← Book details Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 74

Sashe 27

Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga haka suka fita suka bar Uwargida a tsaye ta rasa bakin magana. Sau daya Zubaida ta waigo ta kalleta daga nan tabi sababbin danginta da ta samu sanadiyar kyautatawa Asmau.

*****
Da fitarsu basu zame ko ina ba sai kemis din Sada tare da wanda yace ya santa. Kemis din a rufe yake sai dai sun sami wanda yasan gidansa. Suka dunguma sai gidan Sada.

Umma da Mama ne kan gaba suka shiga da sallama. Rashida suka gani a tsakar gida tana kuka ga Sada yana bata hakuri sai Yaya Tagwai a gefe tana masifa.
"Nayi muku gwaninta na kori wannan annobar shine bazaki dena kuka ba ko Rashida. Allah Kadai Yasan daga ina wannan Asama'un take. Ta zauna ta fada muku karya da gaskiya kun hau kun zauna."

Sada yace "Yaya Tagwai ko tunanin halin da yarinyar nan zata fada bakya yi. Ga ciki ga rashin kudi...."

Umma tayi caraf tace " ba dai kuma kun koreta ba. Wayyo Allah na"
Kawai sai ta fashe da wani kukan mai ban tausayi wanda ya janyo shigowar sauran mazan.

Yaya Tagwai ta kallesu a dakile "ku kuma daga ina?"

Mama tayi mata bayani, Yaya Tagwai ta dubi irin suturarsu tabbas babu tsiya a tare dasu. Ga Umma tana ta kuka ko ba'a fada ba tasan ita ce mahaifiyar Asmau.

Rashida ta tashi tana kuka tana fada musu abinda ya faru da Asmau. Hajjo ta goge hawaye da gefen zani tace "amma wannan tsohuwa baki kyauta mana ba."

Yaya Tagwai tace "haba haba ko makaho yasan kin fini tsufa"

Hajjo taja tsaki "wallahi kinfini tsufa. Ji bakinki fa hakora bazasu fi goma ba"

Sada ya kallesu, ana fama da tashin hankali amma da tsufansu suke fadan shekaru.

Qasim ya harari Yaya Tagwai ta kama bakinta tayi shiru don ya bata tsoro "jiyan da kuka duba babu wanda yace ya ganta?"

Sada yace fada masa ance bus ta shiga. Yayi musu bayanin irib bus din suna zuwa kauyukan gaban Azare har zuwa Jos ne.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽27

Batul Mamman💖

Qasim yayi alkawarin zuwa neman Asmau daga kauyen farko har Jos din. A sanyaye suka koma gidan Sada wadanda suke ganin sun zame musu 'yan uwa sakamakon kyautatawar da suka yiwa Asmau. Duka kayanta Rashida ta hada musu harda na jariran. Umma dai tasha kuka har ta gode Allah. Su Anti Binta, Shema'u da 'ya'yan Mama su Suwaiba duk sunyi ta kira su ji yaya ake ciki.

Da zasu tafi har bakin mota Rashida da Sada suka yi musu rakiya aka karbi numbar wayar juna.

Qasim ya cika alkawari wurin binciken Asmau sai dai babu wani abin arziki da ya samu duk da haka bai hakura ba. Duk inda yaji alamar anga mace da ta bata sai ya duba ko za'a dace.
*****

Humaira babbar 'yar Zulaiha ke zaune gaban Asmau tana jira ta gama sakawa Amatullah kaya a goya mata ita. Zulaiha tace "Asmau kada ki goya mata ita kin santa da rawar kai. Tsorona daya kada garin rashin nutsuwa su fadi shiyasa idan tace na goya mata nake hanawa".

"Umma da gaske zan nutsu bazan yar da ita ba. Ni da har girki nake yi miki amma sai ki hana ni goyo".

