← Book details Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 74

Sashe 49

Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shikenan Alhaji, Allah Ya zaba mata mafi alkhairi." Daga nan suka yi sallama Kawu Garzali ya tashi ya tafi.
*****

Inna mahaifiyar Qasim ce ta saka shi a gaba suna magana akan aurensa.
"Baffanka yace sunyi magana da Alhaji Adamu yace a dan kara musu lokaci zasu sanar da ranar da za'aje kai kudi"

"Eh munyi maganar. Dama Asmau nace ta fada musu da farko to ashe ma Baffa ya kira shi"

Rai a bace Inna tace "yanzu ita Asmaun har sai an bukaci lokaci kafin ace an yarda a kai kudin? Naga dai ita ce ma me abin bincike a kanta. Yarinyar da ta bar gidansu tsahon shekara biyar."

Murmushi kawai yayi. Inna bata son auren nan nasa duk irin yadda zaiyi mata bayani tace su rayuwarsu ba irin ta birni bace. A nan duk wanda yaji Asmau tana da 'ya sai ya tambaya mijinta rasuwa yayi ko sakinta yayi. Wasu ma suyi ta cewa mai zai sa Qasim ya fara da auren bazawara. Babu yadda za'ayi su boye gaskiyar lamari. Wasu ma sun dade da sanin rasuwar abokin Qasim da cikin da yayiwa budurwarsa. Gulma da kananan maganganu sai yawo suke. Ko kadan Inna bata jin dadin hakan duk da tana kokarin yiwa Malam biyayya ta nuna ta amince da auren.
"Sai anyi magana kayi ta murmushi kamar wani bazawari. Ya dai kamata kafin komai ya kankama kuje ayi mata gwajin 'yan cututtukan nan na zamani musamman kanjamau"

"Inna ba fa karuwanci taje tayi ba. Aikin asibiti tayi duk tsahon lokacin nan"

Tabe baki tayi "haka dai ta fada muku ku kuma kuka hau kuka zauna. Mace babu mai kwabarta ai sai ta mike kafa. Ni dai ba wani abu nace ba. Ayi mata gwaji ko don taka lafiyar. Gurbacewa ce dai ka gama gurbata mana dangi. Ko me kuka haifa nan gaba sai ance yayarsu shegiya ce"

Har ransa Qasim baiji dadi ba. Innarsa ta lura da yadda ya hade rai tayi murmushi "Baba kenan, kada ka daukeni muguwar uwa wadda bata son danta yayi aikin neman lada. Duk wata uwa komai shedancin danta tana son ya auri mace tagari. Abubuwan da kaga suna ta faruwa da yarinyar nab kadan ne daga *abinda ake gudu* a zina. Bana muku fata amma wata rana idan kunyi aure zata iya yin abu da zuciya daya amma saboda sanin da kayi na rayuwarta ta baya kawai sai shaidan ya kitsa maka zargi ka hau kai ka zauna. Karuwai da yawa sun yi aure. Wasu ma a gidan mijin suke sheke ayarsu. An sani amma da yake aure rai gareshi sai kaga ba'a sake su ba. Kasan halina bana boye abinda yake raina. Idan ka auri Asmau kayi mata halacci kuma ka rike amanar abokinka. Ka gyara abinda ya bata. Sai dai bazan fasa nanata maka ba ina so ka kara aure a gaba."

Duk maganar Inna yasan gaskiya ne. Idan Asmau zata taba mantawa da juyin da rayuwarta ta samu sai dai idan an goge wannan bakar ranar da tayi sanadiyar tarwatsa mata rayuwa.
"Akwai wadda kike so na aura ne? Da niyata bazan kara aure ba bayanta."

