← Book details Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 115

Sashe 38

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da wani irin mugun gudu Aliyu kejan motar wanda cikin mintuna kaɗan ta kaishi cikin unguwarsu ta yahaya gusau,Cikin zafin nama da kuzari yake danna uban horn abakin tafkeken gate ɗinsu cikin mintuna ƙalilan sojojin dake tsaron gate ɗin sukai saurin zuwa gaban gate ɗin tare dajanshi suka bude mishi cikinsa. Hannu suke ɗaga mishi cikin girmamawa alamun suna mishi barka da zuwa kenan,Shiko baima kula da yadda suke ɗaga mishi hannunba, danna hancin motarshi yay zuwa cikin harabar adana motoci tare da fitowa daga cikin motar phone ɗinshi kaɗai ya iya rikewa se keyn motar yana tafe yana hade hanya cikin ƙanƙanin lokaci ya isa part ɗinsu wanda yay amfani da ƙofar baya wajan ɓulla zuwa samanshi domin baison hayaniya a halin yanzu Acikin ƙayataccen falonshi ya zube saman one seater yana dafe kanshi wanda ke faman sara mishi, duk jijiyoyin kan sun tashi alamun yana damunshi sosai mikewa yay kamar an tsikareshi ya nufi gaban frij ruwa mai sanyi ya ɗauka tare da ɓalle marufin gorar ya kafa kanshi yana faman kwan kwaɗa kamar ze shanye dukkan ruwan frij ɗin haka yakejin maƙogoronshi na faman suya. "Why Aliyu mike damunka?" haka yake faman faɗi a fili bayan ya aje gorar ruwan dake hannunshi wadda take emty domin bai bar komai ba. Nufar cikin bedroom ɗinshi yay batare daya dubi inda ya watsar da phone ɗinshi ba. Sintiri yake acikin bedroom ɗin nashi tare da saka hannunshi yana yamutsa sumar dake kanshi wadda batacika yawa ba se saisaye kaɗan dayayi. Tunanin shi ya zurfafa akan wannan ƙaddararran auren daza'ai mishi wanda bai murnarshi ko kaɗan, Wanda damuwar hakan ta haifar mishi da mugun ciwon kai mai zafin gaske ya fuskanci kowa son wannan aure yake amman shikam baiko jin abin a farcen susanshi. Zama yay saman soparshi tare da kokarin tube rigarshi se a sannan yake tuno wannan yarinyar ta ɗazu tsintar kanshi yay da sakin wani murmushi na daban wanda ban san ma'anarshi ba. Tubewa yay jikinshi yay saura dagashi se dogon wondon rigar daya cire sekuma singlet faffaɗan kirjinshi wanda yake shaƙe da kwantaccen gashi bayyane,ɗora hannunshi yay a saman sopar idanunshi lumshe haƙiƙa yanada damuwa a ranshi amman baida wanda ze fuskanta da ita, gefe guda ga wani haɗaɗɗen ciwon mara dake kawo mishi cafka sakamakon body contact ɗin dayay da wannan ƴar yarinyar amman haka kawai jikinshi ya tashi wanda tun a mota yake faman haɗeshi amman hakan ya faskara, da ƙyar ya mike hannunshi dafe da west ɗinshi gaban cabet ɗinshi yaje tare da janyo drowwer wadda drugs ɗinshi ke ciki ɗaukosu yay tare da komawa ɗan ragowar ruwan dake tsakiyar table ɗin shi ya ɗauka ya balle drugs ɗin ya watsa tare da afa ruwa bisa bakinshi sannan ya koma saman sopar still kwantar da kanshi yay yana saƙe saƙe acikin zuciyarshi. Ganin time yanaja yasashi tashi tare da nufar bathroom domin yaɗanji releife babu laifi ruwa ya watso ajikinshi tare da ɗauro alwala, zube kayan daya cire yay acikin washing machine tare da fitowa jikinshi daure da faffaɗan blue tawul wanda kuma ya ɗauro karami a saman kanshi yana goge saman kanshi dashi. Ko cream bai shafa ba turare kawai yaɗan fesa kaɗan tare da nufar gaban close set ɗinshi shirya kanshi yay cikin ash jallabiya