← Book details Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 74

Sashe 32

Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jafar da Sabira suka fito dauke da kayan abincin tare da Asmau dake binsu a baya rike da hannun Amatullah. Zaune yake a gaba ya kwantar da kansa a saman kujera yana sauraron karatun Al'Qur'ani kira'ar Shiek Mishary Rashid. Tausayinsa Asmau taji saboda kunyar abinda tayi masa. Babban mutum kamarsa sun shanya shi a kofar gida. Kuma ta tabbatar baici abinci ba kafin su taho. Yana dawowa daga masallaci ko zama baiyi ba yace su taho kawai.

Amatullah ta tafi da gudu ta fada jikinsa. Hakan yasa shi saurin bude ido yana murmushi. Jafar ya karasa gaban motar ya mika masa hannu suka gaisa.

"Kayi hakuri don Allah an barka a waje tun dazu. Duk laifin Idon kuka ne da bata fada mana tare kuke ba"

Col. Ishaq yace "Idon kuka kuma?"

Dariya Jafar yayi kana ganinsa kasan yana cikin farinciki, ya nuna Asmau "ai sunanta kenan."

Kyakkyawan murmushi Col. Ishaq yayi yana kada kai "sunan ya dace da ita"

Duk akayi dariya sannan Jafar ya fada masa yana son ya biyo shi gidansa domin yaci abinci. Da farko Ishaq ya nuna baya jin yunwa sai da Asmau ta bashi hakuri tare da rokonsa. Yayi yar dariya

"Haba Idon kuka, bayan ko introducing dina a wurin yayanki baki ba?"

Asmau ta sunkuyar da kanta tana murmushi. Jafar ya sake mika masa hannu murmushinsa yana kara fadada "nima da laifina, sunana Jafar ni Asmau take bi,wannan matata ce Sabira. Idan kaci abinci zamu shiga ciki ka gaisa da duk 'yan uwa."

Col. Ishaq ya dafa kan Amatullah "ni kuma sunana Baban Safina"

Sabira ta kalli Asmau "kice kawai biki zamu sha kwanan nan"

Da sauri Asmau ta daga hannuwa "ba haka bane, Ama ce kawai take kiransa babanta. Sunansa...."

Shiru tayi duk suka zuba mata ido. Kunya taji ta kasa fadin sunan sai ta wayance tace ya kamata su tafi saboda kada abincin ya huce. Col. Ishaq ya nuna su shiga motarsa.

Jafar ya shiga gaba, Sabira na baya sai Amatullah da ta dage zata bi babanta. Asmau tana tsaye suka ja mota suka tafi ta koma ciki.

Hira aka dora daga inda aka tsaya. Shema'u tana goye da Abid din Sabira sai jijjiga shi take kafin Sabirar ta dawo.
*****

Mata kamar kara turo su akeyi gidan ana ta zuwa kallon Asmau. Hajjo duk ta matsu su firfita don su samu ayi hira yadda ya kamata da Asmau. Duk dakin da ta shiga mata ne harda wadanda ma basu zo ba da farko. Su Umma ma dai kara kawai suke yi amma duk a matse suke da a basu fili suyi hira da 'yarsu. Da suka ga abu yaki karewa Hajjo da kanta ta shiga falo rai a bace tana mita yadda masu hankali zasu fahimta
"Kai jama'a ace anzo taron suna anci tatsotse dinnan anci salak, anci tuwo anci wannan anci wancan amma mata sai tururuwa suke yi. Fisabilillahi ko irin karar nan ta a fita a bamu waje da jikarmu muyi hirar yaushe gamo ya gagara".

Wasu nan suka fara jin kunya suka fara hada kayansu suna fita. Sauran da suka yi biris kuwa Hajjo ta rufe idonta ta sallamesu. Umma da Mama dai sunji kunya to amma halinmu na mata wurin saka ido da bin kwaf ya janyo musu.

