← Book details Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 115

Sashe 64

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Ni zaka mayar mahaukaci,ina maka magana kaimin banza sabida ka É—aukeni ban san minakeyi bako?".
Aliyu ya dubi usman wanda hankalinshi ke kan driving yake gaya mishi hakan.
"To yaya kakeson nace maka? cewafa kayi na taka ƙulli yau kuwa zakaga na taka ƙulli ganin idanunka".
Usman ya faɗa yana dariya,Tsaki yaɗanja kaɗan tare da fiddo da wayarshi yana neman layin Alhaji aminu abokin business ɗinshi, ringing ɗaya Alhaji aminun ya ɗauki wayar Gaisawa sukai ya soma yi mashi bayani akan harkokinsu wanda har suka ƙarasa unguwar su Bebi bai daina wayarba har seda usman ya shiga cikin layin sannan ya kashe motar ya zubawa Aliyun idanu tare da jiran ya gama wayar su shiga cikin gidan.
Sun kai kimanin mintuna goma acikin motar usman yana faman jiranshi agogon dake hannunshi ya kalla tara saura na dare.
Alokacin shikuma ya kammala wayar yana ajeta cikin aljihun wondonshi sannan ya dubi usman É—in.
"Kaje ka fito ina nan ni kasan babu inda zan bika".
HaÉ—e hannaye usman yayi kamar ze zuba ihu sannan ya dubi Aliyun.
"Haba angon dija kaiwa girman Allah kazo muje kaga inna ga idanunka bazan zauna kamar rannan ba musamman in kana zabgomin harara da idanunka".
Shi dariyama usman ɗin ya bashi amman dayake wanda ya rigaka kwana tofa seya rigaka wayo seda usman yasan yadda yayi ya ribace shi ya fito yana mita suka ƙarasa ƙofar gidan agarin saurima seda Aliyu ya ƙume da ƙofar gidan, yana ayyana insha Allah ze taimaka masu a gyara musu gidan dan ƙofar kaɗai ma se taima mutum illah.
Daga bakin ƙofa usman yaɗan dakata tare da ɗaga murya kaɗan yay sallama.
Mama dake sauraran malam wanda ke mata bayani akan mahaifinsu Aliyu, ita tai saurin amsa sallamar kuma atake anan taji sanyi ya ratsa mata zuciyarta sabida tun É—azu acikin zuciyarta zulumin yadda mijin Bebi yay biris da zuwan take.
Cikin sauri ta É—auko babbar tabarma ta baje a tsakar gidan akusa da malam sannan ta gyara mayafinta wanda ya kuma haskata sannan ya fito mata da ainihin kyawunta na hausa fulanin Usul.
Usman ke gaba Aliyu na bayanshi, Cikin nutsuwa suka ƙarasa cikin gidan zama sukai akan tabarma da mama ta shinfiɗa musu.
Cikin lkunya usman ya gaisar da malam tare da mama, Shiko Aliyu ko ajikinshi cikin sakin jiki ya gaisar dasu duka biyun yana duban malam.
"Niko baba kamar naso gane fuskar nan wallahi?"
Cewar Aliyu yana É—an nazarin inda yasan malam lado.
Shima malam se a sannan ya dubi Aliyu da kyau sannan yace.
"Lah kar dai wannan yaron ne wanda kataɓa kawoni gida kwanakin baya bani da lafiya ina titi ka ganni a zaune ka tsaya ka ɗaukoni harka bani kuɗi aiko na ganeka ɗan kirki".
Murmushi Aliyu yay.
"Allah sarki baba nine naso sake komowa na ganka kuma senai tafiya Allah bai nufa ba se yau".
YafaÉ—a yana kallon malam.
"Masha Allah hakan ma nagode sosai in wanine ma ai baze kalleka ba".
Sannan ya juya yana kallon mama wadda kanta ke sunkuye.
"Wato Aishatu na jima banga yaron arziƙi mai tausayi irin wannan bawan ALLAH ba, kwanakin baya naje kasuwa wajan wani abokinmu, zan masa ta,aziya wallahi bayan na dawo se ciwon kai da kumallo ya kamani a hanya sena zauna bakin wata bishiya ina dafe kaina, sabida juwar data kamani kawai senaga wannan yaro akaina yay min sallama cikin nutsuwa , yana tambayata baba mai yake damunka haka, sena ɗago nace masa kaina ke ciwo da kuma juwa wallahi aisha bakiga yadda ɗannan ya damuba da kanshi ya ɗagoni ya sakani amotarshi yacemin ze kaini asibiti a dubani abani magani nace masa yabari innaje gida inada maganina, kinsan seda ya kawoni har bakin layin gidana sannan ya ɗauki dubu ashirin ya bani, wato Aisha wannan yaro ɗan arzikine, amman yanzu na daina mamakin alkairinsa tunda bai ɗauka abanza ba jinin alhaji idirisa ai dole ya gaji alkairi".
