai mata da ido ana kallonta. Abba wanda tun ɗazu ya kasa zama se faman kaiwa da komowa yake wayarshi ahannu cikin sauri ya juyo ga Aliyu dake kokarin gaisar da abban bauchi. Tas! tas!! tas!!! falon ya ɗauki sautin tagwayen maruka uku ciff da abba ya wankewa fuskar Aliyun dasu. Cikin wani irin yanayi bebi ta silale a jikin bango ta raɓe tana rintse idanunta sabida yadda taji marin kamar ita akaiwa. Itako khadija tun shigowar bebi takejin gabanta na wani irin bugawa sam bataji marin mijin nata ba gaba ɗaya hankalinta da idanunta yana kan bebi tai mugun zuba mata idanu ko kiftawa batai. Karuwarshi ko matarshi no karuwa dai domin tasan zuri'arsu basa AUREN BARE! rintse idanunta tai gam tana kiran sunayen Allah. Kafin maganar alhaji babba ta karaɗe wurin. "Kaimin dai-dai idiris daka mari shasha Aliyu muzaka zubarwa da ƙima muzaka tozarta muzaka kwancewa zani a kasuwa muzakaiwa abin kunya a cikin zuriya?" Yafaɗi hakan cikin cakuɗaɗɗiyar hausar data saka kowa cikin zulumi wanda tuni zuciyar wasu ta soma raya musu Aliyu karuwa ya aje agidansa. "Dakata Alhaji"! Ammi ta mike a matuƙar fusata wadda tunda abba ya aurota bata taɓa yin irin wannan maganar ga dukkan ahlin nashiba. "Ta yaya kake jefarmin ɗa da irin waɗannan munanan kalaman waɗanda suke kaman ceceniya da zaman dadiro..........., "Bilkisu koma ki zauna kada in kuma jin maganarki in ba hakaba ranki ze mugun ɓaci" Abba ya faɗa cikin zafin rai. "Wallahi idris bazan komaba ta yaya kai kana gani za,a lalata auren ɗanka sabida wata banzar al'adar daba addiniba sannan kai shuru to wallahi senai magana koda zakace yau ƙarshen igiyoyin aurenmu dakai ya ƙare Aliyu auren sunna, yayi da sanin ƴan uwanshi abubakar da usman su'suka wakilci aurensa kuma abubakar shiya miƙa sadakin auren nasa sun ɓoye mukune sabida banzar ɗabi'arku ta rashin AUREN BARE! Wadda nake addu'a Allah ya rusa wannan al'adar kowa ya sami ƴancin kanshi". "Dakata bilkisu! Alhaji babba ya faɗa tare da mikewa. Shiko abba ƙasa yay da kanshi yasan ran ammi ya ɓaci tunda tace abbakar kai tsaye tace idriss kai tsaye wanda bata taɓa faɗin sunanshi ba tunda ta haifeshi sabida alkunya ta ɗan fari hakanan bata taɓa faɗin sunan shi abban ba sabida alkunya itama abba take faɗa mai kamar yaranshi ammi macece mai kawaici da hakuri yadda yaji yau ta mike tana wassafa magana yasan ranta ne ya ɓaci. "AUREN BARE Baya cikin tsarinmu dana iyayenmu sabida kina ganin kin isa kin kai kin kawo shine zaki dubi idanuna ki gayamin wadda duk ta fito abakinki ko? madallah to nagode amman ki sani wannan aure dashi da babu duk ɗayane a wajanmu sabida haka a yanzu base anjima ba kai tsageri marar mutunci inason ka saki waccan yarinyar ka bata takardarta ga matarka nan hadiza ƴar uwarka ta jini da ita muke son ka zauna ba BARE ba! domin bazamu lamun AUREN BARE a mai atamfa family ba" Alhaji babba ya kare maganar yana mikawa Aliyu takarda da biro, Bebi kafe tsohon tayi da idanu tana kallonshi maganarshi ta ƙarshe tafi kalmar sakinta dayace