Sashe 16
Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tajima acikin banÉ—akin tana faman abu guda kafin ta gama ta wanke jikinta ta fito waje idanunta yayi wani mugun yin ja, É—aki ta shiga ta cire kayan jikinta tai saura daga ita se É—aurin kirji, tsakar gida ta kuma dawowa ta tarar da mama, tana buÉ—e kayan miya dasu shinkafa ga su shahid a zaune dasu hassana duk sunata taimakawa mama wajan kunce kayan wurin. zama tayi tana hamma tare da kallon mama"Mama kice yau zata fashe?".da kallo duk suka bita"Zata fashe a ubanki, maman kike gayawa haka shegiya uwar Æ´anci" cewar shahid wanda yayo kanta kamar ze daketa"A,a badole nafaÉ—i hakaba irin wannan gara dazamuci yau wani É—an albarkar ne yayo mana wannan taimako kamar yasan damunace akwai ci".wannan karon seda mama ta dara watakan matsalar Bebi dai É—ayace arayuwarta itace ci indai ita zata samu taci tofa hankalinta ze kwanta.
"A,a Bebi kiyi mana addu,a wannan wata damace rabbana ya kawo mana".........tas ta kwashe komai ta gaya mata kamar yadda ta gayawa su hassana, amai makon mama taga Bebi tayi farin ciki setaga ta miƙe tsaye tare da nufar hanyar kicin abinci ta lodo a kwano tazo ta zauna ta soma ci batare data ce komai ba secan kuma ta ɗago.
"Mama kin amince ƴaƴanki sutafi can kamfanin masu kuɗi su kai abinci?, mama bakya gudun wulaƙancin masu kuɗin nan na yanxu da wasun su basusan darajar ɗan adam ba?".da kallo kowa ya bita cikin mamaki,"Nifa gaskiya nafi ganewa awarar nan yadda duk wanda yay min naci uwarsa a sauki amman wannan kamfanin sam raina bai bani da alkairi akansa ba dan haka ban dani acikinsa".dukansu kallonta suke cikin mamaki jikin mama yayi sanyi sosai.
"Bebi kamar yaya babu alkairi ban fahimceki ba, duk da bakida wata nutsuwar kirki amman hakan baze hana na baki haƙƙinki anan ba".mama ta faɗa duk ranta yayi wani iri"Haba mama kema dai kin manta halin fatan tsiyar ƴar taki musamman idan ranta baiso abu ba,mudai zamuje Allah ya karya bakinki mai fuskar tumatur".cewar hussaina tana hararar Bebin.
"To Allah baku sa,a nidai kar ace wataran naje, ni wallahi mama banyi murna ba gwarama na koma skull É—ita ma baki É—aya".
Tafaɗa fuwww ta mike da abincinta tayi ɗaki, murmushi kawai maman ta saki tana addu,ar Allah ya zaɓa masu abin da yafi xama alkairi akan hakan amin.
Sosai suka fitar da komai tare da adana waÉ—anda zasu lalace shawararsu kuma ta tsaya akan zasuna yin dambu da alala kawai kafin suga kuma abinda Allah zeyi, har dare suna faman aikin shinkafar dambun sabida Æ´ar hausace, Ita kuwa bebi bata fitoba se alwalar sallar magrib koda ta fito tayi ta koma É—aki tayi sallah hijabi ta É—auka tayi gidan iya a É—aki suka kulle da sadiya,suna labaran shirmansu wanda babu komai a labarin se yadda zasuyiwa su salisa dukan tsiya.
