← Book details Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 74

Sashe 60

Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Col. Ishaq na matsawa Qasim ya tambayi Asmau game da Ma'u. Tayi murna sosai ta masa bayani game da ita harda bashi numbar waya. Tana tafiya wurinta ta fada mata. Ma'u tayi murmushi kawai. Asmau tace alamun nasara kenan.

Har cikin falo aka shigo da angwaye aka dauki hotuna da iyaye da kakanni sannan suka tafi.
*****

Bayan magariba aka shirya tafiya Meena event centre inda za'ayi Sword Crossing. Wasu sun saba yi ido na ganin ido amma wannan karon tsarin na dare ne. Fili suka kama ba hall ba saboda shi zai dace da irin abinda suka shirya.

Kayan Asmau na yau har sunfi na jiya. Wannan ango da kansa ya aiko mata dashi dinki kawai ta kai. Material ne light green sosai. Riga da siket aka yi mata. A bisa umarnin ango ita da Amatullah suka dinka kayan. Wani irin dauri Najah mai kwalliya tayi mata da sauran material din wanda ba'ayiwa shafi ba. Kowa sai cewa yake tafi jiya yin kyau. Komai da ta saka ya dace da kayan sai daukar ido take. Amatullah ma Najah sai da tayi mata kwalliya kada da ta dace da yara aka daukesu hoto da Umminta. Ana fara tafiya ango yazo daukar amaryarsa. Drebansa ke jan motar sai wani abokinsa a gaba. Ko kadan ba haka yaso ba amma wannan tsarin na Mami ne. Kasa dena kallon Asmau yayi tunda ta zauna. Itama yayi mata kyau sosai domin kuwa korayen kayan sojoji ne irin wanda suke sawa lokutan taro a jikinsa. Sai yau ta kara jin soja yayi. Fuskar nan tasa ya gyara saje ya kara haske da kyau. Ji yayi inama daga wurin dinner sai gidansu. Ya mika hannu mai sanye da farar safar hannu mai santsi zai riko nata da yasha lalle suka ji kukan Amatullah. Kuka harda ajiyar zuciya wai Umminta da Babanta zasu tafi su barta. Ana ta rarrashinta akan suma can zasu je yarinya taki amincewa. Col. Ishaq yace a miko masa ita. A tsakiyarsu ta zauna ta hana ruwa gudu don har suka isa wurin surutu kawai take yi. Gata a tsakiyar iyayenta duniya tayi mata dadi.

Da suka je wurin ya fara cika. Duk masu cewa zasu sword crossing dinnan kowacce ta je. Gashi dai card admit ne amma haka wurin ya cika sai san barka.

Iyaye ma ba'a barsu a baya ba. Hajjo da Yaya tagwai ma duk tsufansu sunce basu taba ganin bikin sojoji ba dole ne ayi dasu.

Tare da sauran yara aka hada Amatullah sannan MC ya sanar kowa ya zauna ango da amarya zasu shigo. Yace a zauna ne saboda a tsaye dogaye zasu karewa marasa tsaho. Duk sojojin wurin cikin uniform din occassion suke. Dole su burge mutane. Sannan babu hargitsi don biki ne na manyan kasa da kowa baya son tsokano su.

Layi ne sojoji suka yi hagu da dama mutum goma goma. Kowanne ya rike hularsa a hannu daya sannan suka hada takubbansu ta sama inda amarya da angi zasu wuce. Kida ne mai taushi yake tashi aka umarci amarya da ango da su taho su wuce. Babu masu daukar hoto ta waya don ance kowa ya zauna. Masu daukar hoto biyu ne kawai wadanda aka hayo su suke binsu. Sun zo inda zasu shiga karkashin takubban hularsa na makale a hannunsa ya lankwasa hannun damansa yayi mata alama da ta rike. Duk da tana jin kunya haka ta zura hannunta ta cikin nasa suka fara tafiya. Jama'a kuwa sai tafi har suka wuce suka zauna.

