← Book details Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 74

Sashe 74

Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani nishin ciwon ta gama sannan tace ya dauko rezar. Yaje ya dauko ya dawo gabanta ya zauna tare da mike kafafu. Yana zama yaga ruwa yana fito mata ya dago kai a razane.
"Ruwan jikinki zai kare don Allah ki bari na kira ko Hussaini ne"

Jin bata amsa ba ya dan dago "Asmau kina jina"

Idonta a rufe ta gyada kai "faya ce ta fashe kada ka damu"

Yana kallon yadda take famam cije lebe tausayinta ya kama shi. Babu inda baya rawa a jikinsa idonsa a rufe yake ya fito da reza sai kyalli take amma bai san me ma zaiyi da ita ba. Sai da tace ya bude idonsa ya rinka gani ta kusa haihuwa.

Budewar yayi ya juya gefe tare da rike mata kafa yana ta faman cewa "push Matar Jikamshi, push, yauwa gashi nan kin kusa ko? Push, push nasan zaki iya"

Ji tayi kamar ta haure shi da kafarta don takaici. Wai push ga uban ciwo gashi ya kasa yi mata abin kirki. Sake cewa push yayi ta ce cikin bacin rai
"Idan ka sake cewa push wallahi zan haureka"

"Au toh, bansan ba'a fada ba. Naji haka akeyi a tv. Yanzu me kike so?"

Gumin fuskarta ya goge mata sannan tace "addua zaka rinka yi min kuma *ka bude ido ka kalli yadda baby zai fito* kada a sami matsala"

Ya rinka gyada kai tana magana. Ita ke fama da ciwon kuma ita ke fada masa yadda zaiyi. Daga lokacin addua ya rinka karanto mata itama tana yi. Can yaji ta fara nishi ya sake cewa push ai kuwa ta kai masa hauri da kafa. Ji tayi ta tsani kalmar gabadaya. Yana kallo kan baby ya fara fitowa sai ji tayi ya fara kiran sallah. A yanayin da take ciki babu halin dariya. Da yaga abin na gaske ne yace "na shiga uku in hade miki kafarki kada kiji ciwo."

"Kashemu zakayi ne? Ka tara hannu kada ya fado a kasa" Ta fada da kyar.

Yace "toh, ita rezar ina zan yanka miki?"

Tunani tayi kada yayi mata karin da bata shirya masa ba tace "ajiyeta a gefe tukunna" wai tana wannan yanayin yake damunta haka.

Ya ajiye ya mika hannu ya cigaba da kiran sallah tana nishi har Allah Ya taimaketa baby ya fito tare da mahaifa sai kukansa taji. Da jinin da komai Col. Ishaq ya rungume dansa yana hawayen farinciki. Asmau nuna masa yadda zai yanke cibiya sannan ta mayar da kai ta dan kwanta tana mayar da numfashi.

Da dan rungume a jikinsa ya zagayo ya rungumeta sunyi kace kace dasu.
"Allah Yayi miki albarka Asmau. Allah Ya sakawa iyayenmu da alkhairi"

Baby din ya bata yana ta canyara kuka ya dauki wayarsa lokacin biyar da rabi ya kira Hajiyarsa. Cikin bacci ta farka ganin mai wayar ta tashi a gigice. Tana dauka ta jiyo kukan jariri. Col. Ishaq yace "Hajiya mun haihu"

Bakinta ya kasa rufuwa don murna tace "kun haihu ko ta haihu"

Yana ta murmushi yana kallon Asmau da dansu yace "wallahi tare muka yi komai muna gida. Saura wankan ne ban iya ba"

Hajiya ko tambayar me aka haifa bata yi ba ta tashi cikin sauri ta tafi dakin Bilkisu ta tayar da ita tace ta kira mata Dahiru shine gidansa yafi kusa da nata yazo ya kaita gidansu Asmau. Da yazo suna hanya tana addua Allah Yasa haihuwar babu matsala.

Ai kuwa sun sha kallo don da dansa a kafada yazo ya bude musu kofa lokacin an fara kiran asuba. Hajiya tayi saurin karbar baby din tace maza yaje yayi wanka. Ko da ta shiga kitchen ya dora ruwa a manyan tukwane biyu akan gas cooker.

