← Book details Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 115

Sashe 18

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Cikin nutsuwa suka gama fitar da manyan kulolin, da taimakon drivern daya kaisu suka shigar da kayan abincin cikin kamfanin, baban nazir ne ya kai musu har kan teburin da suke zama, sabida yadda yake jin tausayin yaran, kuɗin motar hassana ta bawa drivern tare dayi mishi godiya sannan itama ta ƙarasa inda zasu zauna, bayan sun gaisa da baban nazir ya wuce office sabida yana sauri zasuyi meating.
Yau kamfanin babu yawan shige da ficen mutane kodan sabida safiyace tsuru sukai akan bencin dasuke zaune duk jikinsu yayi sanyi suna tunanin kada Allah yasa dai abarsu da kwantai yau.
Shigowar wata farar mota cikin wajan shine yajawo hankalinsu hussaina, cikin nutsuwa motar ke tafiya harta karasa wajan da ake adana sauran motocin kamfanin, tsirawa motar idanu sukai sabida tsabar yadda ta haɗu, sun jima basuga fitowar na cikintaba, dan har hassana ta mike tana zubawa wani security dambu tana komawa zata zauna, sukaga wani magidancin namiji kamilalle cikin shigar manyan kaya farine tass goshinsa dauke da tabon abin sallah, wayace kare a saman kunnenshi dan da ƙafama ya tura marufin motar yana tafe yana cillah key ɗin hannunshi yana dariya yana magana a wayar.
Da sauri sukai ƙasa da kansu ganin yana kusanto inda suke.
Cak ya tsaya agaban kulolin dake gabansu yana cigaba da wayar, cikin harshen turanci..
Yakai kusan mintuna goma a wajan yana wayar kafin ya kammalata yana mayar da ita cikin aljihun wandonshi.
Ƙarasowar baban nazir yasa suka ɗan sauke ajiyar zuciya domin su da sunɗan firgita da yadda sukaga wannan mutumin yana kallonsu.
Cike da far'a baban nazir ya É—an rissuna gaban wannan mutumin yana gaisar dashi cikin ladabi.
"Oga Usman barka da safiya, wallahi yanzu su manager suketa tambayar ko lafiya baka shigoba duk an hallarafa kai kawai ake jira". yafaɗa yana sadda kanshi a ƙasa.
Cikin sakin fuska wanda aka kira da oga usman ya dubi babansu nazir kana yace.
"A,a fa ni ai ba wancan bane inada iyali dole se nagama sharafin gabana, watakan kun saba aiki da wancan mai fuskar zakunan shiyasa kuka saba dako sammako kamarshi toni fa wannan satin dole se kamfanin nan ma yasan dawa Allah ya haÉ—ashi" yafaÉ—a cikin barkwanci yana dariya.
Shima baban nazir dariyar yayi sabida kowa yasan halin Usman mutum ne mai tsananin barkwanci shiyasa yakeda da jama'a sosai awajan shifa kowama janshi yakeyi.
Hankalinshi ya mayar kansu ƴan biyu waɗanda tun fara maganar sukai ƙasa da kansu suna dai sauraran wannan dramar da ake agabansu.
"A,a kai kace kwana biyu Allah ya hutashshe da madam É—ita masu abinci muka samu ashe?,kasan jiya friday banzoba shiyasa ban gansuba" yafaÉ—a cike da kulawa.
Dariya baban nazir yayi kana yace"ƙwarai kuwa wallahi ƴaƴan yayan matata ne da Allah ya masa rasuwa nine ma na kawosu nan ɗin kasan rayuwar seka mike ƙafa yanzu".
Cikin tausayi usman kebin Æ´an biyu da kallo yara kyawawa tubarkallah dasu amai makon a basu ilimi mai kyau shine za,a dinga É—ora musu talla damma yaga yaran sunada nutsuwa sosai.
Muryarsu ce ta katse shi suna faman gaisar dashi cikin nutsuwa, shima cike da sakin fuska yake amsa musu idanunshi akansu yana jin tausayinsu har cikin ranshi domin yaran abin a tausayawa ne.
Cikin mintuna uku yagama nazarin su daga gani za,a sami cikakkar tarbiya wajansu duba da yadda suke a kame babu baragada daga gani mahaifiyarsu ta tsaya akansu sosai wajan basu tarbiya.
"Toni ai kun sakani a duhu dan babu yadda zanyi na shaida wace hassanar wace kuma hussainar?" yafaÉ—a yana murmushi kaÉ—an.
Cikin nutsuwa hassana tace.
"Nice hassana wannan kuma hussaina" tafaÉ—a tana yin kasa da kanta.
"Masha Allah koke fa kunga yanzu idan naganku zan iya shaidaku to bara mu shiga ciki kunji Allah ya baku sa,a dafatan zaku ɗan sammun ladan ganin ido" yafaɗa yana dariya dukansu dariyar sukai tare da furta "Mai ze hana". zaro idonshi yayi waje"A,a kuce ƙannan nawa masu kirkine a,a ni bazan karya ba sedai na ɗora kada umma ta dakemu".yafaɗa yana murmushi.
Shikam baban nazir tsananin mamakin yadda usman ya sake da yaran yakeyi duk da yakasance mutum mai barkwanci amman dai kam bai taɓa sakewa da kowa kamar hakan ba.
Wayarshi dake aljihunshi ita ta katse masu dariyar dasuke yi.
"Ya salam gafa alhajin faÉ—a nan yana kira" yafaÉ—a har yana wani rike baki kamar wani yaro karami.
Aikuwa tunda ya É—auki wayar suke jiyo sautin wata dakakkar murya wadda sautin fitarta har waje amman yanayin maganar da yadda ake sauri wajan fadinta baya barin na waje yaji taka mai man akan abinda ake faÉ—an sedai kuma kana dai ji kasan faÉ—a akewa wanda ya dauki wayar.
"Yau inaganin tujara yanzu kai dan ubanka ni yayanka kakewa wannan masifar! to ai seka dako sammakon dare kazo kanon agogo sarkin aiki ai kaine namiji mu duka matane" yafaÉ—a yana dariya tare da katse wayar.
Baban nazir ya duba.
"Kaga zo muwuce ciki tun kafin wancan mai bakar zuciyar ya zagen, wai kaji faÉ—a yake akan wai baki zasu zo tun É—azu ake zaman jirana nai sing naki fita office wai aikin minake agidana, kajifa ni mai iyali har ze gayawa haka?" yafaÉ—a yana dariya.
"Ai kasan halin yallaɓai shi baya son sanya wallahi mu kammu mu ringa mun saba da horanshi" cewar baban nazir yana kallon usman.
Gaba usman yay yana cewa su hassana anjima ze aiko masinjanshi ya sai mashi dambu kana ya kama hanyar shi yay gaba sabida sanin halin tujarar Ali kada yaje ya haÉ—a masa bom wajan abba.
11/14/21, 3:06 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
{ _HOT LOVE_ }