"Ke bebi bakiji wata maganar danaji jiya ba?" cewar sadiya tana kallon Bebin,"Ina jinki bani nasha Allah yasa dai ba wani abun bane?"."Hmm kedai bari wai ashe yaya aminu da yaya nura Æ´an biyunku sukeso jiya naji suna gayawa iya amman baza,ai maganar ba se nan da Æ´an watanni kafin nan sun kare skull É—insu" wata kara Bebi ta saka"Wayyo ni harna hango yadda nake hararar su salisa a rabon kayan fati kuma wallahi bazamu gayyacesu iyayen gayyaba saboda kada su cinye mana kayan partyn mu".dariya sadiya ta saki"Kedai Bebi bakida wata magana setaci yanzu dai bana son ki gayawa kowa wannan maganar amanatun amana inkinci taciki babu ruwana", wata harara ta zabga mata"Wazan gayawa kema dai hmmm kenifa zancen makaranta naxo miki gobe zan koma dan wallahi bana iya wannan tallan kamfanin da mama ta samo mana ba nan ta zauna ta kwashe komai ta gayawa sadiya. dariya sukai atare sadiya tace"tabb wallahi nima na goyi da bayanki gwara tallar awarar akan kai dambu can sabida wajan fa naji ance akwai maza da yawa nikuma kinga bana son yawan maza awaje". tagumi bebi tai tana jin yadda sadiya ke shato sharri tana likawa wannan kamfanin wanda ko hanyarshi bata saniba.
Seda iya ta gama tuwo ta kwaso musu shi fall nan bebi ta lanƙwashe ƙafafu tana kai loma bakinta, seda suka share tuwon tsaf sannan sukai sallar isha'i kana Bebi taiwa iya sallama suka wuce gidansu Bebin.
Lokacin da sukaje duk gidan nasu yana hargitse sabida yadda su mama suka baje kayan aiki, da kallo kawai mama ta bita tare da cewa"Bebi zoke ki wanke Æ´an kwanikan can tunda naga dare bai yiba", da taimakon sadiya sukai wanke wanken sannan ta kuma raka sadiya hanyar gida, se ita kuma ta juyo.
A hanya taga habu mai icce"A,a Bebi se ina haka?" bata sami zarafin kallonshiba sabida tai mashi wata muguwar tsana sanin halinta yasa yaja kafafunshi ya koma inda zeyi ita kuma ta nufi gida, kanta tsaye É—aki ta nufa ta fito da uniform É—inta na makaranta tai pillow dashi haka ta kwanta da shirin skull gobe.
_YAHAYA GUSAU_
Yajima a masallacin yana addu'oinshi daya saba kafin liman ya shigo a tayar da sallah, koda aka idar ya jima anan ɗin har aka kira sallar isha'i yana yi ya fito kanshi tsaye ɓarin Alhaji babba ya nufa babban falon ɓarin ya shiga tare da sallama, matar alhaji babba hajiya tana zaune tana kallon saudi jin sallamar Aliyu yasa ta rage tare da faɗaɗa far'arta tana kallonshi tare da amsa mashi sallamar.
"A,a babana kaine awajan namu sannu sannu" tafaÉ—a cikin sakin fuska É—an zama yay yana gaisarta a saman carpet É—in, cikin sakin fuska dattijuwar matar ke amsa mashi"Alhaji yana nan kuwa?" yafaÉ—a yana kallonta"Eh yana ciki bara na sa akira shi".tafaÉ—a tana kiran"Nuratu!nuratu!!"wata budurwace ta fito tare da riisunawa "Yaya barka da dare".kana ta juya wajan hajiyar "Hajiya gani".bai amsa wa wadda take gaisar dashi É—in ba sema kurawa tvn wajan dayay idanu yana nazarin labaran da ake,"Yawwa je wajan alhaji kice masa Aliyu yazo".cikin sauri nuratun ta juya mintuna biyu ta dawo"Yace ya samesa a sitroom".tafaÉ—awa hajiyar kana ta juya ta koma inda ta fito, tashi yay tare dayiwa hajiyar godiya yabi ta É—ayar hanyar ya shiga sitroom É—in.
Babban mutum ne sosai mai yawan shekaru zaune akan kujera hannunshi dauke da carbi,sallamar Aliyu tasa ya É—ago cikin sakin fuska yana kallonshi"A,a babana sannu da shigowa" zama yayi a kasan carfet yana gaisar da tsohon tare da sada kanshi a kasa yana jin maganar tsohon.
