Sashe 100
Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
haɗu da arfa sarkin surutu ko?" Tafaɗa tana zama a saman kujera. "Lahh mama daman shine kikace muna masa addu'a yanzu nake gaya masa ankawo lefen su anty hassana, lah mama daman shine yayanmu mai kyau" Ta faɗa tana naɗewa jikin Aliyu. Da sauri hassana ta fito ta maketa aikawa ta saka kuka tayi ɗaki aguje. "Haba da baki duketa ba yarinya ce ai" Ya faɗawa hassana wadda ta saki murmushi ta koma ɗaki. "Haka suke fama dasu damma dodon tasu bata nan aisu hassana basa duka Bebi ce mai azabar saurin hannu" Dariya ya saki kaɗan. "Mama yanzu bebi tana dukansu?" Gyara zama mama tayi. "Ai Aliyu bebi ko ƙoface ta bugeta wallahi seta koma ta rama sedai fa hannunta ya fashe kaga tana ƙarama intai faɗa aka duketa kwana take kuka! ai duk yarana Aliyu babu mai rashin haƙuri kamar bebi, nasha wahala akan bebi Aliyu gashi ta soma ciwo babu mai rintsawa duk yarana bebi tafi shiga ran jama'a sedai fa tafi kowa rashin ji" Dariya yake sosai yana hango yadda take masifar jin tsoronsa amman ashe agida ba kanwar lasa bace. "Ai Aliyu bazan iya baku arfa ba wallahi matarka seta sumar min daƴa daman sunata murna ta tafi, Bebi akwai saurin hannu babu ƙaddarar da zata saka na baku autata wallahi" Marai raicewa yayi yana faman magiya amman mama taƙi fafur sabida sanin halin ƴar tata. Kallonshi mama tayi cikin nutsuwa. "Aliyu nagode nagode Allah ya saka maka da aljanna ka sauya rayuwarmu daga ƙunci ta koma farin ciki ka gyara mana gida ka bamu kayan abinci kai mana ɗinkunan suttura, wai ashe har malam ma seda ka aika masa da kuɗi da kayan abinci duka dai nagode Allah ya biyaka" Sosai ta bashi kunya sukewa wanima bare surukansa,. "Mama babu komai fa wannan ba wani abu bane ai anzama ɗaya, insha Allahu zan aiko a ɗebi amaran ma akaisu ceɗi su zaɓi kayan ɗakuna ashe an kawo lefe" "A,a Aliyu haba ɗawainiyar da kai mana ma ta isa abin ai seyay yawa" Tafaɗa muryarta tana rawa. "Wallahi mama bata isa ba nifa karki damu bawai kuba ko wani kuka kawo zan masa mama sabida ina son Bebi, sosai, ai kun gama min karshen karamci da kuka bani ƴa guda baku duba cewar koni wanene ba wallahi nagode kuma xan riƙeta bisa amana insha Allah" Kunyace ta kama mama lallai yaran zamani se abarsu yanzu agabanta yake furta mata yana son ƴarta, shiko ko ajikinshi haka ya cigaba da janta da hira har yake gaya mata matar usman ta haihu, **************** Bai iya komawa wurin babar ladiba kai tsaye gida ya wuce yayi kwanan zulumi washe garima haka ya koma shagon wannan mutumin mai kayan lefe anan yakejin labari wai ashe mutumin ɗan damfarane wai sunje sunyiwa wani mutumi irin yadda sukai masa ashe mutumumin ɗan sandane shine ya baza jami'ai har aka ganosu ashe grp ne guda dasu na irin wannan damfarar suke karɓar hayar shago a kasuwa insun yi sesu gudu se wannan lokacin dubun su ta cika. Aka kamesu aka haɗa da masu basu hayar shagunan yanxu haka suna gidan horo na musamman. Awajan kawu tasi'u ya zauna yana kuka wiwi gadai karshen wannan mutumin yadda ya koma yasan shikam kayan lefen nan nasa sun dulmiya. A daddafe ya koma gida nan ɗinma ya tarar da ƴan uwanshi cirko cirko duk jiki a sanyaye. Ga ƴaƴa