Duk taron da akayi da tsari dole ya bada sha'awa. Irin wannan taron akayi a bikin Ishaq da Asmau. Tana daga mazauninta ta hango Qasim table dinsu daya da Ma'u suna ta hira. Ta nunawa Jikamshinta yayi murmushi "Allah Yasa shima tashi Asmaun mace ce tagari kamar tawa"

"Amin" ta amsa tana 'yar dariya masu hoto suka sami na yi.

Yaya Tagwai tace da Hajjo "wai ku a bikin Kano tsufaffi basa takawa ne? Tunda muka zo kidin yara ake sakawa suna ta rawa."

Hajjo tayi dariya sosai sannan ta yafito Yassar da hannu tace aje a saka wakar da zasu iya takawa kuma a fada filin nasu ne tsufaffi. Ango da amarya dole su sauko.

Yassar ya rinka dariya yaje ya fadi sako amma don shakiyanci wakar da yace a saka bata dace da Yaya Tagwai da Hajjo ba da sauran irinsu masu kashin kafa yayi laushi.

Sai da suka fito tsakiyar fili ga ango da amarya kawai aka soma wakar Uban Duma ta Ali Dawayya. Hajjo ta karkace itama Yaya Tagwai ta gotar da kafa daya zasu fara taku suka ji sautin yafi karfinsu. Kunnen Yassar ta jawo yace "wallahi Hajjo tsohuwar waka nace ya saka kuma ita ya saka."

'Yan taro suna ta dariya Yaya Tagwai ta gwangwaje abinta. Ango ma sai gashi yana juyi da abokai. Asmau dai kunya ta hanata rawa sai dariyar tsufaffi dake cikinta.

Iyaye ma sunyi tasu da amarya da ango asa ta turanci asa ta hausa. Da taro yazo karewa su Hajjo sunyi hanyar fita aka saka Mata ku dau turame. Dafa juna sukayi ita da Yaya Tagwai suka koma fili suka sha rawa. Su Ainau sun sha dariya kamar cikinsu zai kulle. Hajjo tace ita ba don amarya tayi ba. Dole ta taka idan aka ambaci sarki.

Sai wuraren shadaya da rabi wurin yayi saukin mutane anata tafiya gida. Col. Ishaq ya dubi Asmau wadda duk ta gama gajiya. Ga tsinin takalmi. Drebansa yace ya bashi key din mota ya bi wasu ya tafi gida. Abokinsa da suka zo tare yana wurin yace "ango duk tsiyarka fa tare zamu tafi. Naga kana sallamar dreba nasan ni zan biyo baya. Kasan Mami...."

"Mamo ba Mami ba. Ka fita idona Captain. Wai Baraka ba tazo ba. Don Allah ka dauketa ku tafi dare yayi"

Saluting dinsa yayi yana kyakyata dariya. "Na barku lafiya angon Asmau."

A can gefe daya kuma su Mami ke neman Bilkisu a tafi gida an rasa inda tayi. Tana can ita da Yassar a wurin wasu kujeru. Abinci yake ci yunwa ta dame shi yaji sallamarta. Har kusan kwarewa yayi don baiyi zaton ganinta ba. Tayi murmushi ta zauna a kujerar dake kallon tasa. Yassar ya ajiye cokalin yana kallonta. Tace "ci abincinka mana"

"Bazan iya ba. Ni bana iya cin abinci a gaban mutane shiyasa ma kika ganni a nan yanzu"

"Ni kuma kaga so nake kullum ka rinka ci a gabana"

Sauran abincin bakinsa ne yasa shi kwarewar da yake gudu da yaji abinda tace. Tayi masa sannu amma tarin yaki tsayawa. Da tayi magana sai ya sake yin tari.

