← Book details Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 74

Sashe 47

Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga kan Mami har Musaddiq sun yaba da 'yan uwan Asmau. Kaddara kam babu inda bata giftawa. Kuma idan ta ratso kamata yayi dukkan musulmin kwarai ya karbeta hannu bibbiyu. Ashe ba daidai bane idan 'yar mutum tayi ciki ko zina a kyamaceta a koreta. Hakan ba komai zai kara musu ba sai bushewar zuciya idan basuyi sa'a kamar ta Asmau ba. Ba'ace a nuna musu sunfi kowa ba ko a shafe girman laifinsu a mayar dasu kamar komai bai faru ba. Amma a jasu a jiki ta hanyar nuna musu kuskurensu da wajibcin tuba da nesanta daga aikin dana sani. Asmau ta zama babban misali. Duk da iyayenta sun yafe mata kuma ta tuba amma fa har abada da gaban abada idan akwai baza'a taba mantawa ba. Ita da ta manta da haka a rayuwarta sai ranar da taji ance *shiga aljannah cikin aminci*. Ya Allah Kasa mu dace.

Ita da Anti Bintu suka fito rakiya. Sai a lokacin suka hango Bilkisu da Yassar a wurin wani benci. Kusan kowa ya manta dasu ma.

Duk abinda taji daga bakin iyayenta da kakarta ta tambayi Yassar ya tabbatar mata da haka ne. Bilkisu tayi kuka sosai taji tausayin Asmau. Ta fada masa shawarar da kawunta ya yanke na rabuwa da Asmau saboda matsalarsa. Nan fa hankalin Yassar ya tashi. Bai ga wanda ya dace da yayarsa ba kamar Col. Ishaq. Suna wannan tattaunawar ne suka hango fitowar su Ismail. Bilkisu ta rasa inda zata saka kanta don kunya. Kada ayi zaton ko Yassar saurayinta ne duk da kuwa hakan take fata. Amma bata riga ta faru ba. Yanzu kokarin daidaita Kawunta da yayarsa suke yi.

Allah Yasa hankalinsu baya wajen. Asmau da Anti Bintu ne suka gansu. Anti Bintu sai ta tsaya wurin Col. Ishaq saboda dama tana son ganinsa. Sauri zatayi suyi magana kafin Hajiya ta fito don Alh Adamu dasu Umma sun dan tsaya hira da ita. Ita kuma Asmau ta karasa wurin su Bilkisu.

Suna hangota suka tashi sai dai ta kula da hawayen da Bilkisu ke gogewa da sauri. Tsorota tayi ko Yassar yayi mata wani mugun abin. Tsaresu tayi da ido tana kallonsu daya bayan daya
"Me kuke yi a nan tun dazu?"

Yassar ya dan sosa kai yana murmushi "babu komai Ummin Amatullah"

Tayi dan tsaki "Bilkisu fada min kinji. Me yayi miki kike kuka?"

Itama murmushi tayi "Allah babu komai, abu ne ya shigar min ido"

Ko kusa bata yarda dasu ba. Daga ganin yanayinsu tasan basu da gaskiya.
"Tunda bazaku fada min ba bari na kira babanki, shi nasan zaku fada masa"

Zata juya Yassar ya riko hannunta da sauri "don Allah kada ma ki fara. Bari su tafi wallahi zan fada miki duk abinda kike son ji.

Suna kallo motocin su Ismail da Dahiru suka fita daga asibitin. Bilkisu tace "bari naje, Anti Asmau sai da safe."

Asmau ta dan bata rai cikin wasa "bazan amsa ba sai naji bayani."