Basu samu gidan yayi daidai ba sai bayan karfe tara. A falo suka zazzauna. Duk 'yan uwan Asmau makusanta suna wurin har da Kawu Garzali ga kuma Haj Lubabatu da danta. A nan aka shiga bada labarin abubuwan da suka gabata. Kowa jikinsa yayi sanyi musamman da suka ga Asmau tana ta kuka da rokon a yafe mata. Suka yi ta kukan wannan kaddara da ta riga fata.

Mama Yalwa tace "ai wannan bala'i na waya sai an dage da addua sosai. Akwai alkhairi tattare da ita amma sharrinta a bayyane yake. Kuma kullum kara samar da sabuwa akeyi mai saurin hada mutane da barna."

"Haka ne" Haj Lubabatu ta amsa mata. " Sai kiga yara kanana sun yini da waya a hannu ki rasa me suke tattaunawa. Wani lokacin a haka ake haduwa da mutane babu sanayya idan kika yi rashin sa'a ba nagari bane sai su bata maka tarbiya ba tare da ka lura ba. Kwanakin baya jikata dake karatu a nan wurina Bilkisu na fuskanci ta soma nacewa waya fiye da yadda ta saba. Kullum suna hira da wata yarinya da suka hadu a irin group dinnan na waya. Kunsan yanzu tsakanin mace da mace ko maza ma babu abinda ba'ayi. Na kula kawancen ya soma yawa bata da zance sai nata. Abun ya fara bani tsoro. Shabiyun dare sai kiji suna waya sai da nayi mata tas akan hakan."

Hajjo tace "ni idan babu hali ba sai a hakura da wayar ba. An fara abu da gaisuwa da sada zumunci a hankali waya ta zama tamkar kana dauke da duniya a tafin hannu. Idan kaki bawa danka waya ma zai fita ya gani a ta wasu."

Tattaunawa suka yi ta yi a game da tasirin waya ga al'umma yanzu. Babu babba babu yaro kowa yana da ita kuma ya iya amfani da ita. Jankunne sosai manyan suka yi garesu akan su dubi yadda rayuwar Asmau ta kasance su kula da kawunansu da na yaransu. Kasancewarsu masu aure duk bashi bane domin yanzu hatta mata da mazan aure suna fadawa tarkon waya. Daga group sai kaga matar aure tana mu'amala da 'yar uwarta mace ko namiji mai aure ko mara shi wanda a da ba halinta bane.

Sun jima suna hira har shadayan dare tayi basu kula ba sannan Haj Lubabatu da Col. Ishaq suka tashi tafiya. Sun sha godiya a wajen dangin Asmau sosai tare da neman a cigaba da zumunci don yanzu sun zama daya.

Fitowa suka yi har bakin mota rakiya Amatullah na makale jikin Col. Ishaq tana bacci. Tashin da yayi zasu fito yasa ta farka ta soma rigimar binsa. Shi kan shi baya son rabuwa da ita. Ana ta lallabata taki yin shiru sai da Asmau ta karbeta ta karfi tana mata fada. Hakura tayi amma bata dena kukan ba. Col. Ishaq ya bata rai sosai saboda fadan da tayiwa Amatullah. Kallon da yake mata ya nuna rashin jindadinsa sai kawai ta sunkuyar da kanta.