sunci duka wajan ƴan sanda. "Tasi'u ina ganin lokaci yayi da zamu saduda fa lokaci yayi da zamu aje maka man yaƙinmufa shekaru suna ƙara ja iyayenmu sun rasu mun cutar da ɗan uwanmu akan gadon damu bai mana ƙarkoba tunda musa yabar gidan nan muke ganin bala'i da masifa wani cigaba muka samu a rayuwarmu? to nidai na gaya muku yanzu xan tashi naje wajan aisha ta yafemin ƴaƴanta ma haka ko Allah ya duben ya yafen laifukana". Kawu sani yafaɗa yana kuka kamar ranshi ze fita. Atake anan kowa yay na'am da hakan shawara suka yanke akan su fara tunkarar gidan malam lado tukunna. Aikuwa nan da nan suka haɗu cif tare da ƴaƴansu maza sukayi sharaɗa gidan malam lado sukaje yana soro yana karatu se ganinsu yay akansa kamar an korosu. "A,a tasi'u salisu Rabi'u sani! zuwa kukai ku kasheni kome?" Yafaɗa a rikice. Jikinsu a matuƙar sanyi suka zauna a gefen tabarma. "Malam ba wannan ya kawomu ba, munzone akan mu baka hakuri sannan kai mana jagora wajan aisha wallahi bala'i yayi mana yawa" Dariya malam yayi. "Kodai kunzo cin arziki kunji labarin yanzu aisha ta wuce raini ai kaɗan kuka gani azzaluman Allah kuma jira sakamakon ku" Rantse rantse suka hau masa akan su wallahi basuma san da sauyin da mama ta samuba. Ganin yadda sukai namada ne sosai yasa jikin malam yayi sanyi. Da kansa ya aika aka kirawo su yaya aminu da sukazo ya zauna yayi musu bayanin komai. Dayake ƴan bokone tuni, suka nuna murnarsu suka kuma yi na'am da tuban da kawunan amaren nasu sukai dan haka sukai musu jagora zuwa gidan mama. Tun a bakin gidan su kawu tasi'u suka soma xare idanu katari da shegiyar motar Aliyu a kofar gidan ya kuma basu tsoro. Malam shiya soma shiga sannan sauran suka bisu. Mama tana zaune suna hira da Aliyu taga shigowarsu malam da sauri ta sauko kasa ta basa kujera ya zauna. Su nurane suka karaso suma tare dasu kawu. Gaisawa sukai da Aliyu inda mama ta sha jinin jikinta takuma haɗe ranta tamau ko gaisuwar dasu nura ke mata a ciki ta amsa falonne yayi shuru. gyaran murya malam yayi. "Aisha ni waye wajanki?" Yafaɗa yana kallonta. "Kai ubane na ƙwarai wanda ya tallafi rayuwar marayan Allah" "Da kyau kiramin ƴaƴanki" Tashi tayi ta kirawo su hassana bebi ce kaɗai babu. Aliyu ya mike zebar falon malam ya dakatar dashi. "Zauna mana Aliyu ai kazama ɗan gida kaima ma haɗu mu bawa babar taka baki" Zama yayi yana murmushi. "Aisha nazo na baki hakuri ga iyayen ƴaƴanki sun gane kurensu sunzo akan su baki hakuri kucigaba da zumuncinku, kamar yadda zumunci yake daman jijiyane daga Allah wanda ya sadashi Allah ze sadashi da rahama, wanda kuma ya yankeshi Allah ze yanke masa rahama, kin dai gani da idanunki yadda Allah ya nuna musu ko?" Kuka mama tasa awajan. "malam da ciwo fa malam kaga cin zarafin da sukai mana nida abbansu bada ban kaiba ina zamuje a kano malam a shagofa muke kwana nida ƴaƴana" Tafaɗa tana kuka. Aikwa nan da nan ƴan biyuma suka hau kukan kamar rasuwar abbansu ce ta dawo sabuwa. "Naji aisha Allah ma ana masa laifi ya yafe bare kuma mu ƴan adam ina haɗaki da girman Allah akan kiyi hakuri ki bar maganar, kinga ga surukanki nan a wajan bai dace kina kuka ba" Malam ya faɗa mata hakan cikin kwantar da murya. Suma su kawu