← Book details Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 74

Sashe 33

Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna fitowa falo suka tarar da kowa a zaune har su Jafar. Rike take da hannun Amatullah sai suka basu sha'awa. Ita kuwa kallon da suke mata yasa taji kunya ta saki hannunta. Yanzu tunda anzi gida sai ta koyi kara kada ace bata da kunya. Suna zama suka gaishe da kowa Anti Bintu ta cikawa kowannensu plate da abinci. Amatullah ta ware ido sai ta tashi taje tayiwa Asmau rada a kunne. Duk ana kallonta sai suka ga tana share hawaye. Hankalinsu ya tashi Umma tace me ya faru.

Kunya tasa Asmau ta kasa fada da wayo Umma tace "Safina zo ki fada min abinda kika fadawa Ummi. Kinga gashi har kin sakata kuka"

Duk aka zuba mata ido ita kuwa tace "Ummi in fada?"

Murmushi kawai Asmau tayi tace "tambayata tayi taci ko kuwa"

Amatullah ta cafe "idan naci Ummi zata ce nayi kwadayi. A gidan Babana ma sai tace naci. Mu a gidan Zinayu koko da kosai muke ci, ko byodi da tea, ko tuwon safe ko Ummi"

Kasa cin abincin Asmau tayi ta fashe da kuka. Sunga rayuwa ita da Amatullah. Dan kudin da take samu a kudin makaranta yake tafiya. Abinci kuwa sai dai aci garau garau. Su Umma suma kukan suke tayata. Abinda tafi karfi a da shine yanzu yafi karfinta. Anti Bintu tazo ta rungumeta "komai ya wuce Asmau. Kuka bazai dauke shekarun baya ba sai dai ya tuna miki da bacin rai."

Hajjo tace "haka ne ki dena kukan haka. Rayuwace kowa da irin tasa duk da dai komai yana da sanadi. Naji dadi da kika koyawa yarinyar nan tarbiya mai kyau."

A haka suka ci abincin ana taba 'yar hira har Asmau ta sake. Kafin su tashi Amatullah ta sake cewa "Ummi daga yau a nan zamu zauna ne?"

"Eh mana ai kun dawo gida kenan" inji Shemau

Tare duk suka tashi aka kwashe kwanukan suka fara layin wanka.

Wurin shadayan safe Asmau na saka kaya don kuwa Mama Yalwa tace yau a gidanta zasu yini taji wayarta na ringing. Ko da ta dauka bakuwar number ta gani har tayi zaton ko Zulaiha ce tace "tuba nake maman 'yan biyu ban samu na kiraki ba"

Shiru taji daga daya bangaren tace "Zulaiha ko kinyi fushi ne. Ni da ke fa ba'a ji kanmu ba"

"Ashe kin iya hira Idon kuka" ji tayi gabanta ya fadi. Muryar da ko cikin bacci yanzu tasan zata gane taji. Kamar yana gabanta ta dan russuna a kunyace ta gaishe shi.

"Har kin gane mai magana, ko kuwa dai wayancewa kika yi?"

Tana murmushi tace "Na gane"

Col. Ishaq ya gyara kwanciyarsa. Shi bai ma san dalilin da yasa yayi mata waya da safe haka ba.
"To waye?"

"Baban Amatullah"

"Uhmm uhmm, a wurinta kadai nake baba. It seems ko sunana baki sani ba. Shiyasa jiya kika kasa fadawa yayanki"

Asmau taji muryarsa kamar baiji dadin hakan ba tace "na sani kuma na fada masa ma"

Magana yake kamar maganar aiki ce mai zaman kanta yace "me kika ce masa? I am sure ba Baban Safina kika ce ba".

Ita fa kunyarsa take ji. Ganinsa take yi babban mutum mai matukar kwarjini da cika ido shiyasa bata tsawaita hira dashi. Sake maimaita tambayar yayi tace "Col I. M Jikamshi"

Wani iri yaji yadda ta fadi sunan a hankali kamar bata so yaji.
"I. M Jikamshi yana rokon alfarmar ayi saving din numbarsa saboda kada ki sake kirana Zulaiha. By the way ina princess dina?