zafi acikin zuciyarta. Lallai namiji munafuki ne au ashe daman yana da mata yake wannan rawar jikin akanta jar bura'uba! lallai ya gama da ita ƙarewa ma matar tashi ƴar uwarsa ce lallai ya cuceta!!! Falon ne yay tsit illah sautin kukan dija dake tashi sannu a hankali tanajin duniyar tana juya mata Aliyu yayi aure? da wadda take hango tsantsar sonta a gareshi wayyo taga takanta itakam. Haka zalika umman khadija datai zaman dirshan tana share zufa. "Amsa nace" Alhaji babba ya dakawa Aliyu tsawa wanda ko motsi ya kasayi illah kansa daya sunkuyar kuma har yanzu yana duƙe ne agaban abban bauchi wanda tun fara maganar baice komai ba, usman kwa ji yake kamar yaje ya naushi Alhaji haka zalika ya abbakar hankalinshi yay matukar tashi,gaba ɗaya falon tsitt ya ɗauka. Ɗago da jajayen idanunshi yayi waɗanda suka kuma girma jijiyar kanshi ta mike tai wani irin ruɗu-ruɗu zubawa alhaji babba idanu yayi batare dayay shakkarshi ba yace. "Alhaji kayi hakuri wallahi bazan saketa ba sabida inason matata! kuma ai AUREN BARE ba haram bane bafa zan saketa ba wallahi kozaka mutu haka nan addini ya haramta sakin mace mai juna biyu akan me zan saki matata da cikin sati biyu ajikinta?" Yafaɗa yana mai miƙewa tsaye yana jefawa alhajin wani irin kallon raini. Gaba ɗaya falon hayaniya ya ɗauka kowa yana na'am da maganar Alin domin daman yawanci mazan biyayya suke bawai son wannan auren haɗin suke ba. Gyaran murya abban bauchi yay wanda daman shi baice komai ba tun farkon maganar. "Zauna babana, ya dubi Aliyu a tsanake. Zama yayi cikin na'am da maganar abban bauchin sabida mutum ne shi mai feɗe gaskiya wannan dalilin ne yasa ma suke yawan samun matsala da alhajin. "Haba yaya ta yaya zaka ringa tilaswa yara Auren da basuyi niyya ba wannan fa abun ba addini bane ba yanzu hakan ku bai ishemu ishara ba? yanzu inda karuwa ya ajefa dafa haka za,a kawo mana ɗan shege mu goya amman ku duba auren nan nasa abubakar da usman su suka goya masa baya yayi akanme zakace ya saki matarsa ita khadijan da kuka liƙa masa ai ya amsa yay muku biyayya ku ba seku goya mai baya a binda yake soba kuduba isharar Allah auren da kwana goma sha biyar har Allah ya basu rabo toni dai babu ruwana sabida haka inma zaku aje wannan makaman yakin naku seku aje, kai babana tashi kaja matanka Allah ya baka ikon yin adalci sannan daga yanzuma duk mai son AUREN BARE yaje yayi matukar zeyi adalci Allah ya bashi tagari amin" Abban bauchi ya faɗa yan mai tashi yabar wajan daman shi abinda alhajin yake yafa isheshi yana musu wata isa da gadara kamar shine ubansu ai wa ba uba bane. Falon ne ya dauki hayaniya nan da nan kowa ya soma tofa ta bakinshi mazan familyn kwa ihu suke suna cewa. "Well done yaya Aliyu Allah ya biyaka ka kwato mana ƴanci" haka suketa faɗa wanda hatta ƴammatan ma ba,a barsu abaya ba domin yawanci da samarinsu amman tsoro yake hanasu kawosu gaban iyayen nasu. Gyaran murya alhaji babba yayi. "Tabbas maganar Abban bauchi ta sanyaya mun jikina
Chapter 107 · 0% Book details