Wurin da Asmau ta haihu ya gyara shi tas ya dauke kafet din ya fito dashi waje. Hajiya ta yaba masa duk da bata fada ba. Asmau ta gani tana dauko robar wankan baby. Tana jin muryar Hajiya kunya ta kamata. Hajiya tace Bilkisu ta juyo mata ruwan tayi wanka ita kuma zata yiwa baby. Anjima kuma da kanta zata yiwa maijego.

Kafin takwas na safe Asmau maijego da jaririnta sunyi fes. Col. Ishaq kuwa baki har kunne. Tare da Hajiya suka je asibiti aka yi mata allurai aka basu magani suka dawo gida. Lokacin su Umma suka zo gida ya cika da yan uwa.

Col. Ishaq shima jegon yake don kuwa daki ya shige yana baccin gajiya saboda irin aikin karbar haihuwa da yayi.

Shi da 'yan uwansa sun nunawa Asmau gata sosai. Amatullah an dawo gida sai murna tayi kani. Kayan barka lodi guda su Mami suka kai gidansu Asmau.

Ranar suna aka shirya walima gagaruma aka ci aka sha yaro yaci suna Abdallah. Su Zulaiha, Rashida, Zubaida, Walida da Ma'u matar Qasim sun sha hidima.

Daren ranar Asmau tayi wanka ta fito ta sami su Ainau suna ta hade mata kayan barkan da ta samu. Hawaye ne ya ciko mata Shemau tace " zaki fara ko."

"Amatullah nake tunani, lokacin da na haifeta babu mai kaunarta. Ita nata uban ma bai san da ita ba har ya koma ga Allah. Ko pant bata dashi sai da Allah Ya hadamu da Zulaiha ta bata kayan Ali. Bazan taba mantawa da bambancin dan zina da dan aure ba. Allah Ya yafe mana" sai kuka yaci karfinta. Su Shemau sunji tausayinsa suka rinka bata baki.

Washegari Col. Ishaw yace tazo ta ga wani abu a waje. Mota ce mai kyau ya siya mata. Bata san lokacin da ta rungumeshi a wurin ba don murna.
*****

Duk abinda miji zaiyiwa mata Col. Ishaq yana wadata Asmau dashi. Ta bangaren yara kuwa duk yadda yake matukar son Abdallah hakan bai hana shi cigaba da nuna tsantsar kulawa ga Amatullah ba. Asmau bata taba ganin wani abu daga gare shi da zai sa taji ya ware Amatullah saboda ba tasa bace ko kuma yanayin haihuwarta. Shiyasa a kullum bata gajiya wurin saka shi a adduarta.

Abdallah na da wata uku Yassar ya dawo daga short service dinsa ya dage shi fa aure yake so. Ga ginin da Umma take yi masa da saura amma haka ya hada har da nasa 'yan kudin kafin aiki ya kankama. Bilkisu ta kunno shi sosai akan maganar aure kuma ya zama irinta. Dama zama dasu Jikamshi sai an koyi hali. Iyaye dai sunyi murna kuma an saka rana.

Bikin Walida ma ya tashi su Asmau sunyi rawar gani. Sai da aka gama ta fara shirin makaranta an gama komai. Jikamshi ya cika alkawari bai hanata ba. Yarinya ta samu suke tafiya tare tana rike mata Abdallah idan zata shiga aji. Yana da wata tara amma da girmansa ga kamaninsa da babansa kamar yayi kaki. A haka ne wata rana ta tashi da safe da amai ko makaranta ta kasa zuwa. Gwajin farko ta gane ciki ne. Murna a wurin Col. Ishaq kamar cikin farko. Yayi ta tattalin matarsa. Dole ta yaye Abdallah ga karatu. A haka tayi ta fama har ta haifi 'yarta mace wannan karon a asibiti. Yarinya taci sunan Hajiya wato Lubabatu amma suna kiranta Amaturrahman.

