← Book details Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 74

Sashe 61

Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta shiga kifta idanu kamar mara gaskiya. Saboda dare ne kuma titin babu motoci sai tsiraru shiyasa yake iya kallon bangaren da take.
"Kinyi shiru, bari na fada miki abinda naji zuciyarki tana cewa"

Kallonsa tayi tana jiran taji abinda zai ce. Shima sai da ya dan juyo sannan ya mayar da ido sa ga titi.
"Zuciyarki tace yau dai gani ga Jikamshina a matsayin maya da miji. Daga nan zuwa ya kaini gida zanyi kokari ko kiss ne nayi masa"

"La'ila ha ilallahu, ni banyi wannan tunanin ba..." Asmau ta fada tare da cukwikuye kanta cikin mayafinta. Kunya taji har bazata iya misalta ta ba.

Shi kuwa dariya yake mata. Yana son wannan kunya ta Asmau.
" ko kwana daya bamuyi da aure ba har kin fara karyata ni?"

Ta dan dago kanta daga kan cinyarta da ta rufe "ba haka nace ba fa"

Nishadi kawai yake ji gashi ga Asmai a matsayin maaurata. Ya daga gira daya "to yaya, kin amince kinyi wannan tunanin?"

Ta soma girgiza kai sai taga ya bata fuska. Tayi saurin cewa "Allah Sarki banyi ba amma dai naji nayi tunda haka kake so nace"

"Good girl, that means I will get one kafin mu rabu yau."

Ta turo baki don ta san idan ta sake magana wani abin zai kuma fada. A hakan ma bata tsira ba ya kalli dan bakin ya sha janbaki
"Mayar da lips din mana, ai ba yanzu za'ayi ba sai mun isa gida. Naga alama kin fini zumudi".

Kwafa tayi tana tunanin me zatayi masa, tukinsa yake hankali kwance. Tace "Jikamshina"

"Yes sweetheart. Kinsan fa yanzu duk wani suna da ake kiran masoyi a duniya zan kiraki dashi"

"Zan rama ne."

Yayi dariya "dama haka nake so. In ce wani abu ki rama yanzu?"

Ta gyada kai "I want to hug you"

Ta bata fuska a shagwabe "wallahi zan maka kuka"

Ya sami abinda yake so. Tana jinsa yana dariya ta ja mayafi ta rufe fuska har suka isa gidan Jafar. Yaron makota da yake masa gadi ya bude ga motarsa nan alamun sun dawo.

Ta kama kofa zata bude taji ta a rufe. Yace mata
"Kiyi hakuri kiyi min magana please"

Ta noke kafada, ya ce "to shikenan ina zuwa. Umarni na baki kada ki bude kofar nan"

Itama nata salon ramawar kenan yau duk abinsa bazata yi masa magana ba har ya tafi. Tana kallo ya bude ya fita ya zagayo ta gefenta ya bude mata. Sai da ta ziro kafafunta waje kawai ya durkusa a gabanta ya kafa kafar ya cire mata takalma yana bin yatsun kafar yana matsawa. Kasa magana tayi saboda bata yi zaton abinda zaiyi mata ba kenan. Ga kunya kamar tayi ihu. Har fargaba take kada wani ya fito ya gansu. Ta dan ja kafar ya rike sosai ya cigaba da matsawa yana magana a hankali.
"Tun dazu kike dingishi kina tunanin zan bari ki shiga ciki ne kice wata tayi miki tausa a kafa?"

"Don Allah ka dena kada yaya Jafar ya fito" tana magana idonta na kan kofa.

"Matsoraciya bari kiga wani abu" bata ankara ba taji yayi mata daukar jarirai. Abinka da dogon soja tashi yayi ya nufi hanyar kofar gidan da ita.