Asmau ta dauko zani cikin wanda Zulaiha ta bata "tashi kinji babbar Yaya na goya miki ita. Ai nasan ko bakin kofar gidan bazaki je ba a nan zaku zauna"

Duk yadda Zulaiha taso hanawa haka akayi goyon Humaira ta fita tsakar gida tana murmushin jindadi. Asmau ta sauke ajiyar zuciya. Watansu uku a gidan nan lokaci yayi da ya kamata ta fara neman aikin yi ko don ta ragewa Zulaiha nauyi. Ga Zinaru kullum tayi zancen kudin haya sai Zulaiha tace mijin Asmau ne ba'a samunsa ko da a waya. Gori kala kala take sha akan abincin da suke bata wanda ba danta ke nema ba. Gyara zama tayi yadda zata rinka hango Humaira da kyau sannan tace da Zulaiha
"Nasan kina kokari sosai tun zuwana Allah Kadai zai baki lada. Amma ya kamata na nemi aiki. Saboda Amatullah dai nasan babu gidan da zasu daukeni kuma gashi bani da wata takardar makaranta. Shine nayi tunanin ko zan sami irin naki sai nayi".

Zulaiha ta katse ta "haba Asmau, yarinyar nan har nawa take da zaki fara neman aiki? Ki bari ta kara kwari. Ni zamanmu dake duk wahalar da zan sha ban dauketa komai ba. Na dade ina rayuwar kunci da rashin makusanci kafin zuwanki."

"Duk da haka gara nayi aikin ko don na taimaka miki. Ki duba fa tunda nazo su Muhsin basu taba zuwa makaranta ba saboda rashin kudi."

Zulaiha tasan gaskiya Asmau ke fada sai dai kuma tana tunanin kankantar Amatullah. Shawara suka yanke washegari da taje aiki ta sami makociyarsu wadda tayi mata hanya. Da taimakon matar nan Allah Yasa Asmau ta sami aikin itama.

Yanayin aikin nasu da wuya suje tare. Juya musu akeyi idan wasu suka yi na safe wasu sai suyi da yamma. Hakan yayi musu dadi kodayaushe akwai mai zama da yaran a gida.

Asmau sai ta goya Amatullah ta tafi aikinta tunda bata isa a fara barinta a gida ba. Da yake yarinyar akwai dariya ga dan jiki sai tayi saurin shiga ran sauran ma'aikatan. Idan Asmau zata wanke bandaki sai a rike mata ita taje tayi aikin. Tunda ita mace ce mai ilimi sai ya zamto tafi sauran mayar da hankali wurin tsaftace duk inda ta gyara. Albashinta na farko kaya ta siyawa Amatullah har kala biyar da Ali autan Zulaiha. Sauran kudin kuwa kayan abinci ta siyo musu. Zulaiha sai godiya take yi mata har tayi mamaki ita da ake ta dawainiya da ita.

Zamansu haka yayi ta tafiya cikin lumana da taimakon juna. A hankali likitoci da dama suka san Asmau saboda tsaftarta zance har wajen Chief Medical Director (shugaban asibiti). Da yaji yadda ake yabonta da son cigabanta tunda har turanci ta iya sosai ya canja mata aiki daga shara zuwa bada kati. Ba karamar murna sukayi ba saboda albashi ya karu. Ko kadan babu hassada tsakaninta da Zulaiha. Karshe ma aka mayar da ita bangaren bada sakamako idan anyiwa mutum gwaji a asibitin. Dan ihsani kuwa daga nurses da likitoci tana samu sosai a dalilin Amatullah.

Bata da wata matsala a lokacin sai Gidado da Zinaru. Daga ita har Zulaiha basa jindadin zama dasu. Kudin hayar daki kuwa taki bawa Zinaru a hannunta kamar yadda take ta naci. Su Humaira aka mayar makaranta. Shi kuma Gidado baya shakka ko a gaban Zulaiha baya iya boye son da yake yiwa Asmau. Ya sha nemanta sai dai taki bashi hadin kai kuma kullum haka ta faru sai ta fadawa Zulaiha don gudun matsala. Tayi ta yiwa Zulaiha nasihar rabuwa dashi sai dai tayi murmushi kawai. Wannan ya tabbatar mata da cewa har yanzu Zulaiha na son mijinta. Sai ta kyaleta suka cigaba da zamansu.