NA
*AUTAR MANYA*

*Siyan nagari mayar da kuɗi gida ga arha ga ƙarko kudai maza ku garzaya ku nemi taku Suna sayar da MTN data akan price Mai sauki 1gb 300 2gb 600 expire 30 days ga masu bukata suna iya tuntuɓarsu akan wannan number din 08066268951*

_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._

*21&22*

Hassana ce ta juyo wajan hussaina tare da ce mata"Hmm wannan bawan Allah baya da matsala jiba kamar ba mai kuɗiba yadda ko ƙyamatarmu bai ba".tafaɗa tana ɗan kaɗa idanunta kaɗan,"To ai daman wasu mutanan zakiga Allah ya zuba musu sauƙin kai tamkar bamasu kuɗiba aidaman ba duka aka taru aka zama ɗaya zakiga ai ko a talakawan akwai masu izza to kuma suma haka masu dashi ɗin akwai masu izza da ƙi faɗi", hussaina tafaɗa tare da mikewa sabida zuwan wani ma'aikaci zesai dambu bayan ta zuba mashi ta dawo ta zauna tana cigaba da hirarta da ƴar uwarta, cikin ikon Allah ahaka akaita zuwa wajan siya wasu sukan zuba musune a packet wasu kuma anan zasu zauna saman bancinan wajan suci su ƙara gaba abunsu.
_CIKIN BABBAN ÆŠAKIN TARO NA MUSAMMAN DAKE CIKIN KAMFANIN MAI ATAMFA_
Sosai suka zauna tare da manyan cikin kamfanin suka tattauna akan abubuwan cigaban da kamfanin nasu ya samu duk da kasancewar kamfanin sabone amman kuma ikon Allah haryaso yafi na *mundaɗu* samun jama'a sosai kuma duk ba kowane yay silar haɓɓaka wannan kamfaninba kamar *Aliyu Idiriss Mai atamfa* wanda shi kanshi usman ɗin ya jinjinawa ɗan uwan nashi yakuma san dukkan wata nasara da kamfaninsu na nan dama sauran suke samu tofa tare da taimakon ɗan uwan nashine saninsa mutum mai ɗan banzan naci tare da mayar dakai akan dukkan abinda yasaka agabanshi tofa da zarar ya kafe babu zancen bari, duk da kasancewarshi mutum mai wuyar sha'ani amman hakan bai saka ya samu miskila wajan iya hulɗa da mutane ba wanda hakan ya kuma jawo mashi ƙara samun tarin mutane yadda ba,a zato sosai mahaifinsu yake alfahari da Aliyu sabida yadda yake bashi gudunmawa fiye da sauran ƴan uwanshi.
Sun kammala taron su cikin awowi biyu kacal wanda aka tashi cikin farin ciki gami da fahimtar juna, anan usman ya ƙaddamar da abinda ze ƙaddamar kafin kuma mai gayya mai aiki director manager ya dawo, sosai.
Chapter 18 · 0% Book details