"Yo dan nan kasan me gobe zata haifar ne da zaka ce haka? Zabin wata matar yana daga gareka don kada ma a sami matsala nan gaba kace nice na zabo matar. Bari na shiga wurin Malam naga la'asar ta kusa"

Da Inna ta tashi Qasim dogon tunani ya zauna yi game da auren Asmau da ya takurawa kansa lallai sai yayi. Burinsa ya kyautata rayuwarta ba ya zama sanadiyar kunci da bacin ranta ba. A yadda ya fahimci hirarta da Col. Ishaq kwanakin baya ba karamin so suke yiwa juna ba. Addua ya rinka karantowa a zuciyarsa
"Ya Allah, na sani ina daga cikin mutanen da suka batawa Asmau da Abubakar rayuwa. Allah Ka yafe mana baki daya. Ka zaba mata miji nagari tsakanina da Ishaq. Idan aurenta ba alkhairi bane garemu Ka kaita gidan da za'a so ta dominKa."

Tashi yayi yayi shirin masallaci. Yana ganin janyewa kawai zaiyi amma zai tsaya mata sosai idan ta tashi aure. Dole mijin da zata aura ya kasance mutum da za'a iya yarda dashi. Mai amana. Shi kadai yayi murmushi da ya tuno irin kalaman da Col.Ishaq yake fadawa Asmau. Hmmm dole ta so shi ma. Shi kam ya manta rabonsa da tsara mace irin haka. Tun zamanin yana Qasim mai shafe 'yan mata. Rasuwar Abubakar tasa duk tunanin soyayya ya fice masa a rai. Kila harda rashin wannan yasa Asmau bata sauraron shi sosai. Mata da son soyayya kuma....
*****

Haj Lubabatu ke faman fifita an dauke wuta saboda hadarin da ya hado. Ta kira Bilkisu da ke zaune wurin taga tana ganin haske tana karanta littafinta na makaranta saboda test da zatayi washegari.
"Bilkisu ina babanki ne? Na zata ya dawo amma naji shi shiru tun dazu."

"Ya dawo Hajiya, na kai masa abinci ma"

"Duba min kiga me yake yi a ciki tun dazu. Kwanakin nan sai kace wata amarya bashi da aiki sai zaman daki"

Dariya Bilkisu tayi "Hajiya ita amarya zaman daki take yi?"

"Ban sani ba. Wuce ki duba ga magariba ta kawo kai."

Da sallama Bilkisu ta shiga dakin. Duhu ta gani duk labulayen a sauke ga zafi. Daga kan gadon ta hango shi a kwance ya rike kansa. Saurin karasawa tayi bakin gadon
"Uncle Ishaq" ta kira shi a hankali.

Da kyar Col. Ishaq ya iya bude idanunsa. Kansa ke masa wani azababben ciwo kamar zai tsage. Kwana uku kenan yana fama amma na yau yafi tsanani.
"Uncle baka da lafiya ne, bari na fadawa Hajiya."

Ta tashi zata fita wayarsa tayi ringing. Bata yi niyar dauka ba sai da yace "dauki wayar nan Safiyya ce take kira tun dazu. Idan kin amsa ki kasheta kawai. Ga dayar can a kusa da tv itama ki kashe"

Muryarsa da kyar take fita. Hankalin Bilkisu a tashe ta dauki wayar ta fita. Karawa tayi a kunnenta tace "Anti Safiyya bashi da lafiya Uncle din. Kamar ciwon kan nan da yake na bari..."

Gaban Asmau ne yayi mugun faduwa. Baki na rawa tace "Bilkisu nice Asmau. Tun yaushe ne bashi da lafiyar?"

Dan sauke wayar Bilkisu tayi daga kunnenta ta duba sunan. MJ ta gani wanda ta gane yana nufin Matar Jikamshi saboda ta taba ji Uncle din nata ya fada.
"Anti Asmau yi hakuri ban san kece ba. Yanzu na shiga dakinsa na ganshi a kwance. Zan fadawa Hajiya ne ko za'a kai shi asibiti. Dama yana yi idan baya samun hutu sosai."

Idanunta har sun ciko da kwalla , duk abinda tayi niyar fada masa na bacin rai tuni ta manta. Sake rike wayar tayi da kyau tace " Bilkisu don Allah ki kai masa wayar kinji."

