← Book details Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 74

Sashe 28

Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asmau ta dage sosai kullum tana yiwa yaran lesson musamman na turanci da larabci. Duk wanda yake da homework zata zauna ta koya masa. A makarantunsu 'ya'yan gidan sun fita daban saboda kokarinsu. Ita kam Zulaiha zuwan Asmau ya janyo mata alkhairi. Manyan yaran Humaira, Muhsin, Amina da Habib duk makarantar gwamnati suke yi. Anisa, Aliyu da Amatullah kuwa a makarantar kudi mara tsada irin ta cikin unguwa suke. Gabaday Asmau ta tattara hankalinta ga 'yarta. Burinta a rayuwa yarinyar ta sami kulawa sosai ta kuma san addininta don gujewa [truncated by WhatsApp]
ABINDA AKE GUDU🙆🏽28

Batul Mamman💖

Da yamma Asmau ta dawo daga wurin aiki tun kafin ta bude gate din taji kukan Amatullah. Ji tayi kamar an tsikareta. A duniya babu abinda ta tsana kamar a taba mata 'ya da rashin adalci domin kuwa indai Amatullah tayi kuka a cikin gidannan baya wuce aikin Zinaru. Su Humaira ji suke yi da ita balle tace anci zalinta. Da sauri ta shiga ta sami Zinaru tsaye da bulala ta daga zata sake dukan Amatullah ga Ali da Anisa a tsaye suna nasu kukan. Asmau tayi saurin dauke 'yarta bulalar ta sauka a bayanta. Don ma da mayafi amma ba karamin shigarta tayi ba. Bata damu ba ta duba jikin Amatullah sai ga shati lafcece a bayanta tana ta kuka da sheshsheka.
Kawar da kan da take yiwa Zinaru yazo karshe. Bazata zuba ido a kashe mata 'ya ba. Cikin tsananin bacin rai ta dago ido tana kallon Zinarun da ko a jikinta an kamata tana dukan karamar yarinya haka.
"Me tayi miki kike mata irin wannan dukan?"

"Lallai Asamau wuyanki yayi kauri. Ni kike tsarewa da ido haka kamar wata sa'arki. Ko zaki rama mata ne?"

Amatullah sai wani irin kuka take yi, Asmau ta tambayi su Ali me suka yi.
Zinaru tace "jikokina babu abinda suka yi. Ba su nake duka ba. Wannan afiruwar yarinyar da har yau ba'a san ubanta ba ita na daka ehe. Na fada na sake nanatawa ta dena kiran Gidadona da Baba taki ta dena. Kun zo kun tare mana a gida kamar tare muka gina shi daku"

Rai a bace tace "akan wannan kike neman kashe min ita. A iya zamanmu ban taba tanka miki ba idan kina cin zalinta. Zulaiha ke shiga kullum. To ina so ki sani wallahi kika kara taba min 'ya za'a ji kanmu dake. Na baki girman da zan baki a matsayinki na uwa amma tunda hakan baiyi miki ba zan zauna dake yadda kike so. Kuma da kike cewa ba'a san babanta ba don Allah ki nuna mana naki dangin ko na baban Gidado. Mtsww, gida kuma yanzu na fara zama tunda kema ba naki bane."

Zinaru taji zafin maganganun Asmau "ni kike fadawa haka saboda baki da mutumci. Ita Zulaihan ce ta fada miki bamu da 'yan uwa?"

Asmau bata tsaya ta karasa sauraron Zinaru ba ta shige daki. Da kyar ta rarrashi Amatullah tayi shiru har bacci ya dauketa tana ta ajiyar zuciya. Kuka ne yazo mata da ta tuna irin rayuwarta. Yau da a gidan aure ta haifi Amatullah babu abinda zai fito da ita daga cikin danginta har wani ya sami damar fada musu magana irin haka. Ta tabbatar har ta mutu duniya bazata taba mantawa da cewa a zina tayi cikin 'yarta ba. Ta cuci karamar yarinya saboda soyayya.