Asmau ta gama tsurewa ga tsoro tasa hannuwanta biyu ta kankame masa wuya "Ji...Jikamshi don Allah ka saukeni"

"Anki din, ki sassauta rikon nan kin shake ni"

Ta dan marairaice "idan aka fito aka ganmu fa"

"Zaki sa na shiga dake har dakin da kike kwana idan bakiyi shiru ba"

Shirun tayi don kada ta kara tunzura shi. Kanta a wurin kafadarsa ya cigaba da tafiya ta lumshe idanu. Komai nasa daban yake mata. Aure dadi aure lada yau ba tsoron fada take yi ba idan da wani zai fito ya gansu. Ko waye sai dai taji kunyarsa sabanin da wani namijin ne kawai da babu aure a tsakaninsu. Taji tsoron a kamasu sannan ta hada da lodin zunubi. Allah Ya kara karemu daga soyayyar tabe tabe babu aure wadda wasu suke yiwa kallon burgewa.

Tunaninta ya katse da taji ya ajiyeta a bakin kofa sannan ya bata takakmanta. Ya daidaita fuskarsa da tata ta hanyar rankwafowa ya rage tsaho suna jin numfashin juna. Idonta a rufe don fargaba.
"Ina jin na cancanci wannan kiss din da kika yi tunani dazu"

Bata bude idon ba taji ya hada bakinsa da nata. Alhamdulillah cikakken farinciki yana tare da aure. Da da yanzu ta kwatanta sai taji yanzu duk da tana jinta kamar akan kaya kada wani ya fito kuma shima tana jin kunyarsa amma yanzu ne hankalinta ya kwanta. Yanzu ne taji nutsuwar kasancewa da namiji-mijinta.

Ya dan dago kansa yana karewa fuskarta kallo kamar kada ya barta yace "saura ladan nauyi da na sha"
.
Tar ta bude idon "gaskiya bani da nauyi"

"Ba kiji yadda zuciyata ke bugu bane da na daukeki." Ya dora hannuta daidai kirjinsa ya sake kissing dinta.
"Ke dai ba na nauyinki bane, tsabar dadin kasancewa dake ne. Ba don ina jin kunyar Umma ba sai dai a biyoki da kayanki gobe"

Kunya tasa ta kasa kallonsa. Ya rungumeta sosai a kirjinsa zukatansu na kara son juna "yau zanyi bacci mai dadi Matar Jikamshi. Ina fata kema zakiyi. Sai gobe idan mun hadu a dakinki" a goshinta yayi mata wani kiss din ya tafi ya barta a tsaye tana numfashi da kyar.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽54

Batul Mamman💖

_Gaisuwa da fatan alkhairi gareki Maman Iman da Asim. Nagode Allah Ya saka da alkhairi._

Har motarsa ta fita daga gidan Asmau ta kasa motsi kamar an kafeta a wurin. Daga ciki taji kamar ana taba kofa tayi saurin bude kofar ta shiga da sanda ga takalma a hannu. Tayi sa'a masu kwanan falo wasu sunyi bacci. Na ido biyun kuma ba 'yan tsirku bane.

Dakin Sabira ta lallaba ta shiga suma suna kwance. A ranta tace wai sun dade ne da Jikamshi a waje? Ita fa gani tayi kamar bai jima ba. Tana dukawa ta ajiye takalmanta taji ance
"Sai yanzu"

Ba karamin tsorata tayi ba harda dan tsalle. Ta juya suka hada ido da Zulaiha tana murmushi.
"Meye haka kika firgice kamar an kama barawo. Kinga bakinki kuwa?"

Asmau tayi saurin dora hannu akan lebenta tana rufewa don a tunaninta ana ganin abinda Jikamshi yayi mata a bakin. Ko kafin ta shigo ji take kamar a lokacin yayi. Ido a waje tace "me...me kika gani a bakin nawa?"

Zulaiha sai dariya tace "amma dai kina da matsala. Kowa ya ganki sai yasan baki da gaskiya. Yanzu yanzu kin tonawa bawan Allah asiri har na gano abinda baki son na gane"

"Da gaske ana gani? Na shiga uku. Shiyasa a falo suka bini da kallo ashe." sai kuma ta sake rufe baki da ta gane sake tonawa kanta asiri take ta shige toilet da gudu tana jin dariyar Zulaiha.