Ta san baya son komai idan yana wannan ciwon musamman surutu. Amma kuma bazata iya cewa Asmau a'a ba. Juyawa tayi ta koma dakin. Yana nan inda ta barshi a kwance ta dan kara masa wayar a kunnensa tayi saurin fita kafin yayi mata fada.

Asmau ji tayi kamar tayi tsuntsuwa ta ganta tare dashi. Allah sarki Jikamshinta. Ashe bashi da lafiya shiyasa kwana biyu ta dena jinsa. Haushin kanta taji da har da tayi niyar nuna masa fushinta saboda baya kiranta kuma baije gidansu ba.

Yanayin canjin numfashin da take iya ji yasa ta gane an bashi wayar. Mamakin karfin halin Bilkisu yake da ta kawo masa a halin da yake ciki. Bari ya warke zata fada musu. Rashin Asmau yasa shi shiga damuwa sai yayi ta dadewa wurin aiki. Hakan ya tayar masa da ciwon kai. Sai kuma ga text da tayi tana fada masa yadda suka yi da Qasim akan zasu sake turowa. Tsabar kishi ne da rashin sanin me ya kamata yayi ya kara kwantar dashi. Kamar ba soja ba ya kasa daurewa zuciyarsa yaje ya fada mata ya janye. Dena kiranta a waya din ma ba karamin juriya yayi ba.

Muryarta mai sanyi yaji tace "Jikamshina me ya sameka?"

Bugawa zuciyarsa tayi da karfi da yaji muryarta babu zato babu tsammani. Ba karamin dadi yaji ba ya ratsa shi har ya dan manta da ciwon kan na 'yan dakiku. Bai iya ce mata komai ba sai manna wayar da ya sake yi a kunnensa. Ita kuma ta sake rudewa ko ciwon yayi tsanani ne
"Jikamshina nice, matarka ce, kayi min magana don Allah."

Shiru da ta cigaba da ji ne ya sakata kuka. Dama kullum haka take kamar tana jiran kiris.

Kukan nata murmushi ya saka shi babu shiru. Idon kuka kenan ya fada a ransa kamar yadda yaji a gidansu.
"Its ok ki dena kukan"

Cikin shagwaba tace "Kaji sauki? Ina da ina ke yi maka ciwo? Me yasa baka fada min ba kawai naji ka shiru"

Ta so saka shi dariya yadda yake jin muryarta a hankali amma tana rawa alamun kukan nata bai kare ba
"I miss you too" taji yace a wahale saboda ciwo.

"Uhmm?"

"Duk wannan tambayoyin nan nasan abinda kike son cewa kenan. Kinyi missing dina. But I miss you more Matar Jikamshi. Kin hana Ishaq sukuni."

Jin kanta take kamar anyi mata wani babban albishir da taji muryarsa har ya fara tsokana yadda ya saba. Ta kara kashe murya
"Nima ka hana ni. Har dan wuya nayi. Kasa naji ina kara ....uhmm....na fasa fada"

Sautin dariyarsa taji. Dama Asmau ce ciwon kuma ita ce maganin. Ajiyar zuciya yayi yana gyara kwanciya
"Yanzu ina kwance babu lafiya ma sai kinja min rai. Ki tausayawa patient."

"Kasha magani ne?"

"No, muryarki kadai ta isheni magani. Yau ki shirya zamuyi ta waya har sai kunnenki ya gaji"

Kamar yana gabanta tayi dan fari da ido "bana fatan gajiya da kai Jikamshina. Baban Ama _da kannenta_"

Yaji dadin furucinta amma kalmar karshe ta dawo masa da tunanin da yake addabar zuciyarsa.
"Matar Jikamshi ina son ganinki. Akwai magana mai mahimmanci da zamuyi kinji"

Tunanin maganar aurensu ne yazo mata tace "to Allah Ya kaimu. Ka bari sai kaji sauki sosai. Dama duk na damu ne da naji ka shiru."

"Ki kular min da kanki." Ya iya cewa zuciyarsa babu dadi ya ajiye wayar.
Chapter 49 · 0% Book details