← Book details Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 115

Sashe 80

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Baya tayi ta kwanta a gefen carpet ɗin ɗakin tana mayar da azababbiyar ajiyar zuciya mai tsananin ƙarfi hawayen idanunta ne yaƙara gudu, tunda take bata taɓa jin yanayi kamar wannanba, bata taɓa jin abu makamancin wanda yay mata a yanzun ba, tome hakan yake nufi? zafin da ƙwaƙwalwarta tayi yahanata lissafa yanayin datake jiki.
Face tsintar kanta datayi cikin wata irin nutsuwa tare da sanyin jiki, a matuƙar wahale ta miƙe gaban madubin ɗakin taje ta tsaya ta yagi tissue'n data gani a gefen madubin kusa da kayan kwalliya, ta goge hawayen daya ɓata mata fuskarta, sannan ta ɗauki mai ta shafa gaban gadon ta koma tare da ɗaga kayan da ammin tace ta aje mata, doguwar rigar after dress ce sedai ita gabanta a rufe ike sannan kuma tana da kauri jikinta tamkar karen muski, jace mai adon duwatsu masu ruwan gwal, agabansu, se mayafinta madai-daici shima ja, se kayan undies waɗanda suke acikin ledarsu daga gani sabbine.
Sakasu tai ajikinta kamar angwada da ita, cif da cif kayan sukai mata warware doguwar rigar tai ta saka acikin jikinta.
Gaban madubi ta ƙarasa tare da mayafin a hannunta.
"Masha Allah tabarakallah amman nayi kyau".
Tafaɗa tana kallon kanta wato rigar tai mata mugun kyau ba ɗan kaɗan ba, daga sama tai wani irin tattara ta kame kirjin nata tai ɗam, daga ƙasa kuma taɗan saki tawajan cikinta sedai daga baya ta kame hips ɗinta tai ɗam-ɗam domin hatta shatin pant ɗinta seda ya bayyana.
Mayafin ta É—auka ta yafa a saman kanta tare da É—aukar turare ta fesa amman É—an kaÉ—an.
Kana taja kafafunta ta nufi kofar fita hannunta É—aya yana kan cikinta sabida tun É—azu da tasha wannan zumar takejin cikinta yana É—an kartawa kaÉ—an kaÉ—an kamar ciwon mara nason kamata, sekuma jikinta datake jin abu naÉ—an zubo mata kaÉ—an daga ciki.
Kama handle É—in kofar tayi ta buÉ—e ta fita zuwa falon.
Yana daga xaune daga kujerar datai saitin Tv ammi kuma tana daga wadda take kallon kofar É—akin data fito É—in.
Ya zubawa Tv idanu amman a cikin zuciyarsa ba Tv ɗin bace wani tunanin yake daban, musamman a ɗazun daya fito a matuƙar wahale sabida yadda sirrinshi ke ƙoƙarin tona asirinshi inda Allah ma ya rufa masa asiri ammi bata falon lokacin tana can wai kicin tana haɗawa abba break, wannan damar ta kaɗaicin daya samu ita ta ƙara bashi damar zubewa gaban ɗan frij ɗin dake falon hannunshi na rawa ya buɗesa ya ɗauki gorar faro mai sanyi ya kafa a bakinshi yana sha yana ɗan danna ƙasan mararshi da tafin hannunshi har yaɗan sami nutsuwa sannan ya dai daita kansa ya koma saman kujera ya zauna to ahakan ammi tazo ta sameshi koda ta tambayeshi ina Bilkisun seya ɗan shafa kansa kaɗan irin na halin ko in kula ɗinnan sannan yace.
"Inaga kotana ƙarasa shirin ne"
YafaÉ—i hakan batare da sakin fuska ba domin bai son ta gano halin dayake ciki shiyasa ya rufe idanunshi kamar mai bacci tare da fuskantar Tv, wanda a hakan Bebi ta shigo falon ta samesu.
"Kai masha Allahu autata kinyi kyau masha Allah kamar a sureki a gudu a,a wallahi na É—auka kayan nan bazasu maki ba sabida ana hussaina na É—aukar maki ashe dai autar tawa tana da girma kai masha Allah".
