← Book details Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 115

Sashe 68

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Ƙarar! Buɗe ƙofarshi ita ta dawo da bebi daga duniyar tunanin data faɗa cike da fargaba ta juya tana kallon saitinshi ta cikin glass ɗin motar taga yadda yake faman sauri kamar wanda kashi ya matseshi kunsan yadda mutum yakeji idan kashi ya matseshi duk izzarsa duk yanganrshi matukar kashi ya kamashi tofa seya saka gudu ko sauri tunanin hakan yasa Bebi tai masa uziri tare da mayar da kanta kasa batare dataji fitar usman ba.
Har sanda usman ya dawo bata sani ba seda taji alamun ya bude ɓarin ta sannan ta ɗago a tsorace tare da zuba masa manyan dara daran idanunta waɗanda in suna halin tsoro suke ƙara firfitowa.
"Ƙanwata taso mu shiga ciki".
YafaÉ—a tare da É—an matsawa baya domin ya bata guri ta fito.
Tattare hijab É—inta tayi tana ayyana karamcin usman, sannan ta fito waje tana kallon harabar gidan wanda tsoronta ya kuma ninkuwa, inba idanunta ne yay mata karyaba tasan dare yayi domin kusan goman dare amman yaya akai wannan gidan shi yake kamar da rana sabida hasken manyan fitilu, jibi harabar gida kamar girman anguwarsu.
Bai tsaya É—auko mata kayanta daya aje a boot ba sabida daren dayayi, Cikin nutsuwa ya dubeta.
'Zamuje wajan matata ki kwana kafin gobe mijinki ya É—aukeki, dafatan babu wata damuwa?".
Ya kalleta.
Girgiza kanta tayi alamun babu, tana satar kallon tsarin gidan yadda motoci ke zube a harabar gidan kamar ba gobe lallai waÉ—annan sunfi karfin ta.
"To ƙanwata muje ciki ko?"
Yafaɗa yana wucewa gaba cikin nutsuwa tabi bayanshi har tana haɗawa da tuntube bata taɓa ganin girman gida da kyau da tsari kamar wannan ba( niko nace bebi bakiga komai ba, gidan Alhaji mai atamfa ai ba baya ba wai danma a iya harabar gidan kikene kike faɗar haka )Gaban gate ɗinshi na part ɗinshi ya dakata yana buɗewa seda ya tura gate ɗin sannan ya juyo ya dubeta.
"Bisimillah mu shiga ko".
YafaÉ—a yana shiga ciki itama tabi bayansa.
Tundaga farkon part ɗin usman tasoma ganin wasu irin fulawowi masu fisgar hankali tare da wasu irin fitilu masu haske gaban wata irin ƙofa mai kyau ya tsaya tare da danna wani abu nan da nan kofar ta bude ya danna kanshi ciki, itama tabi bayansa.
Suman tsaye tai sabida jinta cikin wata irin ni'ima sassanya mai kamshi ƙafafunta ta nutsa cikin, lallausan carfet ɗin falon tana kallon tsarin yadda aka haɗe falon da wasu irin zafafa kujeru ga wata katuwar tv tana aikinta, faɗin tsarin haɗuwar falon ɓata bakine amman dai an tsarashi cikin ilimi tare da wayewa da kyau.
"Muje mana".
Taji muryarshi firgigit! ta É—ago tana kallonshi, sannan ta bi bayanshi cikin falon suka shiga yace mata ta zauna yana zuwa minti biyu.
Wata kwana taga ya nufa tare da buÉ—e kofa ya shige ciki.
Lokacin ta mayar da ajiyar zuciya tacigaba da bawa idanunta hakkinsu oh lallai gobe insu hassana sukazo akwai labari dama da irin waÉ—annan gidajen aduniya itafa inba a tvn gidan iyaba bata ganin irin waÉ—annan falukan, tsuru taiwa Tv duk tsoro ya cikata gani take kamar mutanan ciki zasu faso su watso waje sabida tsabar girmansu.
Shiko usman bedroom ɗin Zee ya shiga harta soma barci ya tasota tare da ce mata ta fito falo akwai baƙuwar Aliyu amman gobe zata koma wajan ammi yauma dai dan dare yayine.
Da har zata fara mita amman jin ya ambaci Ali yasa tasan abin bana wasa bane ba,setai zaton ko abokiyar cinikinshi ce tai dare shine ya haÉ—ota da usman tunda tasan shi ba son jama'a yacika ba.
Ajiyar zuciya ta mayar tare da saukowa daga saman gadon ta É—auko hijab tabi bayanshi.
"Amman shi mai yasa baze kaita part É—inshi ba senamu?".
TafaÉ—a tana kallon mijin nata.
"Kinga bana son wannan maganar nida Aliyu duka É—ayane in kuma bazaki bata É—akin ba semugani".
"Ni bance ba muje kaga karka ɗagan murya da tsohon daren nan kaje ka gaya masa ya ƙara girman harara fiye da tada da".
ƙunshe dariya usman yay sanin zee daman ba shiri suka cikayi da Aliyu ba duk da kasancewarta ƴar ƙanin ammi uwa ɗaya uba ɗaya, amma sam basa shiri domin Ali yace zee ta cika tsiwa da yawa.
Har suka ƙarasa falon bebi tana ta kallon ta sabida daman ita batada baƙunta.
Sallama zee tayi cikin nutsuwa tana dafe tirtsetsen cikinta daya tsufa.
Cikin sauri Bebi ta ɗago tana ƙarewa matar gabanta kallo wadda batafi sa'arsu hassana ba, sedai tafi ƴan biyu jiki da kalar hutu, farace tarr kuma babu laifi tanada kyanta.
Amsa mata sallamar tayi itama tana zamowa daga saman kujerar tare da cewa.
"Ina yini?".
Cikin sakin fuska zee ta É—an sunkuyo ta riko hannun Bebi.
"Lafiya kalau kanwata zona nuna maki bedroom É—in dazaki kwanta dare yayi".
TafaÉ—a mata cikin kulawa.
"To seda safe Aliyu ze shigo gobe insha ALLAH".
Usman ya faÉ—a mata yana juyawa ya bar wajan.
Amsa masa tai da "To"
Sannan tabi zeee wadda hannunta ke rike dana bebin.
Wata kwanar suka nufa, gaban wata kofar ɗaki zee ta tsaya ta bude sannan suka shiga cikinshi babu laifi yana da kyan tsari, da gado da madubi, da kuma wata kofa sakin hannunta zee tayi tana yabon kyan bebi tare da kallon ƙanƙantar yarinyar.
"Ga É—akinan ga gado da toilet bara na kawo maki abinci".
"A,a na ƙoshi nagode".
TafaÉ—a muryarta na rawa.
Juyowa zeee tayi tare dayin jimm alamun bataji daÉ—i ba amman setace.
"To babu matsala ai da safe kina nan kyaci seda safe"
"Nagode".
TafaÉ—a tana zama gefen gadon har zee ta fice daga cikin É—akin..............
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *PART* 2

NAKUÆŠINE

*75*
Chapter 68 · 0% Book details