← Book details Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 74

Sashe 71

Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari da kyar ta iya tashi ta shirya cikin wani riga da zani na atampa. Jikamshi yana makale da ita a dakin kamar zata gudu. Motsi kadan sai ya hau shafa mata ciki. Ita kuwa idonta na kan agogo tana tunanin fita daga dakin su gamu da Hajiya. Kai hatta Bilkisu ma kunyarta take ji. Ganin duk ta damu yasa yaje ya duba Hajiya tana daki ya fadawa pAsmau. Da sauri ta fita taje falo ta zauna dama bata so kowa yaga fitowarta daga dakinsa. Da Hajiya ta fito tana kallon Asmau ta kula da bala'in kunyar dake tattare da ita. Shima ya fito lokacin banda murmushi da kallo da yake bin Asmau dashi babu abinda yake. Sunyi breakfast Asmau duk a takure gaban surukar da ta gama ganin rashin kunyarsu. Hajiya tace "idan kun gama sai ku tafi gida saboda Safina ko. Zan sa a nemo miki mai tayaki aiki idan ba'a samu ba sai Bilkisu ta dawo nan wurinku saboda ta taimaka miki"

Suka yi shiru kawunansu a kasa. Zancen su tafi gidan ne yasa su jin kunya. Wato taga abin nasu ba mai karewa bane gara su koma gidansu. Zancen Bilkisu kuwa cewa yayi gara a samu mai aikin saboda baya son a bar Hajiya ita kadai. Bilkisun ce kawai a gabanta yanzu.

Suna sallar azahar suka fito Hajiya ta zuba mata abinci wai ya ishesu har dare kada tayi girki. Sai godiya take da yiwa wannan dattijuwa addua da fatan alkhairi. Yaushe zata manta da ranar da suka fara haduwa wanda tun lokacin Haj Lubabatu take kyautata mata gashi bata kyamaci aurenta da danta ba.

Tayi tunanin gida zasu wuce sai taga yayi hanyar Hotoro. Dadi kuwa ya kamata sai murna zata ga Umma. Lokacin da ya dena mata magana tana ta kewar mahaifiyarta amma ta kasa fada masa zata gida. Ya lura da murnarta har ya tsokaneta ko a nan ma zasu kwana ne su sake yiwa baby kani ko kanwa. Murmushi tayi, Jikamshi bashi da dama.

Umma da Hajjo sunyi murna da zuwansu sosai. Sai da Umma ta lura da ramarta to a gaban idon suruki sai ta kasa tambayarta me yake damunta. Tsoronta kada ya zamana gori ake mata tasa abin a rai. Don kuwa bayan sun dawo daga Yankari sunje Jikamshi inda wasu cikin 'yan uwansa mata suka fada mata magana son ransu. Sun ji amsa kuwa daidai dasu daga bakin Jikamshin Asmau. Ranar tasha kuka sosai da kansa ya kira Umma yace ta tayashi rarrashinta.

Ido irin na manya Hajjo tace "ya naga kina wani kyalli ne Asmau ga 'yar rama kinyi. Nasan dai kina tare da wannan sojan ba kewarmu kike ba"

Col. Ishaq da Umma suka yi murmushi ita kuma Asmau ta fada kan Hajjo tana dariya.

Tana fadawa ya tashi da sauri don ya manta Umman na wurin yace "wane irin ganganci ne haka don Allah kiyi hankali da jikinki"

Kunya ta kamata da su Umma suka soma kallonta. Hajjo tace "Ishaq ko dai abinda nake zargi ne? Naki fada ne dai ko ba hakan bane na tayar muku da hankali"

Asmau ta tashi ta fita daga dakin da gudu. Umma ma kunyar taji sai kace wata 'yar fari ta tashi ta bar dakin. Hajjo tace "Alhamdulillah kaga ikon Allah. Allah Ya kara hada kanku Ya kareku daga sharrin makiya da mahassada" idonta fal hawaye yana cewa amin tana addua.