*****
Annur yana kwance a daki bayan ya dawo daga makaranta yana dan danna wayarsa aka turo masa wani text da hoto. Da farko baiyi niyar bude hoton ba sai da ya karanta labarin yarinyar a matsayin wadda mijinta ya rasu ranar aure kuma aka gane tana da ciki. Tsaki yayi sannan ya bude hoton don shi da Gaddafi yanzu karatu suka saka a gaba.

Matar ya gani kyakkyawa da ita har ya ajiye wayar sai ya sake daukowa ya duba hoton. Hannunsa na rawa ya turawa Gaddafi yace ya duba ko ya gane ta. Ba jimawa Gaddafi ya kira yace sai ya ga kamar matar nan mai ciki da suka taimakawa mai suna Asmau. Matar da suka je nema a asibiti basu sameta ba.

Tausayinta suka ji musamman da suka tuna halin da suka tsinceta da irin nasiharta garesu. A cikin sati daya suka yi ta bincike da tambaya ko akwai wanda ya santa har suka dace da samun wani dan makarantarsu da yace a unguwarsu abin ya faru a Kano. Yaron har gidan Umma ya kaisu suka sanar da ita labarin haduwarsu dai Asmau. A wannan ranar an sha kuka sannan Umma tace ita ta hakura zata cigaba da yi mata addua. A duk inda take Allah Ya tsareta kuma Yasa ta dawo gida da kafarta.

*BAYAN SHEKARA BIYAR*

Idan kaga Asmau bazaka ce itace tazo garin Jos a rame da tsohon ciki ba. Duk da bata da jiki kamar da amma ta dan samu nutsuwa. Ita da Zulaiha kuwa ko 'yan biyu bazasu nuna musu kusanci ba. Tana tuka tuwo Zulaiha na tsinke zogale taji sallamar Amatullah da Aliyu.

Da gudu Amatullah tazo ta rungumeta ta baya
"Ummina tuwo kike yi?"

Asmau ta bata rai "Ama so kike na kone zaki fado min haka. Me ya dawo daku yanzu bayan ba'a tashi ba?"

Zulaiha tayi dariya "tunda kika ji ta kiraki da _Ummina_ kema kinsan akwai abinda take so".

Amatullah ta kama kasan dan hijab dinta tana wasa dashi, Zulaiha ta dubi Ali "kai da kayi mata rakiya sai ka fadi me ya dawo daku ai"

Ya ja baya da sauri "Umma nifa fitsari tace zata yi na rako ta".

Asmau ta nuna hanyar bandaki "wuce kiyi kizo ku koma".

Sum-sum Amatullah ta wuce bata dade ba ta dawo ta sake tsayawa a bayan Asmau. Zulaiha ta kula akwai abinda take so ta janyota jikinta
"Amatullah ta Ummi me kike so ne, fada min naji"

Dan turo baki tayi wanda duk lokacin da tayi sai Asmau ta ga kamarta da babanta ta fito sosai Nabila ce take shan kafi kaza kuma Ummi ta hanamu roko shine nazo ta bani biyay na siyo".

Zulaiha ta kwashe da dariya "bakinki ne biyay din ai"

Amatullah ta dan buga kafa "Umma biyay nace fa ba biyay ba".

Wannan karon Asmau ma tayi dariya. Amatullah bata iya fadan duk kalma ma harafin *r*, idan ka fada yadda tayi kuma tace sam ba haka ba.

Zulaiha ce ta basu naira biyar biyar ita da Ali suka tafi. Asmau tace
" da baki basu ba. Sun baro makaranta takanas saboda kwadayi. Yanzu gobe idan taga wani abin sake dawowa zatayi."

"Na sani, rokon ne bana so tayi. Idan suka dawo sai a kwabesu akan hakan. Amma da ban bayar ba karshenta nan gaba bazamu sani ba sai da su roka a makarantar.
Chapter 27 · 0% Book details