Murmushi kawai Bilkisu tayi ta kama hanyar motar Col. Ishaq.
******

Tana karasawa taji Anti Bintu cikin tashin hankali tana cewa "wace irin magana ce wannan Ishaq? Haihuwa ta Allah ce. Yanzu saboda wannan zaka ce ka fasa. Wallahi baka ga yadda na shiga damuwa ba da naji zancen Qasim"

Rabin hankalinsa yana kan Asmau da yake hangowa suna magana da Yassar. Ba a nan inda 'yarta ke kwance tana jinya yake so taji zancen ba. Bilkisu ya kalla babu fara'a a fuskarsa.
"Kin gama kai gulmar? To kije ki fada masa nace kada ya kuskura ya fada mata komai yanzu"

Hanjin cikinta har wani kullewa yayi don tsoro ta koma wurinsu da sauri sosai. Ya mayar da hankalinsa ga Anti Bintu.
"Rashin haihuwa ba karamar matsala bace. Ke shaida ce ina sonta amma yaushe zan tauye mata hakkinta ta zauna dani babu haihuwa"

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, Asmau tana ganin jarabawa kala kala a rayuwarta. Tunda ta dawo gida ban taba ganin farincikinta ba kamar idan tana tare da kai. Ishaq wallahi tana sonka. Kada kayi mata haka. Yarinyar nan taga taskun rayuwa. Yanzu kuma zata rasa masoyi" Anti Bintu tana magana ita kanta kamar zata yi kuka.

Ji yayi zuciyarsa har wani zafi take masa. A jiya ya yanke shawarar ko me zai faru bazai rabu da ita ba. Amma magana daya tasa ya tuno da rashin dacewarsa da ita.
*****

Kafin Bilkisu ta isa wurinsu Asmau tayo gaba. Yassar yayi mata alkawarin sai sun koma gida zai fada mata komai, ita duk tunaninta ma ko soyayya sukeyi a boye. Bata matsa masa ba tace shikenan. Cikin nutsuwa ta taho wurin da Jikamshi yake tsaye da Anti Bintu. Ita dai Anti Bintun tana ganinta ta bar wurin zuciyarta tana kara karaya. Bata san halin da Asmau zata shiga ba idan taji abinda Ishaq yake tafe dashi. Gashi lamari na haihuwa ba'a daukarsa da wasa. Ita bata isa tace dole ayi auren ba tunda da kansa ya fada mata aurensa na fari shekarunsu goma shadaya da matar. Gashi suna rabuwa ta haihu.

Da zata bar wurin suka hada ido da Asmau tayi saurin sunkuyar da kai a kunyace. Shima ba dadewa zatayi a wurinsa ba saboda kada Hajiya ta fito.

Yaji dadin ganinta amma yanayin da zuciyarsa take ciki ya hana ya bayyana mata duk kokarinsa na boyewa. Da murmushi a saman fuskarta ta gaishe shi.

"Matar Jikamshi"

"Uhmm"

"Yau nafi sonki akan kullum, ji nake kamar yau na fara sonki ma" yadda yake furta kalamansa a hankali yasa taji wani dadi a ranta.

Mukullin motar yake dan kadawa yace "baki amsa min ba."

A zuciyarta tace zai fara sakata jin kunyar da ya saba. Kasa take kallo tace "to me zan ce?"

"Au baki ma sani ba, to bari na fada miki tunda ni nake son jin amsar. Ina ji idan baki fadi abinda nake so ba bazan iya kaimu gida ba." jikinsa duk a sanyaye yake. Daga yau baya jin zai kara furta mata kalmar so. Kallo kuwa tamkar ya cinyeta da idonsa. Jin soyayyarta yake sabuwa a zuciyarsa.

Dago kai tayi "don Allah ka dena fadin haka bana so"

"Nine bakya so ko maganar da nayi"

Kwabe masa fuska tayi tana shirin kuka yaji ta kara shiga ransa"kasan me nake nufi. Ka dena cewa bazaka iya zuwa gida ba"

Yayi dariyar karfin hali "to bani amsar da ta dace"

Rufe fuskarta tayi da mayafi sannan tace "I love you Jikamshina" da sauri ta juya zata gudu ya dakatar da ita ta tsaya amma bata juyo ba.

"Matar Jikamshi ki rike mijinki da gaskiya kinji ko. Allah Ya albarkaci rayuwarki"

Duk ya kashe mata jiki da kalamansa amma ko kadan bata kawo komai a ranta ba. Ita a zatonta shi yake nufi a matsayin mijin nata shiyasa tace
"Amin" sannan ta shige cikin asibitin.