A dakin Umma Asmau ji tayi Umman ta shigo ta rungumeta. Hawayen farinciki take itama "Alhamdulillah ala kulli hal. Kinga yadda Allah Ya dubi zukatanku da taimakon da kuka yi niyar yiwa juna Ya baku abinda zai kara inganta zamanku. Amma dama ba cewa akayi bazai taba haihuwa ba?"

Asmau tana nata hawayen ta labartawa Umma bayanin da yace likita yayi masa ba tare da ta fadi matsalar da suka fuskanta ba a dalilin cikin. Tasha addua a bakin Ummanta. Sannan tace duk abinda take so ta fada mata. Dole ne su taya Col. Ishaq tattalin abinda yafi so a rayuwarsa. A nan suka yi sallar laasar sannan suka wuce gida. Kulawa kam Asmau tana gani a wurin Jikamshinta sai godiyar Allah.
*****

Tana zaune a dakin da suke girki duk hayaki ya bude ta taji sallama. Mai sallamar yayi ta yi ta tashi rai a bace ga bakincikin itacen yaki kamawa ga takaicin lokacin girkin na kurewa yanzu fitsararriyar yarinyar nan zata zo ta sakata a gaba da rashin kunya. Fuska a daure ta bude karamin gate din tana kallon mutanen su biyu.
"Don jaraba kuyi ta sallama kamar kuna bin mutane bashi. Me kuke nema?"

Daya cikinsu yace "ina Gidado?"

Tana ta harare harare tace "kana magana da Zinaru ne uwar Gidado."

Dayan ya bata wata takarda "gashi daga Hajiya Zulaiha lallai ku tashi daga gidan nan da sati biyu ko a hadaku da hukuma"

Zinaru ta soma raba idanu. Abinda da ake gudu ya faru. Idan suka tashi ina zasu je. Yadda ta tsani rayuwar kauyensu ta dauko tilon danta ta gudo yanzu ana neman a mayar da ita duk tsahon shekarun nan. Sakin fuska tayi harda murmushi
"Ku dena ambaton Haj Zulaiha nasan bazata koremu ba. Wasu ne dai suke neman shiga tsakaninmu. Hala baku da labari Gidado mijinta ne har yau. Ai ba rabuwa suka yi ba. Sabani ne irin na masoya"

Wanda ya bata takardar yace "kinga ki bashi sakon nan. Lallai ne ya aiko mata da takardarta kuma ku bar gidan nan. Idan ba haka ba zaku ji sammaci daga kotu"

Zinaru na kallo suka tafi tace "shegu masu karawa wuta fetur."

Ciki ta koma ta tarar da Amarya tsaye a wurin girkin tana ta wani jijjiga jiki tana bata rai. Zinaru ta shigo ta dan rakube a gefen bango. Amarya tace "yanzu ko wutar baki hada ba bare ki dama min kunun. Idan cikin nan ya zube kwarankwatsa dubu sai na fadawa Baba ya karbe shagon da ya bawa Gidado. Ku haka kuke rayuwa ne shi malalaci ke kuma sai dai aci banza. Anjima kadan zani gida ni na gaji da wannan auren miji babu abinda ya iya sai bacci da shaye shaye"

Gaban Zinaru ya fadi. Yanzu dan shagon da Baban Amarya ya basu Gidado ke kasa gwanjo a kasuwa idan ya ga damar fita idan suka rasa shi ai tasu ta kare. Tun yaushe suka cinye jarin kayan miyarta shiyasa bata fita sai aikin Amarya da dan cikinta.