tare da fita zuwa falo lokacin anata kiran sallar magrib dan haka phone ɗinshi kaɗai ya ɗauka.tare da sauka ƙasa, Falon ammi ya shiga bakinshi dauke da sallama wadda yayta ciki-ciki, Ammi ya samu zaune akan sallaya tana lazimi gyaran murya kawai tai mishi dan haka bai zaunaba seya fita domin yaji ana kokarin tayar da sallah ya bari idan ya dawo ɗin suyi magana. Har zuwa sallar isha'i yana cikin masallaci kasancewar shike jan limancin masallacin time to time idan yana available, bayan an idar da sallah tare suka jero da usman suna tafe usman na addabarshi da labarin yadda ɗazu sukaje wajan da zasuyi taron wunin bikin Aliyun wanda shi baima san da hakanba bada ban usman ɗin ya gaya mishi yanzu ba. Taɓe bakinshi yay batare dayace uffan ba, kusan a tare suka shiga cikin babban falon abbansu wanda yake a farko kafin ka kai ga shiga ainihin falon ammi. Usman ne ya zube a ƙasan carpet yana faman mayar da numfashin gajiya kamar wanda yay wani abun sakamakon ƴar ƙibar dayake da ita, shiko Aliyu daga ɗan wani saman stoll na table ɗin tsakiyar falon yaja ya zauna yana ɗaukar wani ɗan littafi daya gani a saman table ɗin, idanunshi kafe akan littafin har abba yay sallama ya shigo bayanshi yaya abbakar ne, se nusaiba wadda take biwa Aliyu, tare da ƴan ƴaƴanta ƴan biyu a bayanta. Cikin sauri ya juyo cikin ɗubin mamaki yake bin nusaiba da kallo na yaushe kikazo? amman seya bar abin can ƙasan ranshi tare da mayar da hankalinshi kan yaranta ya saka hannu ya ɗagosu yana manna musu kiss a saman goshinsu. Gaba ɗaya ya mayar da hankalinshi kan yaran seda ya gama wasanshi da ƴan biyun waɗanda basufi shekaru ukuba, kuma dukkansu matane masha Allah, kyawawa dasu, sannan ya riko hannunsu sukai wajan abba wanda ya zauna akan lallausar darduma yana bawa ya abbakar umarnin ya haɗa mishi tv,gab da ƙafafun abbansu ya xauna yana aje yaran a saman carpet tagumi ya zuba tare da ƙurawa abbansu ido kamar bai taɓa ganinshi ba. Sarai abba yana lura da yadda yakeyin ɗin kuma yasan da abinda yake bukata sedai zurfin ciki bai barinshi ya faɗi abinda ke ranshi, sedai abba da ammi suna yawan gano idan yay hakan tabbas yana cikin damuwa wanda daman can tun yana ƙarami da haka suke gane yana da matsala ko damuwa cikin ranshi. Nusaiba ta zauna daga ɗayan side ɗin cikin girmamawa tace. "Yaya haidara ina yini kai kaɗaine yau ban gani ba, yaya aiki ya shirye shirye?" tafaɗa cikin mutuntaka. "Lafiya alhamdulillahi! ina su amir?" ya bata amsa idonshi na kan abba. "Suna school kasan ba,ai hutu ba, na barsu da abbansu kawai se masu aiki". Zaro idanunshi yay waje waɗanda suke ƙara mishi madarar kyau ɗan gaske, yana mata kallon bakida wayo. "Kina nufin kin barosu acan tare da wasu kika kwaso ƙafafu kika tawo ke?". Murmushi tai tuna yadda yake mutuwar son yara tasan idan shine baze iya ba. "Eh! mana bikin yayana guda wanda nakeji dashi duk duniya aiko cikine idan da damar na aje sena aje bare kuma yaran dazasu iya yiwa kansu tsarki". Dariyar usmance ta karade wajan. "Gaya masa dai ƴar nusai angaya mishi kowa mayen yarane irinshi". Wannan karon murmushi yay tare dajan bakinshi yay shuru. Ya abbakar ne yagama haɗa kallon bayan ya kamo tashar CNN zama yay shima daga gefe tare da ɗaukar remote control domin ya rage volume ɗin tv'n. Ammi ce tai sallama ta shigo se ƴan biyunta da