Tacan ƙasan idanunshi yake ɗan satar kallonta kaɗan aranshi yana ayyana ai ammi ma ke a iya riga kikaga girman nata, amman a fili seyay kamar bai san ta fito daga ɗakin ba.
Raɓewa tayi daga gefen kujera tana sunƙe kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta
"Maza zona miki hoto autata kinyi kyau zan turawa su nusaiba su ga matar Baba Ali kafin suzo zo"
Ammi ta faɗa tana fito dawata azababbiyar waya mai shegen kyau wadda kyanta ya bayyana tsadar kuɗinta ƙarara.
Takowa take zuwa gaban Ammi wadda duk taku ɗaya se kirjinta da hips ɗinta sun kaɗa kamar da gayya, Yana ankare da hakan tsaf, kuma duk takun dazatai ɗin yana dai dai da takun sautin bugun zuciyarsa ne, cikin jarumta ya miƙe batare daya saki fuskarshi ba.
Gabanta yaje ya tsaya wanda yay mata shamaki da isa gaban ammi
"Ke jeki É—auko hijabinki wanda kika cire wani wawan ne ze fita dake da wannan shigar".
Yafaɗa tare dayin kicin-kicin da fuska wadda tasa cikin sauri Bebi ta juya hartana haɗawa da tuntuɓe tayi ɗakin ammin.
Lashe gefen bakinshi yay kamar wani maye tare da bin bayanta da wani munafukin kallon ƙulla yana mai tura hannayenshi cikin aljihun wandonshi ya fito da waya yana dubawa a basance gudun kada ammi ta gano halin daya faɗa.
Harta fito bai bar wajan ba yana kallon yadda ta sinƙe cikin hijabin ɗazun wanda hakan yaji yafiye masa sau dubu.
Juyowa yay gaban ammi yaÉ—an rissuna gabanta.
"Ammi zamu wuce in abba ya fito kice masa na tafi TOKARAWA".
Bebi ma tsugunnawa tayi gaban ammi kamar yadda yay tana mai sada kanta a ƙasa.
"Allah yay muku albarka Allah yasa albarka a zamanku Allah ya tsareku yabaku ikon faranta ma juna, inka samu shigowa zan baka kaya ka tafi mata dasu tunda kaga bamuyi lefe ba, kafin muga zuwa lokacin bikin amina sena haÉ—a da kayan lefenta a ordern nusaiba".
TafaÉ—a tana janyo wata Æ´ar jaka a gefenta rafar kuÉ—ine Æ´an dubu dubu kimani guda uku.
Ta miƙawa Bebi cikin hannunta.
"Niga tawa Æ´ar gudun mawar babu yawa ki sayi koda katin wayane".
Hannun Bebi yayi kaɗan da riƙe irin waɗannan manyan kuɗaɗan dan haka se hannun ya soma rawa.
Cikin azama ya kwashe kuÉ—in a hannunshi tare da kallon ammi
"Nagode ammi Allah ya ƙara buɗi"
yafaÉ—a yana mai tashi tare da kuÉ—in a hannunshi.
Itama Bebin godiya taiwa ammi kana ta miƙe harya fita daga falon da sauri tabi bayansa tana juyawa tana kallon ammi mace mai dattako tare da sanin darajar ɗan adam kenan.
Har ta fita zuwa harabar gidan tare da nufar inda taga ya miƙa...........................

*ÆŠAN MAJALISSA*
*H A S K E*
*RABON WANI*
KOBA SO*
*DA IZZATA*

_Kowannensu akan farashin 300 waÉ—anda suke documents complt, gabaki É—ayansu kuma naira 1000, maiso seya nemi,08142105218, haka nan mai son wannan littafin shima dai seya nemi wannan numbern ta sama domin ya saya_
11/14/21, 3:13 PM - Allah Akbar: *85*

*Assalamu Alaikum ina miƙo saƙon ban haƙuri zuwa ga ɗunbin masoyana masu bibiyar wannan littafin na yadda kuka jini kwana biyu shuru abinne ya haɗemin mun ɗan shiga hidima ne amman yanzu alhamdulillahi na kammala komai sabida haka zamu ɗora daga inda muka tsaya waɗanda suka kirani domin suji lafiya da waɗanda sukai min magana ta watsapp inbox duka nagani kuma nagode da yadda kukai min uziri Allah ya saka muku da ɗunbin alkairinsa amin summa amin nagode*
Chapter 80 · 0% Book details