Ita Zulaiha kwanciya ta gyara tana dariya tace "dama wannan angon naki ai banga alamar wasa ba tare dashi. Goben ma gara a kaiki da wuri kada muji dirar sojoji a gidan nan".
*****

Wanka Asmau tayi ta dauro alwala ta fito. Dakin dai shiru Zulaiha ma ta gyangyada. Ta dafe kirjinta oh Allah Yasa sauran basu gane ba. Amma Jikamshi ya janyo mata jin kunya sosai.

Ko mai bata shafa ba ta saka kayan bacci ta kwanta saboda gajiya. Ji tayi tana son kiransa taji ko yaje gida lafiya. Gashi har daya ta wuce idonta ya soye kamar ba wadda ta gaji ba. Tana ta tantamar kiran nasa taji wayarsa ta shigo. Saurin dauka tayi saboda kada ringing din ya tashi masu bacci.

Zaune yake akan gado ya jingina da pillow. Shima tunda yayi wanka bacci ya kaurace masa. Matarsa yake tunani da yadda yaji dadin hirarsu ta dazu. Tana dauka yace "me ya hanaki bacci"

Wannan murya ta Jikamshinta ita kadai tasan dadin da take mata. Sai taji kamar kada ya dena magana. Rufe ido tayi taki magana

"Ni ne ko? Na biya miki sabon karatu na tafi na barki da bugun zuciya"

Sake runtse ido tayi kamar yana gabanta tana jin kunyar kalamansa "ban ce ba fa"

"Ai ni nace. Kada ki manta ban dade da jin bugun zuciyarki ba a kirjina, kinsan shi baya karya. Nasan dai nawa yafi naki. Tsoronki yasa baki nutsu ba kinji zuciyar da take bugu da kaunarki. Burina na farko ya cika. Na aureki, na biyun ma in sha Allah zai cika. Shine mu sami zaman lafiya da fahimtar juna"

Tayi dan murmushi tace "Amin Jikamshina"

Kwanciya ya gyara yace "Kinsan tun yaushe nake son daukar ki? Tun ranar da kare ya biyoki. Daga ranar kika tashi daga matsayin Ummin Safina a wurina kika koma Matar Jikamshi."

"Wannan karen naka bai kyauta min ba"

"Ni kuwa yayi min komai. Ya bude kofar zuciyar Asmaun Ishaq. Ya kamata ki kwanta haka kafin gobe"

Hamma take yi amma kuma bata so ya ajiye wayar.
"Bana jin bacci. Gobe nayi idan an gama hidimar nan"

Tashi yayi zaune yana kallon wayar da mamaki kamar ita ce Asmau sannan ya mayar kunnensa "ba dai a gidana ba ko?"

Asmau tace "to a ina zanyi. Kasan nan yini za'ayi babu lokacin bacci"

"Kinga Allah Ya bamu alkhairi, ki kwanta kawai ko babu baccin ki rufe idonki ki huta. Wai bacci! Matar Jikamshi anya kina sona kuwa, a ina kika taba jin anyi bacci ranar da aka kai amarya idan ba auren dole ba?" magana yake da gasken sa ya ma za'ayi ta fadi magana irin wannan.

Sai da tayi dariya tace
"To bazan tambayeka me ya kamata ayi ba nasan halinka. Yanzu sai kasa na gwammace banyi magana ba, ka fi karfina"

"Muka fi karfin juna dai. Dama yaushe zaki tambaya bayan kin san abinda nake nufi."

Dariyarta yaji sannan tace "uhmm bari naje falo neman pillow din kujera na dakin sun kare ni kuma bana jin dadin bacci haka."

"Kice dai kawai kina so kiyi pillow da kirjin mijinki. Daga gobe ne fa Matar Jikamshi. Har kin fini....."
Chapter 61 · 0% Book details