Bayan tafiyarsu Umar ya tafi kai Mama Yalwa gida shi kuma Abdulhalim ya dauki matarsa da yara suka wuce. Dakin Umma suka koma Amatullah tana ta kuka har sai da Asmau ta goyata duk girmanta don taki yarda da kowa. Daga nan aka soma wata sabuwar hirar har aka zo kan Kawu Rabe Asmau tace shi kadai ne bata gani ba . Shema'u tace "hmmm Asmau mutum babu kyau. Ashe duk tsahon lokacin nan Kawu Rabe wurin wani malami yake zuwa ana rufe bakin Hajjo da su Yaya Abu. Bayan tafiyarki Hajjo tazo ta nemi gafarar Umma har ta bukaci lallai ta dawo gidannan dasu Aina'u idan har ta yafe mata. Shi kuma tace ya soma gyara musu gidan kofar mazugal su koma. A nan aka ji ashe ya dade da siyar da gidan. Ya kuma dage wannan nasa ne. Sai ga ainihin takardun gida Hajjo ta fito dasu, ke magana har za'a shiga kotu don duk su Kawu Garzali sun ce sai ya biyasu kudin gidansu da ya sayar. Wurin aikinsu ma suka kore shi yaci kudin kamfani bai biya ba. Sai da yaga abu ya kure masa ya roki gafarar Umma suka tashi. Yanzu haka yana kauyen Dakasoye can ainihin kauyen babansu Anti Sagira. A nan baban nata ya bashi gona da gida suka zauna tunda bashi da wurin zama. Yanzu da wuya yazo cikin Kano. Zahra dai tayi aure tana Jigawa"

Asmau tace "har ya bani tausayi. Da ma Umma ta barshu kawai a nan din"

Aina'u tace "tabdi, ko yanzu fa ba wani rissina yayi ba. Tsoron hukuma yaji don da gaske su Yaya Abu sunso a kama shi sai ya biyasu kudin shiyasa ya bada hakuri ya tattara yayi gaba"

"To Allah Ya kyauta" duk suka ce Amin.

Kan katon gadon Umma suka kwanta su uku sannan aka shimfide yaran akan bargunan banda baby Asmau wadda suke kira Husna.

Sai wurin daya da rabi na dare Umma ta baro dakin Hajjo inda su Anti Lami suke. Su ma sum gama tasu hirar. Wani hawaye taji yazo mata da taga 'ya'yanta mata kwance su uku a wuri daya sun takure alamun daya gefen nata ne. Kasa kuma ga yaransu duk sunyi bacci. Maimakon ta kwanta alwala ta dauro tazo tayi sallah tana mai mika godiyarta ga Allah tare da adduar dadin shiriya ga zuri'arta da sauran musulmi.
*****

Col. Ishaq yana kwance amma ya kasa bacci. Ya rasa abinda yasa yake ta tunanin Asmau. Can kasan zuciyarsa yace tausayinta ne kawai da kuma son Amatullah. Sai dai kuma ko rufe ido yayi murmushin da tayi bayan komawarta gida yake tunawa sai kawai ya tsinci kansa da yin murmushin shima.
*****

Washegari karfe takwas na safe sai ga Jafar da Sabira dauke da kwanunkan abinci. Dankali ta suya da plantain da kwai. Duk da tasan dai a gidan ma za'ayi. Umma ta nuna jindadinta sosai. Shiyasa take son Sabira, barta dai da surutu amma mace ce mai ladabi da sanin ya kamata. Sauran matan masu jini a jika irin su Shemau da Rashida suna kitchen ana ta soye soye. Aina'u ma ta tashi duk da hanata aikin komai ita da Zubaida mai ciki. Asmau kuwa kamar wadda aka saukarwa bacci tana yin sallar asuba ta koma. Ji takeyi rabonta da bacci mai dadi cikim kwanciyar hankali har ta manta.

Amatullah ce ta tasheta tana kiran Babanta. Cikin bacci Asmau ta janyota jikinta ta soma rarrashi
"Ama nan ne gidanmu fa, na rasa inda kika koyi rigima. Amma idan kika cigaba zan mayar dake wurin Zinaru"

Shiru tayi ta kwanta a jikin Asmau daga baya tace "Ummi to zaki kaini naga Babana sai mu dawo?"

Asmau ta shafa kanta tana murmushi "in sha Allah zan kaiki kinji. Tashi muje muyi brush a gaishe da su Hajjo"
Chapter 32 · 0% Book details