"Ana yi mata wanka"

"To zan sake kira anjima ki hadani da ita. Ina fata kinji request dina. Idan kika sake kirana da sunan mata zamu kulleki ni da Safina. Ki gaida da Umma."

Amsa masa tayi da to...tana 'yar dariya ta ajiye wayar.

Mimi babbar 'yar Shemau ce ta shigo tana kiranta Umma tace tazo falo. Hijab ta saka ta fito daidai lokacin da Qasim ya dago kansa. Suna hada ido nata ya ciko da hawaye shi kuma nasa suka yi ja sosai.

Ya kura mata ido yana kallonta "Asmau ke ce?"

Ta fashe da kuka tana kallonsa tana tuna wasu lokuta a da. Yayi dan jiki kamar bashi ba. A da Abubakar ya fushi kumari. Gashi duk ya canja alamun yana da sukuni.

Kusa da Umma ta zauna a kasa ta gaishe shi tana dan murmushi ga hawaye
"Yaya Qasim ai bazan ganeka ba"

Yau da Asmau namiji ce babu abinda zai hanashi rungumeta don ya nuna mata tsantsar farincikinsa da ya ganta. Jiya da ta tsaya a Shanono su Inna suka ce dare yayi ya bari gari ya waye ya karaso Kano ji yayi inama bai biya ya sanar dasu ba. Yau dai burinsa ya cika Asmy din Abubakar ta dawo gaban iyayenta.

Amatullah ce ta shigo falon tana kira Asmau. Duk da ta sake da mutanen gidan amma haka halinta yake da an dan jima sai ta nemi Umminta. Tana ganinta kuwa zata kama wata sabgar.

Gaban Qasim har faduwa yayi da ya ganta. Baya bukatar wani karin bayani ya tabbatar wannan 'yarsu ce wadda rabon haihuwarta ya jefa iyayenta da su kansu cikin rudani. Tashi yayi ya durkusa a gabanta yana shafa fuskarta, muryarsa na dan rawa yace "yaya sunanki"?

Tayi masa murmushi irin wanda yake tunawa Asmau da Abubakar idan tayi shi "Safinatu Amatullah Abubakay"

Rungumeta yayi kawai hawayen farinciki na fito masa. Muddin yana raye yayi alkawarin kula da ita har karshen rayuwarta. Yana shafa kanta yace
"Safinatu nine babanki"

Ta dago kanta tana kallon Asmau "Ummi ni babana biyu ne"?
ABINDA AKE GUDU🙆🏽37

Batul Mamman💖

Tana gama wayar Ainau ta tambayeta ko waye tace baban Amatullah ne. Ainau ta kurawa 'yar uwarta ido
"Yaya Asmau zaki iya yin sati a garin nan kuwa ko kawai mu bi Yaya Yassar mu koma Kano"

"Kada ki damu Ainau, irin wannan abubuwan nasan ban fara ganin komai ba ma. Idan ya faru ne yake taba min zuciya na dan lokaci har nayi kuka. Dama abinda ake gudu kenan, ba wai yin a lokaci daya ba, abinda zai je ya dawo bayan kayi. Kinga rana daya a rayuwata ta canja akalar komai nawa." Kuka suke yi duk su biyun Ainau tana bata hakuri
"Ku zan bawa hakuri ma da na janyo ake yiwa tarbiyar da Umma ta bamu kallon gazawa. Don Allah kada ku bari taji wannan labarin. Shima Yassar din zanyi masa magana"

Anti Bintu tana bakin kofar tana jinsu. Tausayin Asmau ta kara ji ta koma wurin maigidanta. Alfarmar kada su fadawa Yayarta tazo nema sai gashi Asmau tayi wannan tunanin.

Sun dauki lokaci a dakin suna magana kafin su dawo falo bisa umarnin Kawu Yusuf. Rokonsu yayi da suyi hakuri da halin tsufa irin na mahaifiyarsa kuma yana fata zasu sake a gidan bazasu takura kansu a daki ba.