tasi'un kuka suka saka. "Tabbas mun cutar da musa amman aisha muna rokonki da kiyi mana afuwa ki bamu damar gyara zumuncin mu" Ɗago kanta tayi. "Na yafe muku, nidai sauran ƴaƴanku gasu nan, suma ƴan biyu atake anan suka yafewa dangin mahaifin nasu nan kuma hira ta barke cike da nishaɗi sunayi suna kuma bata hakuri kamar zasu ari baki. Wayar kawu tasi'u ce tahau ringing yana ɗagawa ya dire yana furta. "Innalillahi wa'innah ilaihir raju'un ganinan" Yafaɗa a firgice Gaba ɗaya tambayarsa aka hau yi mai ya faru. Da kuka yake shaidawa malam abinda ya faru da ladi da khalifa. Zaro idanu Aliyu yayi yana jin jina rashin imanin khaleefa shiko nura tashi yayi tsaye. "Kawu ina ganin zan shigar da ƙara kotunmu dan wannan bai isa ya taka doka mun barsa ba sunana barrister nuraddeen adam rimin gado sabida haka zan tsaya maka insha Allah harse na kwatar maka hakkin yarka nike neman auren hussaina ga kuma ɗan uwana Dr aminullah adam rimin gado shikuma shike neman auren hassana, se wannan Md Aliyu idiriss mai atamfa nasan kunsanshi shine mijin bebi na gabatar muku da kammu amatsayin surukanku dasuka auri ƴaƴan ƙaninku dan nasan baku sammu ba" Sosai su kawu suka rude da lafazin nura. "ni ina aiki anan kotun dake court road,a matsayin lauya, se yayana yana aiki a asibitin malam aminu kano, ƙwararren likitan matane, wannan kuma nasan kuna da sanin ɗane wajan Alhaji idriss mai atamfa textiles kuma shine director manager na kamfanin mai atamfa wanda ke sharaɗa kamfani nasan dai ko baku sanshi ba kunsan sunanshi a redio" Ya nura ya faɗa yana mai fiddo da wayarshi. Rudewa su kawu sukai tsoron Allah ya kuma kamasu lallai baka raina mutum domin baka san mai Allah ze masa ba, jiba aisha bata da ƴaƴa maza manya amman Allah ya bawa ƴaƴanta mata maxaje na nuna sa'a lallai ka tsayama ka bawa ɗanka tarbiyar ƙwarai jarine yanzu inda ta saka ƴaƴan a gurbatacciyar rayuwa da bazasu taɓa xama haka ba. "Aisha mungode da samun uwa kamarmi kin jajurce wajan bawa ƴaƴan ɗan uwanmu tarbiya wadda tasa har Allah ya basu mazan ƙwarai madallah da samun uwa marar son abin duniya kamarki" Suka faɗa a tare. "Ni yanzu zan koma asibiti wajan ladi sabida yanzu ance ana bukatar jini da allurai wai tana ta wani abu kamar jijjiga" Mikewa sukai mama ta bisu tana musu sallama tana kuma jin tausayinsu sabida yadda duniya ta murxasu. Cikin sauri Aliyu ya bisu yaran sune suka tafi gida sukuma ya ɗaukesu a mota suka nufi asibitin harda ya aminu ma. Transper suka ɗauka zuwa wani asibitin daban wanda Aliyu ne yay bill kuɗi har wanan dubu ɗari ukun ta jiya seda ya biya. Asibitin kudi mai kyau aka mayar wanda nan da nan Aliyu ya sakar musu kudi aka soma bata taimako fiye da wanda aka bata abaya. Bai baro asibitin ba seda ya biya kudin komai kana ya cikasu da kuɗi yanajin idan yay musu kamar mahaifin bebi yayma ne. Fitowa yay kawu tasi'u da rabi'u suka biyoshi suna faman masa godiya hatta babar ladi seda tai kukan daɗi. "Kaga ikon Allah ko tasi'u? suda muka walalanta ashe ajikinsu zamu huta" Rabi'u yafaɗa yana murmushi. Sosai suka saduda da lamarin rayuwa kuma sukai nadamar abinda sukai abaya. Mama da daddare sukazo harda abincinta koda taga ladi seda tai kuka su