Su Humaira sun dawo daga makaranta suma kannensu ke fada musu abinda Zinaru tayiwa Amatullah. Duk sun zo sun dubata har lokacin bacci take yi.

Bata farka ba sai bayan magriba da zazzabi mai zafi jikinta sai rawa yake yi. Lokacin Asmau tana kan abin sallah tana karatu taji fadowar Amatullah daga kan katifarsu. Sauri tayi taje ta dagata taji jikinta yayi mugun zafi. Hankalinta ya tashi ta rasa me zata yi mata. Da kuka ta fito da ita a kafada ta tafi dakin Zulaiha wadda bata dade da dawowa gidan ba. Har tana jin muryar Ali yana fada mata Zinaru ta zane Amatullah. Ko sallama bata yi ba ta shiga "Zulaiha taimakeni don Allah Amatullah zata mutu."

Zulaiha ta bar kokarin cire kayan aikinta ta karbi Amatullah tana salati. Kwantar da ita tayi akan katifa tana ta karkarwa. Asmau ji take inama ciwon ya dawo gareta. Ta matsa jikin bango ta jingina tana jira kawai ace mata ta cika.

Amina ce ta shigo Zulaiha tace ta samo mata ruwa mai kyau a roba da sauri. Asmau na kallo ta tubewa Amatulla kayanta duk da sanyin da take ji da aka kawo ruwan ta cire dankwalin kanta ta rinka guga mata ruwa a jikinta. Kukan Asmau kai kace Amatullah ta rasu. Zulaiha tana bata hakuri. Da taji zafin ya dan ragu tace bari ta cire kayanta su tafi asibiti. Asmau ta dauki Amatullah ta goyata suka fita. Yaran gidan duk jikinsu yayi sanyi. Kafin su karasa asibitin da suke aiki numfashin Amatullah har wani sama yake yi.

A asibitin emergency suka wuce likita da nurses suka karbeta. Ana ta gwaje gwaje Asmau tana kuka kamar ranta zai fita. Likitan ya fito ya bata takardar magani sannan yace zazzabi ne mai zafi da kuma alamun pneumonia(ciwon nemoniya ko sanyi da yake kama kirjin yara).
Hankali a tashe Zulaiha ta karbi takardar da kudin magani a hannun Asmau ta tafi ita kuma ta shiga dakin da aka mayar da Amatullah. Idonta a bude sai dai ta fada kamar ta dade babu lafiya. Tana ganin Asmau abinda ya fara fitowa daga bakinta shine "Ummi ni waye Babana ne? Zinayu tace Baba Gidado ba babana bane."
Wani kukan ne yazo wa Asmau. Yana daga cikin _abinda ake gudu_ ki haifi yaro kafin aure ya tambayeka mahaifinsa ki rasa amsar bayarwa. Tun farkon haihuwarta take fargabar irin wannan lokacin. Ta tabbatar idan Amatullah ta kara girma abin sai yafi haka. Cike da nadama take tunanin da tana gidansu Yaya Jafar, Yassar , Yaya Abdulhalim da Umar duk bazasu bar 'yarta tayi maraici ba. Allah Sarki Abubakar ta fada a ranta. Yau ga sakamakon rashin hakuri ta kusantar zina wanda ya janyo musu fadawa ga yinta. Shekara biyar da faruwar abin amma babu ranar da zata wayi gari bata tuna da wannan yinin ba. Hawaye ta share ta kirkiro murmushin dole "Ama babanki yana aljannah kinji ko. In sha Allah yana can yana jiranmu. Kullum kika yi sallah kice Ya Allah Ka yafewa babana Kasa shi a aljannah."

Ta zauna a kan gadon Amatullah tayi pillow da cinyarta."Ummi yaushe zamu je aljannah wurin babana? Ni yau nake son zuwa na fada masa Zinayu ta dokeni. Sai ya yama min ko."