Sai da suka yi sallah aka zauna cin abinci. Babu wata hirar kirki sai hayaniyar Amatullah. Kowa jikinsa a sanyaye yake. Ganin haka Asmau ta rinka dauko hira duk don ta nuna musu bata tare da damuwa.

Su Yassar sun dawo daga masallaci inda suka yi sallar la'asar yace zai kama hanyar komawa. Anti Bintu ta tsayar dashi ya jira a kawo sako da take son ya tafiwa da Umma dashi. Yana zaune a falon Col. Ishaq yayi masa waya yana tambayarsa kwatancen gidan da suke zai zo ganin Amatullah.

Yassar ya tashi tsaye cike da mamaki, sannan ya kwatanta masa inda zaije ya jirashi sai yazo ya kawo shi gidan. Anti Bintu ta tambayeshi ko lafiya ya sanar da ita bakon da zasuyi. Murmushi tayi "anya 'yar yazo gani ko uwar 'yar"

"Nima tunanin da nake yi kenan Anti. Mutumin ba karamin burgeni yake yi ba. Idan yace yana son Yaya Asmau ai ya gama min komai. Wallahi binsa zan rinka yi sau da kafa".

"To sarkin zumudi, daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaki" Anti Bintu ta fada amma itama tana fatan hakan ya tabbata. Dan ganin da tayi masa ranar da suka dawo da Asmau ta yaba dashi.

"Bari kiga naje bakin layin kada yazo yayi ta jirana"

"Ita yayar taku tasan da zuwansa?"

"Kai bana jin ta sani, kyaleta kawai Anti kada ta bata lamarin. Ba karamin aikinta bane ta tura masa Amatullah taki zuwa su gaisa. Kuma ai kinga bai dace ba mutum yayi tafiya irin wannan saboda danka"

Wannan karon dariya sosai ya bawa Anti Bintu. Lallai Yassar da yana da iko tuni zai bawa sojan nan auren yayarsa. Yana fita ta shiga ciki suna daki ana ta wanka saboda zafin gari. Ta tarar Asmau ta shirya cikin wata doguwar riga mara nauyi shudiya ta yafa karamin mayafi fari a kanta. Anti Bintu tace ta taso ta tayata hadawa bako abinci don duk 'yan matan gidan suna Islamiyya.

Tashi tayi tabi bayanta ta bar Ainau da yaran. Da yake akwai sauran abincin rana salad kawai ta sake hadawa ita kuma Anti Bintu ta hada zobo mai sanyi.

Tray din abincin ta dauka ta shiga falo, ko tsakiyarsa bata kai ba taji sallamar Yassar da ta Jikamshi. Sai dai murya ta biyun ce tafi daukar hankalinta har ta daga kai suka hada ido. Sanye yake cikin kayan aikinsa da hularsa rike a hannu. Yayi kyau sosai. _Innalillahi wa inna ilaihi rajiun_ ta fada saboda tsabar kaduwar da tayi hannuwanta suna rawa tana neman sakin tray din a kasa.

Wani irin kallo ya bita dashi yana wani kashe ido. Sai kuma ya karasa gabanta ya karbi tray din da yake tangal-tangal ta kasa rike shi da kyau. Sai da ya ajiye shi a kan centre table din falon ya sake dagowa yana kallonta kamar wadda aka kafe a wurin yace
"Duk murnar ganina ce haka tasa kika kasa motsi?"

Juyawa tayi bayanta taga Anti Bintu tana murmushi,daga bakin kofa kuwa Yassar ne bakinsa ya kusa zuwa keya don dadi. Ji tayi kamar ta make shi.

Mamakin ganinsa ta yi sosai har ta kasa hada wata kalma a bakinta. Shi kuwa ba karamin dadi yaji ba da ya ganta.
"Kinyi tunanin wasa nake yi da nace zan zo? Gashi ko wurin zama baki bani ba sai aikin daukar miki tray daga shigowata"
Chapter 33 · 0% Book details