"Yawwa abinda yasa na ce kazo shine, maganar bikinka da kanwarka shin meka shirya akan hakan?". wani irin takaicine yazo masa kirjinsa amman ya danne tare da É—ago kansa har yanayinshi ya sauya"Alhaji duk yadda kukai yayi".yafaÉ—a a dake, É—an jimm Alhajin yayi"To madallah tunda kace haka babu komai zamu zauna da sauran Æ´an uwana abinda muka yanke za,a sanar maka, amman kasan dai nan da sati biyu bikin naku babu É—agi ko?".girgiza kanshi kawai yay batare daya iya furta komai ba,"Wai kamarshi za,aiwa Auren dole lallai bada ban iyaye iyaye bane da babu abinda ze da waccan yarinyar.
"Bakace min komai ba Aliyu?"! Alhajin ya faÉ—a yana kallonshi"Alhaji babu abinda zance Allah ya kaimu".yafaÉ—a tare da mikewa yana sosa keyarshi kana yaja ya bar sitroom É—in bai kuma bi takan alhajin ba.
Murmushi Alhaji yayi tare da mayar da kanshi ya kwantar yana jan carbinshi.
Shikuwa kai tsaye ɗakinshi ya koma ya watsa ruwa again tare da kwanciya saman gado yana naxarin abinda ke gabanshi har wajan 12 bai rintsaba alwala ya mike yaje yayi kana ya tada sallah har wajan 3 sannan ya sami bacci, kiran sallar farko ya tashi ya bada raka'atul fijir kana ya sauka zuwa masallaci har wajan 6 yana can daga nan wajan dayake motsa jiki ya nufa wajan 7 ya gama komai ya sauko sanye cikin yadin kufta yana zuba kamshi ammi ya gaisar rannan a hade tare da mikewa ze fita"Bazakai break ba?" ciki ciki ya bata amsa daya makara sabida yana son yay landing komai sabida tafiyar dazeyi, "OK Ga Khadija nan zaka ajeta a skull tana shirin fitowa yanzu".harya mike ya koma ya zauna tare da dafe kanshi mintuna uku ta fito jikinta sanye da after dress ammi taiwa sallama kana ta gaisar dashi, bai amsa mata ba"Ammi na wuce office" "Nace zata bika ka sauketa a skull".girgiza kanshi yayi"Ammi nai latti sedai ta nemi driver".yana gama faɗin haka ya dauki car key ɗinshi ya kama hanya ze futa,"Yaya pls ko a jection ka saukeni zan sami napep" tafaɗa tana mikewa da jakarta a hannu ta bishi, adai dai corridow ya tsaya yana aika mata da mugun kallo"Ni sa'anki ne dan ubanki ɓacemin anan" yabuga mata tsawa kana yabar wajan yana huci wata motar ya shiga sabida tasa tana wajan gyara koda yaje aikin rannan nashi a hade yake wajan 4 ya tashi zuwa yay wajan bokking na jirgi kana ya koma gida ya soma shiri, wajan magrib yay wa su ammi sallama ya wuce airport jirgin dare yabi zuwa garin na legos wanda yabarwa usman ragamar komai na kamfaninsu na kano.
Washe gari bakwai Bebi tai makaranta, wanda hakan ya baiwa kowa mamaki agidan haka rayuwar bebi tai ta tafiya cikin wannan satin bata wani magana seta skull sabidama kada mama ta sakata a lissafin tafiya tallan kamfani, yau takama asabar tun wuri mama ta kammala komai ta haɗa musu abin bukata cikin tsafta ƴan biyu suka shirya kansu haka shahid ya samo musu mota har ƙofar gida ta ɗauki kayan nasu zuwa bakin tafkeken kamfanin na mai atamfa dake sharaɗa, da taimakon baban nazir suka shigar da komai cikin kamfanin daga gefen masallaci dakwai wata ƴar rumfa mai dauke da bencina da tebur a saman teburin ya aje musu kayan abincin nasu wanda tsananin mamakin girman kamfanin da yadda yake a tsare ya daskarar dasu hassana, zamansu da kamar mintuna uku ciniki yace salamu alaikum domin tuni har an cinye damubun har ana neman kari.
Kayansu suka haÉ—a wajan karfe 3 sukayo gida cike da tarin nasara.
11/14/21, 3:06 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
{ _HOT LOVE_ }
NA
*AUTAR MANYA*
_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._
*18*