Allah Ya taimaketa domin kuwa a hanya ta hadu da Umma da Mama sun rako Haj Lubabatu. Gashi babu damar canja hanya haka tayi mata sallama ta wuce su kuma suka rakata har mota.

Har su Umma suka zo tafiya Anti Bintu bata ga wani sauyi a tare da Asmau ba. Wannan ya sa tayi tunanin Ishaq bai riga ya fada mata ba. Duk su biyun tausayi suke bata, zata saka su a addua don ita bata san wace shawara zata basu ba.
*****

Bayan kwana biyu aka sallami Amatullah. Duk kwanakin da Mami tayi a Kano a gidan Col. Ishaq tayi su don kuwa da gaske Haj Lubabatu ta hanata kwana a gidanta. Ranar da zata tafi suka taru ita da kanneta suka sake bawa Hajiyan hakuri. Shi Col. Ishaq tuni ya ware dasu. Fushin bazai kaishi ko'ina ba yanzu tunda akwai gaskiya a maganarsu. Mami ta tafi akan duk shawarar da ya yanke su duka zasu bashi goyon baya.

A wannan lokacin ya rage kiran Asmau. Idan ta kira sai taji wayar a kashe. Nambobinsa biyu gareta duk bata samunsa sosai sai idan shi ya kirata. Shima din hirarsa tafi yawa da Amatullah. Idan ta karbi wayar daga gaisuwa sai yace mata zaiyi aiki ko zai kwanta. Tun bata dauki abin komai ba har dai ta fara tunanin akwai wata a kasa.

A bangaren Qasim ya matsa mata sosai da waya yanzu. Yazo sau daya ya koma bakin aikinsa. Nunawa yayi bai san da maganar Col. Ishaq ba. Ita kuma taki sakar masa jiki tana jira taji daga bakin Jikamshi tukunna.
*****

Haka tayi sati daya duk abubuwa sun cakude mata. Jafar ya karbi takardunta na SSCE zai sake nema mata admission. Amatullah tunda taji sauki Abdulhalim ya zo wata litinin da safe ya tafi da ita makarantar da yaransa suke yi. Makaranta ce mai tsada sosai domin kuwa ana arabiya da boko tun bakwai da rabi sai hudu da rabi ake tashin yara.
Ga karatun Qur'ani ba kama hannun yaro. Ita dai Asmau sai son barka. Kowa na kokarin kyautata musu. Shemau taso ace a makarantar da nata yaran suke zuwa aka saka Amatullah. Da yake saura sati daya hutun makaranta gwaji kawai aka yi mata suka bata aji, kayan makaranta da litattafai. Karatu sai an dawo zata fara sosai. Abdulhalim ya biya kudin komai. Alh Adamu ya kara masa kudi don kada ya shiga matsi tunda yana da nasa yaran. Amma yaki karba Amatullah 'yarsa ce baya bukatar taimakon kowa.

Da ya dawo da ita gida kuwa an sha labarin sabuwar makaranta. Tana ta zuba zance akwai lilo da wurin computer irinta Uncle Yassar. Hajjo da Umma kadai ke amsa mata. Asmau na rike da waya a hannu tana ta kiran Jikamshi ta kasa samu. Bata jima da ajiye wayar Qasim ba yace mata iyayensa suna so a sake basu ranar da zasu dawo.

Umma ce ta lura da yadda take ta tsaki ga waya a hannu tana ta dannawa.
"Asmau wa kike nema ne haka? Kinsan dai wani lokacin network sai yaki dadi amma duk kinsa abin a ranki sai tsaki kike faman yi."

Amatullah tayi caraf tace "kuma ni ta hana ni yi, wai tsaka ce yake yi"

Ran Asmau yayi mugun baci ta kai mata duka ta sameta a gefen fuska "ban hanaki idan manya na magana ki saka baki ba. Tashi ki bar wurin nan kafin na kara miki"
Chapter 47 · 0% Book details