Bilkisu ta dan harare shi "dama saboda ni kake tarin? To aiki ya sameka don bazan dena yi maka magana ba"

Yassar ya rasa me zai ce mata. Haka yake da kunyar mata tuntuni. Babu wanda zaice ga budurwarsa. Ta dan sassauta kallonsa tace "ni na gaji da kallon kallo da muke yi fa, sai yaushe zaka ce kana sona?"

Wannan karon da ya fara tari har sai da ya sauko daga kan kujera. Yana dafe da kirji tana yi masa sannu yace "ke haka danginku suke ne, basa jin kunyar magana"

Turo masa baki tayi "to ba wani bane a cikin 'yan biki yace yana sona ba. Kuma har cewa yayi zaiyiwa Uncle magana shima soja ne a karkashinsa yake"

Yassar ya ware ya koma ya zauna yana kallonta babu zancen wasa "don Allah kada ki amsa masa. Nima zanyi sojan nan har Yaya Ishaq ya karbo min takarda zanyi short service"

"Uncle Ishaq nake ce masa fa" tana magana kamar zata yi masa kuka

Duk ya rude da tayi zancen wani soja yace "to nima Uncle Ishaq kinji"

Ta juya masa ido "to kana sona kenan na sallami wancan"

Kai ya sunkuyar kasa da gaske kunyarta yake ji ya gyada kai a hankali.

"Ni da baki zaka fada"

"Kiyi hakuri zanyi miki text ko na kiraki"

Shan kunu tayi "zan cewa wancan ya turo kawai"

Yassar ya sake rudewa "me yayi zafi kiyi hakuri. Ina sonki mana ai ko ban fada ba kin sani"

Sai yanzu yaga alamu taji kunya ta rufe kuskarta da mayafi ta tashi "bari naje nasan ana jirana. Don Allah ka kirani fa"

Yayi murmushi "in sha Allah ina zuwa gida zaki ji wayata"

Sai da ta soma tafiya ta dan daga murya yadda zaiji tace "Yassar"
Ya juyo yana kallonta "dama karya nake yi, so nake kawai kace kana sona" daga haka ta tafi. Ya zauna yana sosa keya. Yana tunanin ko dai soyayya a jinin dangin Jikamshi take. Tasha fada kuwa a wurin Mami. To bukatarta ta biya ko kadan ranta bai baci ba.
******

'Yan uwan Asmau sunyi gaba da harda yi mata tayin ko zata bi motar Umar tunda Ainau ce kawai a ciki. Col. Ishaq ya jefi Shemau da kallo harda harara ta kwashe da dariya. Dama tsokanarsa tazo yi. Sai da yayi sallama da abokansa sannan yazo ya sameta a inda yace ta jira shi. Jikinta yayi sanyi tunda taga ya sallami 'yan motar tasu. Har wani dan tsoronsa take ji. Ya kula da canjin yanayinta a ransa yace baki ga komai ba.

Hannunta ya kama ya tayar da ita suka nufi wurin motar yaki sakin hannun. Wani iri take ji daban don bata saba ba. Idan ba bisa lalura ba tana iya rantsuwa banda Abubakar babu wani namiji da ba muharraminta ba da ya taba mata hannu. Shima jin hakan yake har ransa. Ya dade yana jiran ranar da Asmau zata halatta gareshi ya tabata batare da tsoron zunubi ba. Sai ma lada da zai biyo baya.

Gaba ya bude mata ta zauna sannan ya zagayo ya zauna wurin dreba. Ya tayar da motar sannan ya kamo hannunta ya dora akan giyar. A haka ya saka giyar ya soma tuki cikin nutsuwa. Zuciyar Asmau ta kusa ballo kirjinta don tsoro.

"Tunanin me kike yi ne"

Ta dan rufe idonta ta bude "babu komai" muryar nan a salihance take fita.

"Are you sure, har tunanin abinda zan iya yi miki daga nan zuwa na kaiki gida bai zo kanki ba?"
Chapter 60 · 0% Book details