*Bayan shekara uku*

Asmau ce tsaye a kofar dakin yaranta suna bacci. Amatullah da Amaturrahman akan gado suna rungume da juna. Shakuwarsu har ta baci. Saboda Amatullah bata iya fadin sunan kanwarta sosai itama idan an tambayeta sunanta sai tace Amatuyyahman. Duk yadda mutum yaso gyarawa sai tace ba haka Yaya take fada ba. Abdallah yana kwance a kan nasa gadon ga kayan wasa sun baza.

Hannuwan Jikamshinta taji ya rungumeta ta baya tare da dora kansa a kafadarta. A daidai kunnenta yake magana
"Tunanin me kike yi Matar Jikamshi?"

Kwantowa ta sake yi a jikinsa tace "ina godiya ga Allah akan ni'imarSa gareni."

Hannunta yaja suka tafi dakinsa ya tura kofar da kafa. Yana juyowa yaga tana hawaye.
"Allah nagode Maka baki da aiki sai kuka. Ni kaina daga haduwarmu zuwa yanzu sau nawa kina sani kukan nan. Yau kuma me ya faru?"

"Ina tsoron ranar da yaran nan zasu tsaneni. Gara gara ma su Abdallah amma Amatullah sai taji ina ma bani bace mahaifiyarta. Me zan fada musu a lokacin da suka kara wayo mutane suka sanar da su mamansu ta taba ciki a waje? Ya zanyi da Amatullah idan ta tuhumeni da gurbata mata asali? Idan suka kyamaceni yaya zanyi da rayuwata?"

Kuka take yi da gaske. Kwantar da ita Jikamshi yayi ya kwanta kusa da ita kanta yana kan kirjinsa.
"Daga ranar da kika ji rasuwar Abubakar da batun cikinki kin taba tunanin zaki kara samun nutsuwa a rayuwarki?"

"A'a"

"To a yanzu Allah Ya kyautata miki rayuwa ko kuwa?"

"Ya kyautata min"

"Ina so ki sani cewa tunanin gaban da baki gani ba babu alkhairi a ciki. *Abinda ake gudu* ya riga ya faru. Adduarmu shine Allah Ya kara karemu daga sharrin shaidan da mukarrabansa. Yara kuma da kike tunani bazasu taba guje miki ba da izinin Allah. Ke dai kiyi iya yinki wurin basu tarbiya da nuna musu so irin na uwa, sauran kuma mu barwa Allah. A karshe Matar Jikamshi, Asma'un Ishaq ina mai kara shaida miki idan duniya zata gujeki in sha Allah bazan taba rabuwa dake ba. Kece Ishaq, Ishaq kuma Asmau. I love you with all my being"

Kara rungumeshi tayi sosai tana hawayen farinciki "I love you too Jikamshina. Allah Ya barmu tare"

Suka ce Amin a tare.
*****************

*ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH*

Ina godiya ga Allah da Ya bani ikon gama wannan labari. Ina fata Allah Yasa mu amfana da abinda yake cikinsa wanda yake daidai. Kuskuren dake ciki Allah Ya yafe min Ya kawar da hankulanmu daga aiki dashi. Allah Ya karemu daga abinda ake gudu.

Godiya mai tarin yawa gareku masoya wannan labari. Hakika kun cancanci yabo domin kun bani kwarin gwiwa sosai. Bazan kama suna ba domin kuwa kuna da yawa kada nayi abinda ake gudu na manta da wasu. Allah Ya saka muku da alkhairi.

*Gaisuwa gareku* matan
1.Batul Mamman novel grp
2. Yan uwa na Fikrah writers association.
3. Taskira
4. Rufaida Omar fans
5. Maryam Ameen novels
6. Tafeesu novels
7. RAZ novella
8. Zauren Biebee Isah
9. Feenat Jaafar novels
10. Mss MJay novels
11. Hausa novels only
12. Hausa novels xallah
13. Zauren karatu
14. Fairytopia novels
15. Rash kardam novels
16. Queen Meemi fans
18. Fati Ali novels
19. N,N $ Z novels

Da wadanda ban saka ba duk ina godiya da mika sakon gaisuwa.
Chapter 74 · 0% Book details