Sashe 112
Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kuma tashi taji zata iya bawa mijinta dukkan kulawarta matukar tana son zaman lafiya dashi seta mike ta cire dukkan gandar dake zuciyarta, ada in mama na mata faɗa seta ɗauki abin a wasa amman kam yanzu tagane cewar sefa ta mike tsaye inba hakaba duk son dayake mata ze tashi a banza ne. Cikin nutsuwa ta kunna gas kana ta ɗora ruwan tea duk da yadda bata son warinshi amman haka ta daure ta haɗa komai na tea ɗin bayan ta gama ta fita main falo ta zauna carbi a hannunta tanaja gaba ɗaya nutsuwa ta sauka ajikinta tamkar ba bebin daba lallai zama da nitsatstse shike sakawa kaima kaji kazama nitsatstsen cikin zuciyarta take raya hakan domin zamanta da Aliyu ta ƙaru da abubuwa kala-kala na cigaban rayuwarta. Zamanta da kamar mintuna uku taji karar bude kofa bata ɗagoba sabida taji kamar matarsa ce. Cikin wulakanci dija take kallon yadda aka ɗora mata tukunya akan gas ɗinta kuma tasan ba kowa bace ba face amaryar Aliyu. cike da gadara ta dawo falon tana wani bude hanci a tsaye ta tsaya akan bebi. "Ke ƴar matsiyata ubanwa yace uwarki taƙi haɗoki da tukunya setawa zaki ɗauka angaya miki kayana na matsiyatane irin......, Ai bata barta ta karasaba cikin tashin hankalin jin wannan furuci Bebi ta mike ta kwashe dija da mari wanda hakan yay dai dai da shigowar Aliyu,cikin wani irin yanayi Dija ta ɗago a firgice zata zubawa bebi marin domin ta rama. Cak ya rike hannunta Bebi batai aune ba taji tagwayen marukan Aliyu a fuskarta har guda biyu. "This is the first and last dazan kuma ganin kin marar min matata duk da ina nuna miki so wallahi baki isa kin takan itaba wannan ƙanwatace ta jini and kuma matata uwar gidana sabida haka banga dalilin dazakiga fuskar marinta ba". Yafaɗa mata cikin tsananin zafin rai. Dafe kuncinta tai cikin mamaki take kallonshi. Murmushin dole ta saki, tana kuma ganin yadda khadija ke mata gwalo batare data bar Aliyun ya ganiba. Da sauri Bebi tai ɗakinta jikinta yana matukar rawa. Har wani jiri take gani. Hijab ɗinta ta ɗauka ta saka tare da takalmi kana ta fito falon tarar dashi tai tsaye ya goya hannunshi a baya yana kaiwa da komowa A falon alamun komai ya tsaya mai cak! Matarsa kwa tana saman kujera tana wani hura hanci. Rabeshi tayi ta wuce sabida babu abinda ze saka ta zauna tanaji gwara ta koma gaban mahaifiyarta taji da abinda ke damunta. Cikin zafin nama yasha gabanta. "Kada ki sauka Beby wallahi ranki zeyi mugun ɓaci in kika bude kofar nan" Yafaɗa cikin tsawar data saka hatta dija seda ta tsorata dashi. Wawan tsaki taja tare da nufar kofar ko kallonshi batai ba. "Wallahi sedai komai zakai kayi amman sena fita" Tafaɗa kanta tsaye. Hannunta yaja da ƙarfi yay bedroom ɗinshi da ita yabar dija da leken kofa datse kofar yayi tare da tsayawa a gabanta yana faman zuba uban huci, ƙam ta tsaya a gabansa gaba ɗaya hawaye ya gama jiƙa mata fuskarta. "Kaban guri malam zan fita ai nan ɗin ba ɗakin ubana bane zan tafi na barka da uwargidanka kuma kanwarka ni bare banga amfanin zama dakai ba kamatsa min na fita" tafaɗa tana mai kai mai duka a saman kirjinshi jijjigashi take da iya karfinta amman shiko ko gezau yama