YafaÉ—a yana kallon Aliyun da yabawa.
Shiko ko ɗago kanshi bai ba amman yana mamakin yadda har yau mutumin bai manta yadda akaiba  lokacin shima ya dawo daga office ne lamarin ya faru, shaff ya kuma mance, da batun seda yaga fuskar tsohon sannan ya shaida shi kuma abin ya faɗo masa.
"Wallahi kam baba maganarka haka take Allah bamu dacewa kawai".
Cewar usman yana kallon malam danshi bai mamaki ba sabida kowa a gidansu yasan Aliyu akwai tausayi duk zafinshi yana da mugun tausayi aranshi.
"Masha Allah baba gwara da Allah yasa muka sameka anan ɗin kaga base munje can ba gashi na kawo maka baba seka damƙa masa amana".
Dariya malam yay yana kallon usman tare da cewa.
"Aiko ni ko birnin sin wannan yaro ze tafi da balki wallahi ban damu ba sabida tun kafin nasan shine na yaba bare kuma da Allah ya haÉ—ani dashi na ganeshi kasan wannan shi ake kira da ka gina alkairi a baya domin ka girbi abinka agaba".
"To malam Aliyu ya kamata ka É—ago ka fuskance ni sosai tare da kunnen basira".
Cewar malam yana kallon fuskar Ali.wadda take can gefe guda.
Cikin nutsuwa kamala haiba Aliyu ya juyo yana kallon malam kacokan ya basa dukkan nutsuwar shi, aranshi yana mamakin komai ya kawo hakan oho?.
"Da farko dai Malam Aliyu ni dakaina da kuma wannan baiwar Allah".
Ya nuna mama da hannunshi.
Sannan ya cigaba.
"Muna miƙo buhun godiya wajanka da kuma yi maka addu,ar mai yawa mai albarka, yadda kai mana Allah yay maka yadda ka taimaki maraici ka rufa masa asiri kaima Allah ya duba bayanka kada ya wofantar dasu, naji abin alkairi a wajan ɗan uwanka abubakar da kuma usman mungode mungode"!!
Zaro manyan idanunshi waje yay waɗanda suka ƙara haska masa kyawunshi.
*WANNAN LITTAFI NA KUÆŠINE KADA KI KARANTA BAKI BIYABA NAIRA 200 BABU YAWA IN KINA BUƘATARSA TUN TUÆI WANNAN LAMBAR KAI TSAYE 08142105218*
Tare da kuma matukar mamakin mai yay masu haka suke masa godiyar data saka jikinshi yay sanyi.
"Aliyu ga amanar bilkisu nan mun baka har abada babu janyewa mun baka bilkisu kamar yadda ka buƙata kuma mun cika maka kudirinka na ɗaura muku aure ayau kamar yadda ka bukata harka turo mana usmanu da abubakar sabida haka yanzu muna jiran ta bakinka domin bama fatan balki ta kuma kwanar mana agida se agidan mijinta"
Cikin sauri usman ya tari numfashin malam.
"Ai malam wannan lamarin yay mana daɗi sosai Allah dai ya ƙara girma dayake shima ɗin yau kwananshi uku da yin auren farko amman duk da haka babu damuwa insha Allah zamu san abinyi sabida hakama bama bukatar komai naku Bebi kawai muke buƙata".
Wannan kalamin  na usman sune suka saka Ali ya farga ga batun nasu.
Innalillahi wa'inna'ilaihirraju'un hasbinallahu wani'imal'wakil!
Tabbas inba ƙarya kunnenshi yay mashiba usman yazo tare da abubakar yayansu sun karɓa masa auren wannan yarinya batare da saninshi ba.
Gumine ya soma fito masa ta saman goshinsa batare daya shiryaba.
Maganar mama ita takuma katse masa tunaninshi.
"Ni mahaifiyar Bebi ce nasan komai daga cikin halinta ina rokonka daka riken bebi amana intai ba dai dai ba ka hukunta min ita inda hali ka sakata a makaranta domin ta sami zurfin ilimi ko ze saka ta daina wannan shirmen nata nagode nagode................

Tofa akwai ƙura agaba
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *PART* 2

NAKUÆŠINE

                          *72*
Chapter 64 · 0% Book details