Tana dogon tunanin sai ga baban Amarya. Dama da wuya yayi kwana uku bai zo ba. Ita kadai ce 'yarsa yake ji da ita kamar rai. Zinaru tayi wuki wuki don bashi da mutumci ko kadan. Ko sallamarsa bata gama amsawa ba ya banko kai cikin gidan. Don abin kunya harda kai gwiwa kasa tana gaishe shi saboda ta girme shi ya amsa yana shan kamshi.
"Ina shi yaron nan yake? Yau kwana biyu bai bude shago ba. Idan baya so ne sai na bawa wani ko na bayar haya"

Amarya ta kwabe fuska "dama yaushe zai zo Baba. Bashi da aiki fa sai na shaye shaye tun jiya bai san inda kansa yake ba. Ga amai ya kwara a dakin"

Babanta ya dafe kirji "ince ko ba ke kike gyara wurin ba idan yayi amai"

Tayi kwalkwal da idanu "waye zai gyara idan banyi ba. Yanzu ma itace nake so ya siyo min wani saboda wannan yayi danshi yau da marmarin kunu na tashi. Amma yaki fitowa"
Zinaru sai bude baki take amma ta ma kasa magana don mamakin karyar da Amarya ke gillawa.

Ran Garbebe ya baci sosai. Yadda yake son yarsa shiyasa tana cewa Gidado take so ya amince. Yanzu ga ciki burinsa ta haihu ya sami jika. Ya dallawa Zinaru harara sannan ya fara kwalawa Gidado kira. Mutumin banza haka ya fito daga shi sai wani kodadden wando duk jirwaye.

Garbebe yace "na gaji da wannan rashin kirkin naku. Kaje ka kwashe gwanjonka daga shagona. Ke kuma Zinaru idan jikan ne baki so ki fada ba sai kunyi mata horon yunwa ba. Daga yau bazata kara aikin amai ba don ba baiwarku bace"

Gidado yace "uwar tawa kake fadawa magana haka?"

Zinaru ta kwabe shi cikin harshen fulatanci "kyaleni dasu ka koma daki. Takarda aka kawo daga wurin uwar yaranka nasan bazasu yarda ta kuma zama da kai ba. Amma na sami dillali zan biya shi ya taimaka mu sayar da gidannan ko babu takardu. Ita kuma wannan kazar matsiyatan ka bari mu karbi kudin gidan sai ka saketa itama su karata ita da uban nata. Har yanzu da kyaunka Gidado baza mu rasa 'yar masu kudin da zaka iya aura ba"

Shiru Gidado yayi da yaji zancen saki tsakaninsa da Zulaiha. Yara har shida tsakaninsu dole yaji yana sonta duk irin halinsa kuwa.

Garbebe ya ja hannun Amarya suka yi wajen kofar gidan yace "shegun nan basu san mu fulani bane hala"

Amarya tace "basa yin yaren a gidan shiyasa bana yi musu. Basu san na iya ba"

Garbebe ya tafa hannuwa "karen bana ke maganin zomon bana. Kyaleni dasu ki koma amma ki fara shiri gaskiya aurenku ya kare. Ya ma kika ce sunan baban matarsa ta fari?"

Amarya ta fada masa ya kwashi kafa sai gidan su Zulaiha.
*****

Qasim da Ma'u ke hira a bangaren da ake ajiye motoci tana cewa ya shigo ciki yaci abinci saboda ya kwaso hanya. Innarsu ce tace ta kirashi ma amma yaki amincewa wai gara ta kawo masa nan.

"Kai har ka fini kunya ma"

Qasim yace "haka kike gani ko, nan da wata uku ne zaki gane waye Qasim"

Ma'u tayi dariya "har kasa mana ranar ne?"

"Nan da sati biyu za'a kawo kudi da sa rana. ni dai nace wata biyu za'a saka daga nan sai ki fara shirin komawa Zamfara"

Tayi murmushi "Allah Ya tabbatar mana da alkhairi"

Hayaniya suka ji daga bakin gate karshe dai maigadi yazo ya fada mata wani ke neman Alhaji tace baya nan bari taje ta gani. Qasim ya daure fuska "ina zaune zaki je bakin gate ganin wanda ba'a sani ba. Muje tare dai just incase na gida ne."
Chapter 71 · 0% Book details