Asmau tace "zamu je watarana kinji. Amma ba yau ba don Allah. Sai kin girma kin zama babbar malamar addini kin tara yara da yawa".

Amatullah tayi dariyar jindadi "idan munje shine zai kaini school. Ya siya min jaka mai kyau irin da takalmi. Har kayan sallah fa." Kula tayi da hawayen da Asmau take yi tace "Ummi ki dena kuka zai siya miki kema. Sai mu tafi namu gidan ko?"

"Uhm" kadai ta iya cewa hankalinta yana wani wurin. Yaya zata yi da Amatullah yarinya mai dan karen wayo. Nan gaba kadan tasan zata sake tayar da zancen.

A haka Zulaiha tazo ta same su. An bawa Amatullah maganinta da allurai sannan Zulaiha ta koma gida dauko musu kayan kwana.

Cikin dan lokaci labari ya karade asbitin 'yar Asmau bata da lafiya. Ma aikata da yawa suka rinka zo duba ta. Sai da sawu ya dan dauke wata likita tazo tana yiwa Asmau fadan irin dukan da take yiwa Amatullah wanda take tunanin harda shi da kukan da tayi ya sa mata zazzabi. Asmau ta tabbatar mata ba ita tayi dukan ba. Likita tace to dai ta kiyaye don babu mai kular mata da 'ya kamar ita kanta. Sannan dole a kula da hanata shiga sanyi da kura don tana ganin alamun asthma gareta ba pneumonia ba. Sake tsorata Asmau tayi. Tabbas Abubakar yana da asthma ba abin mamaki bane idan 'yarsa tayi. Amma irin halin da taga yana shiga ga kashe kudi wanda bata dasu sosai ya tayar mata da hankali.

Kwanansu uku sannan aka sallamesu. Kullum Zulaiha da su Humaira indai ba aiki ba ko su suna makaranta a nan suke zama sai dare su koma gida. Asmau kuwa taci alwashin bazata sake yarda da Zinaru ta taba lafiyar gudan jininta ba.

*****
Zinaru ce zaune a gaban wata kawarta da suke kasa kaya a kasuwa take fada mata irin maganganun da Asmau ta fada mata ranar da ta zane Amatullah
"Wato Kande maganganun sun kona min rai. Yarinya kamar wannan ina ta kawar da kai duk da bana son zamanta damu sai da ta kaini bango. Kuma ina ji lokuta da dama tana ziga shegiyar nan Zulaiha akan ta rabu da Gidado. Ni yanzu idan auren ya mutu ai ta tona min asiri. Ina zamuje mu zauna. Gashi dan banzan yaron har yau bai san ya girma ba. Daga shaye shaye sai neman mata ya iya."

Kande ta tabe baki "tun farko ke kika yi sake. Ke da kike da jari a hannu. Gidado ai *farar haihuwa* ne. Kina kalli ya rasa matar aure sai Zulaiha ga 'ya'yan masu kudi a gari. Kinsan mu da rauni akan mai kyau. Idan da hali kisa ya saketa ita kuma bakuwar ku koreta ya auro sabuwa 'yar masu kudi".

"Kin kawo shawara Kande. Amma babbar matsalar shine gidan nan nata ne. Ga yara har shida don bala'i haihuwa kamar zomo. Don ma Allah Ya takaita mana ta tsaya. Babbar fa zatayi shahudu yanzu. Kinsan auren kuruciya suka yi."

"Duk wannan ba matsala bane. Ke dai ki samu yaron nan ya dau saiti ya gyara kansa. Da kanki zaki bani labari. Kin sanni da shige shige sai na tayaku neman mai maiko."

Tafawa suka yi sannan kowacce ta cigaba da ihun azo a sayi kayanta.
*****

Kwanaki hudu a tsakani wurin karfe tara na dare Asmau ta fito zata je bandaki taji Zinaru tana ambaton sunanta. Tsayawa tayi taji abinda za'a ce tayi.
Chapter 28 · 0% Book details