← Book details Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 115

Sashe 83

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Mayar da ƙwallar datake ƙoƙarin zubo mata tayi kana tace.
"Shinkafa da salak da nama".
Murmushi yayi irin na gefen baki sannan ya dubeta da ƙasan idanu.
"Tofa harda salak da nama?".
YafaÉ—a yana É—age mata girar sa guda.
Tura kanta tayi a tsakanin cinyoyinta tana dariya ƙasa ƙasa sabida yadda yay acting ɗin nasa harda kwaikwayon muryarta.
"Hmm sarkin rigima kenan wai kece autane wajan mama?".
Taji sautin muryarshi kamar an jefo ta cikin dodon kunnenta.
Ɗago kanta tayi tare da kallonshi ganin yadda yay mata ƙuri da ido yana kallonta yasa taɗan kauda kanta gefe ƙaɗan sannan tace.
"Taɓɓijan akwaifa ihsan da arfa autar mama kenan".
TafaÉ—a tana dariyar da tunda ya É—aukota jiya batayi ba seyau dataji ya ambaci sunan mamanta.
"To sewa kuma?".
Ya kuma tambayarta idanunshi still cikin nata damma tana kauda kanta ne.
"Kaga daga hassana da hussaina se shahid É—an rainin hankali" tafaÉ—i hakan tana harara da ido kamar shahid É—in yana gabanta.
Sannan ta cigaba.
"Se Bebi se ihsan se arfa"
Murmushi yayi aransa yana nanata kuruciyarta
"Wacece Beby kuma?"
Taji maganarshi akanta.
Wurr tayi da idanunta kaÉ—an alamun irin mamakin nan sannan tace.
"Gata agabanka kwa tana maka magana bafa Beby ba, Bebi ake cewa se an É—aure sunan naji kai kana faÉ—in Beby kamar ta wasan Æ´ar tsana"
Tsintar kanshi yayi dayin ƴar dariya kaɗan yanajin yarinyar tana burgeshi idan tana magana sabida komai faɗinshi take direct ba kwana kwana dominshi yafi son mutum simple ya tsani mutum mai nuƙu nuƙu sabida yawancinsu munafukai ne acewarshi, ita kwa wannan daga gani zatai sauƙin kai tare da saurin sabo yana tunanin ta hakan kaɗai ze kuma janyota jikinshi harya bata dukkan wata dokar daya dace ya gindaya mata batare daya takurata ba.
"To nima nace BEBI" yawani ja sunan kamar shiya soma raÉ—a mata shi.
Dariya tayi kaÉ—an tana mamakin dama yanada surutu haka? ( hmm nima dai Bebi yau nasha mamakin wai Aliyu ne ke zuba surutun nan har yana dariya anya kwa Ali hmm bara dai nai shuru).
Shurune ya kuma biyo baya kafin taga ga muskuta kaÉ—an ya zaro wayarshi yana dannata, minti É—aya taga ya kara wayar.
"Hellow goma kana daga ina ne?". bataji mai yace masa ba tadai ji shiɗin yana cewa"ok da Allah ka biya kayomin take away guda biyu sannan ka siyo kaji masu yawa pls inda halima katawo mana da ɗan ƙaramin frij" jimm yay kana taji yace "ok nagode" sannan ya katse wayar kallon agogon hannunshi taga yayi setaga ya zaro ido kaɗan.
"Lahh lokacin sallah yayi"
Seya miƙe.
"Ki tashi kiyi sallah nima zanje na dawo amman zuwa anjima goma ze kawo saƙo bance ki fita ba ki zauna a ɗaki inya gama shigo da kayan seki fita ki ɗebe dafatan kin fahimce ni sena dawo".
Itama tashi tsayen tayi tana kallon yadda ya kere mata a tsaho nesa ba kusaba aranta tana yaba kyawun halittar da Allah ya bashi.
Idanunta zube a bayansa tace.
"Katu romin mufidan, to kazauna muyi sallar mana anan".
Se lokacin ya juyo gareta sabida da ya kalli hanyar ƙofane ma'ana ya juya mata baya.
Saurin juya kanta tayi ta daina kallon bayansa seta kalli ƙasan carpet tana wasa da yatsunta.
"Ni ai tunda nake bantaɓa missing jam'iba ko ciwo nake sena fita nabi, sabida haka akanki bazan fasa ba".
Taji maganarshi acikin kunnenta.
Turo bakin ta kumayi gaba.
"To naji mufidan fa?".
Taku yake har yaje bakin kofa bayada niyyar tanka mata secan taji yace.
"Bazata zoba koda ita aka kawoki"
Yana faɗin haka taga ya buɗe kofar ya fice batare data ɗara daga inda take ba tafara dira ƙafafunta aƙasa kamar wata yarinya ƙarama................
11/14/21, 3:13 PM - Allah Akbar: *87*
Chapter 83 · 0% Book details