zuba mata jajayen idanunshi kawai yana kallonta. Seda ta jigata dan kanta sannan ta daina ta soma zuba uban huci! Riko tsintsiyar hannunta yay rikon tsauri gam yana mai zuba mata zafafan idanunshi masu uban girma da kaifi waɗanda sukai wani irin jajur fuskarshi babu alamun sassauci yake kallonta. "Bilkisuu"! Yafaɗi sunan adake. "Dan kinga ina sonki shine zaki nemi takamin matata? ko dija bata rigaki aurena ba ai agirme ta girmeki ni ba lusarin namiji bane bazan yarda da sakarci acikin gidana ba" Kokarin tureshi take amman yaki bata damar hakan. "Nida tacemin ƴar matsiyata ta zagi mahaifiyata akan na ɗora maka ruwan shayi a tukunyarta baka ɗauki mataki ba se ita dayake kanwarka ce tonima Allah yasa iyayena basu haifan ni kaɗaiba" Tafaɗa tana murguɗa mashi bakinta gaba. Kana ta cigaba dayi mai bayanin duk abinda ya faru cikin kuka! Jikinshi ne yay wani irin sanyi zubewa yay a wajan ya janyota jikinshi ya rungumeta kafin ya ɗagota. "In dai marina ze sakaki jin dadi ga fuskata kita mari har kiji zuciyarki tai sanyi pls am very sorry wallahi laifina ne da ban nemi ba'asi ba" Yafaɗa muryarshi na rawa kamar zeyi mata kuka! Tureshi tai tana kuka"kaima kasan bazan iya marinka ba, amman nima kabani waya na kira mama ta saimin tukunya sabida adaina min gori" tsananin tausayin maganarta yaji har ransa. "Ummi nine mamanki nine abbanki nine yayanki nine ƙaninki sabida haka komai kikeso zanyi miki indai kicin ne da kayan kicin duk zan miki kinji kanwata". Yafaɗa yana mai ɗagota hanyar waje suka nufa a falo suka tarar da dija tana faman kai komo. "Dija zauna xamuyi magana" Yafaɗa fuskarshi babu sukuni, zama tayi a gefen kujera inda ya zaunar da bebi a kusa dashi. "Ummi ki faɗi abinda ya faru a tsakaninku keda dija har kika ɗauki hannu kika mareta?". Batare da tsoro ko fargaba ba bebi ta mayar mai da duk yadda akai sannan ta ɗora da cewa........ "In kuma karya nake aje a duba kicin akwai tukunyar dana ɗora akan gas ɗin". "Ke dija mai yasa kikai mata haka? bayan kinsan komai na gidan nan mallakina ne haka zalika mallakin dukkan matar dana aurone? mai yasa kina babba bazaki assasa zaman lafiya agidan nan ba?" Sosai yake mata faɗa wanda seda ta raina kanta. Sannan ya juya ga Bebi itama yahau yi mata nata faɗan, akan me zata mari dija mai yasa bazata bari ya dawo ta gaya masa ba? daga karshe ya ɗora da cewa. "Dukkan ku kunyi kuskure amman ninafi ku yi domin ban tsaya naji ba'asin komi ba na ɗauki hukunci dakaina, sabida haka ina son daga yau kada wadda ta kuma tayar min da husuma ke anjima zan saka a gyara wancan extra room ɗin a maida miki dashi kicin ɗinki and store anan zakina girkin ki dan Allah ina son ku haɗe min kanku bana son tashin hankalinku pls". Yafaɗa yana mikewa ya nufi dakinshi shirin office yayi ya fito anan ya sami dija itako Bebi tana ɗakinta tana baccin daya zame mata jiki. Sallama yay mata ya wuce. Acikin satin kullum Aliyu yana like da bebi kamar cimgam yasa an gyara mata kicin ɗin dayace sabida haka yanzu babu zancen shiga kicin ɗin dija. Kowa girkinshi yakeyi. Seda tai sati guda sannan aka raba girki inda in yay kwana biyu a ɗakinta zeje na khadija yay biyu dayake ma shi baya