amina waɗanda hannayensu yake ɗauke da manyan farantai na sliver guda uku waɗanda aka jero kayan abinci a samansu ajewa sukai daga gefe bayan sun gaisar da yayin nasu guri suka nema suka xauna, kowa ya halarta a wajan idan ka cire umar wanda ke legos, amman akwai abbakar, usman, aliyu, nusaiba, amina, hassana,hussaina, se ammi tare da abba, se ƴan jikokinsu waɗanda nusaiban tazo dasu daga birnin tarayya. Gyaran! murya abba yay sannan ya dubi usman. "Shehu fara bude mana taro da addu,a". Yafaɗi hakan cikin bada umarni. Batare da bata lokaciba usman ya mike ya jagoranci addu,ar kamar yadda abban yace bayan ankammala aka rufe da salatin annabi (s.a.w) se suka shafa sannan usman ya koma ya zauna, kowa ya bada hankalinshi akan abba. "To Alhamdulillahi! muna godiya ga Allah mai kowa mai komai tsira da amincin Allah,su ƙara tabbata ga annabi muhammad ( s.a.w ) amin, kamar yadda kuka sani ban taraku anan domin komaiba sedan murnar sha'anin bikin ɗan uwanku dazamu fara nan da kwanaki biyu, to Alhamdulillahi ranar da kowa acikin wannan zuri'a yake fatan tazo tofa gatanan Allah ya nuna mana fatanmu Allah ya basu zaman lafiya da iyalai masu albarka". Yaja fasali wanda ya bawa iyalan nashi damar amsawa da. "Amin". Sannan ya cigaba. "Muna fatan Allah ya sanya alkairansa acikin wannan zama ya ƙara mana danƙon zumunta da kaunar juna amin, Aliyu kamar yadda ka sani, ina son kaima ka zauna anan cikin gidan acikin ɓangaren dana mallaka maka bana son zuri'a ta tabar cikin gidan nan dan haka kowannenku na sama masa inda ze zauna, sedai kuma bayan aurenku da wata guda, zan turaka legos kucigaba da xama da umaru nan kuma ze koma hannun usman da fahad da mansur insha Allahu". (fahad da mansur ƴaƴan Alhaji babbane yayan abba). Nisawa ya kumayi inda falon yay tsit kamar babu kowa se saukar numfashinsu. "Abbakar ya baka gudun mawarshi amatsayin shi na babban yayanku magajina, yayi maka lefe akwatuna seti biyu, umar ya ɗauki nauyin yiwa ita wannan yarinya jeren kayan ɗaki shiko shehu ya ɗauke nauyin komai wanda za,aci za,a sha acikin wannan taro, nusaiba, ta ɗinko maka kayan dazaka saka tundaga ƙasar sinigal, amina ta cika muku store da kayan abinci suko ƴan auta, lemuka da ruwa suka siyo maka, nagaya maka hakane domin kaiwa ƴan uwanka godiya sannan kuma kaima ka ƙara akan alkairin da kake musu na zumunci fatanmu Allah ya ƙara haɗe mana kanku". Gaba ɗaya kanshi ya ɗauki zafi inama auren so yay da anga rawar kai duk da yaji dadin yadda ƴan uwan nashi sukai mashi amman abin bawani ratsashi yay ba sabida baya ɗaukin auren ze daurene kawai dan kyautatawa mahaifanshi. "Bakace komai ba, babana?". yaji saukar muryar ammi akanshi. "Hajiya kinsan ɗan nawa da kunya fa, yaudai burinki ya cika ɗanki ze aure sekibar yimai lissafin shekaru". Abban ya faɗa cikin barkwanci. Murmushi ammi tai tana nazarin ɗan nata wanda yaƙi koda ɗago kanshi bare yay godiyar da aka ce. Kamar ze kuka ya ɗago jan idanunshi yana fesar da zazzafar iskar baki. "Nagode Allah ya saka da alkairi". Abinda ya iya faɗi kenan murya a shaƙe kamar wanda yaci wani abun ya tsaya mishi a makoshin sa. Hirar yadda lamarin bikin ze kaya ita tacigaba da wakana acikin falon wanda Aliyu yay gum kamar ba shi za,a yiwa bikin ba. Har wajan 9 suna faman tattaunawa kafin amina ta mike ta
Chapter 38 · 0% Book details