bin ɗaki sedai kowacce ranar girkinta taje gareshi. Zaman gidan Aliyu ya koma kamar gasa domin ko wacce ta mike sotake taga ta ƙwaci kambun so wurin mijinta musamman a yanzu dayake kokarin nuna adalci a tsakaninsu domin duk son dayakewa Bebi baya yarda ya tauyewa dija hakkinta babu ta inba baya kyautata mata amman ita a nata ɓangaren kullum korafinta yaki yay mata ciki. Kwanan Bebi goma agidan ta saba da mutanan gidan domin sun ƙulle ita da zee matar usman haka nan sunyi sabo dasu amina domin kusan kullum tana wajan ammi tana koyon girke girke wajanta awajan su amina ko ta iya gayu ta ƙara koyar abubuwa na kwalliya haka nan zee matar usman ita take bata kayan gyara namu na mata da abubuwan rikita oga, Alhaji babba kuwa kusan duk girkin dazatai seta zuba takai masa wanda hakan yasa yaji yana mata wani irin so wanda ko ganinta in bai ba seyayta cewa hajiya matarsa ina ƴar albarkata yau ban ganta ba. Lokacin bikinsu hassana yayi wanda yazo kusan ɗaya dana ƙannenshi komai na hidimar da uba kewa ƴaƴa Aliyu yay musu amman abin takaici bai gayawa Bebi ko bikin ba har akai bikin aka gama bebi bata saniba. Haka nan aka faɗa bikin amina dana su hassana wanda a daran da za,ai mothers event ammi ta mikawa Bebi nata lefen da basuyi mata ba, akwatina ne saiti biyu haka ma dija akai mata na faɗar kishiya sosai Bebi tai murna. Tare da zee suka ɗauke kayan sukai part ɗinta dashi, abin takaici duk hidimar da akai Aliyu ya hanata ko leke wai acewarsa kada ta wahalar mai da bebinsa haka ze sakata a daki yayta faman abu ɗaya. Har akai biki aka gama ƴan uwa na nesa dana kusa suka tafi a wannan bikin Bebi taga nusaiba mai kama da Aliyu sak sannan suka gaisa da ya umar sabida ba'ai taro a sunan zee ba yasa basu zoba. Tunda anty ruma tazo biki taga bebi da ciki take faman zuga khadija akan damme ita tana zaune wata zatazo ta rigata haihuwa agidan, to hakance ta saka dija tai muguwar sauyawa Aliyu komi yace mata setace bazatai ba rashin kirki kala kala take masa abin da yasa yake rabuwa da ita sabida kar ace dan yay aurene ze wulakanta tata. BAYAN WATA BIYAR Lokacin cikin Bebi yana wata shida sosai yay wata irin girman dayake bawa kowa tsoro alokacin ta kafa mashi rigimar seya kaita wajan mama, seda ammi tasa baki sannan ta haƙura da maganar, lokacin ma yawanci tafi zaman wajan ammi domin shi baya samun zama sabida ya riga ya bude kamfaninshi na TOKARAWA wanda tuni har an soma aiki acikinshi wanda ya ɗora goma da baban nazir a matsayin manajojinshi,wannan dalilin yasa bai fiye samun zama ba. Matar goma ma tazo mata kusan ma tana yawan zuwa sabida tana mata kitso da kunshi, cikin wannan lokacin ne Allah yaywa Alhaji babba rasuwa mutuwar data girgiza ilahirin zuri'ar mai atamfa sosai Bebi ta dinga kuka! ranar uku mama tazo gidan tare dasu hassana da iya da sadiya da baba matar malam da wasu mata da bebi bata sansu ba, a part ɗin ammi suka zauna lokacin da bebi taga mama kuka ta saka mata sedai abinda ya bata mamaki sauyin dataga kowa yayi hatta su hassana sunyi wani irin kyau seda ammi ta basu wuri sannan mama take bata labarin duk abubuwan dasuka faru, awajan gaya mata bikinsu hassana ne tahau kukan mai