← Book details Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 74

Sashe 29

Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga cikin dakin Zinaru ke cewa Gidado "dole ne ka rabu da Zulaiha hakan ne kawai zai sa Asamau ta bar gidan nan. Zulaiha ma da dabara zaka saketa yadda zamu tsira da gidan nan. Ka santa da son 'ya'ya sai ka ce mata ka saketa amma tare da yaran zamu tafi. Nasan idan taji haka zata bar maka gidan ita ta fita. Kande ta riga ta samo mana 'yar wani kusa a gwamnati da zaka yi auren jari da ita."

Gidado cikin muryar wanda giya bata gama sakinsa ba yace "amma Zinaru idan muka yi haka kamar bamu kyautawa Zulaiha ba. Kuma Asmaun nan na fada miki ita ma sonta nake yi."

"Sakarai mara lissafi, Asama'un me. Ana maka zancen 'yar masu kudi. Yanzu dai ko da safe ne sai kayi yadda nace."

Asmau ta jinjina bakin hali irin na Zinaru. Gashi Zulaiha laulayi take yi babu wanda ya sani sai ita. Har kuka tayi saboda bata son cigaba da haihuwa ga talauci da rashin gata. Sauri tayi taje dakin Zubaida ta fada mata abinda taji sai tayi tuntube da kwaftareren takalmin Gidado. Zinaru ta fito da sauri taga ko waye suka hada ido da Asmau. Ta dan ji tsoro da farko sai kuma ta dake ta soma kwalawa Zulaiha kira.

Cikin bacci taji kiran da Zinaru ke yi mata ta fito tana murza ido. Zinaru tace "munyi magana ne da Gidado akan yadda Asamau ta raina ni da irin rashin jituwar dake tsakaninmu shine yace zai koreta. Ni kuma sai na tuna masa cewa gidan nan ba namu bane. To yanzu yake fada min wai ko dai ki sallameta da kanki ko kuma ya sakeki mu tafi mu bar miki gidan."

Zulaiha ta rude "me yayi zafi Gidado har da zancen saki? Zinaru ki bashi baki don Allah."

Asmau tace "wallahi karya take yi Zulaiha. So take ya sakeki ki bar musu gidan".

Zinaru ta kalli Gidado
"Ince dai kaga irin yadda take yi min. Ni bazan zauna a gidan nan ana wulakanta ni ba".

"Zinaru kiyi hakuri indai Zulaiha ce yanzu zan saketa mu tafi"

Yaransu duk suna kallo ita Asmau har ta soma jindadi sai kawai Zulaiha ta durkusa a kasa ta rike masa kafa tana kuka"ka rufa min asiri Gidado kada ka sakeni. Ina zani da yaran nan."

Muhsin ya dagata tsaye "Umma kawai ki bari ya sakeki kema kya huta da duka da wankin amai. Dama don ke kike yi ne nake tayaki amma daga yau sai muga mai wanke masa"

Bakin Muhsin din ta daka "waye ya saka bakinka. Ku bar wurin nan kafin na bata muku rai."

Suna tafiya ta cigaba da rokonsu shi da babarsa. Zinaru ma tasa kukan karya ita dole su bar gidan. Ganin haka Asmau tace "indai saboda ni ne to in sha Allah da safe zan tafi. Zulaiha ki tuna da gatan da Allah Yayi miki ki koma gaban iyayenki. Gobe nima gidanmu zan tafi na roki nawa iyayen gafara".

Daga haka ta bar wurin. Wannan wane irin so ne Zulaiha ke yiwa Gidado. Tausayi take bata don wannan ba karamar jarabawa bace. Mutum ya mayar da kai bolarsa amma ka kasa rabuwa dashi.

Da kuka Zulaiha ta biyo bayan Asmau."kiyi hakuri Asmau ki zauna gobe zan sake rokonsu."

"Zulaiha a kaina bazan so kiyi ta zubar da mutumcinki a gaban su Humaira ba. Ni dai shawarata ki koma gida ki roki gafarar su Inna".

Zulaiha tayi shiru. A yadda zuciyarta ta karaya bata jin zata iya zuwa gaban iyayen da ta yiwa rashin kunya harda kaisu kara.
*****

Karfe goma na safe Asmau ta gama hada 'yan kayanta da na Amatullah. Tayi mata wanka suka shirya tafiya. Daga kan Humaira har Ali kuka suke yi basa son tafiyarta. Itama kukan take yi amma gara ta koma gida. Kewar iyayenta ta dameta gashi duk inda ta zauna sai wani dalili ya koreta.

Kamar bazasu rabu ba ita da Zulaiha kowa kuka ta rike hannun Amatullah suka fita.

Tasha suka je bata dade ba motar Kano ta cika suka fito. Sunyi tafiya mai dan nisa sun wuce wani gari Saminaka ba jimawa suka ga wani mutum yana daga hannu alamar neman taimako. Gefensa mace ce babba da dogon hijab sai wata 'yar budurwa da bazata kai shekara ashirin ba. Dreban farko kamar kada ya tsaya sai kuma yaji tausayin dattijuwar suka tsaya. Motarsu ce ta lalace ga makanike yana dubawa amma yace injin ya buga sai an sauke shi. Su Asmau suka marmatsa matar da yarinyar suka shigo. Aka bar dreban da makanike.

Sallama tayi musu suka gaisa tare da yi musu godiya.

Ta kalli Amatullah da ke zaune a cinyar Asmau tayi mata murmushi.
"Yan mata yaya sunanki"

"Safinatu Abubakay. Amma Ummina Amatullah take ce min ko Ummi"

Asmau tayi dan murmushi kawai. Fargabar zuwa gida ce fal a zuciyarta. Ita kuwa dattijuwar tace "Safinatu Abubakay ko Abubakar" tana yar dariya.

Amatullah tace "Abubakay nace ba Abubakay ba"

Mutane da yawa a motar sai dariya. Can ta dan taba matar nan "kema aljannah zaki je? Ni da Ummi can zamu wurin Babana. Ban taba ganinsa ba, Zinayu zai zane saboda tana duka na."

Asmau ta dan kai mata duka saboda suruta sannan ta share hawaye. Matar nan tana kallonsu sai taji tausayinta ya kamata. A hankali yadda Asmau zata ji tace "Allah Ya jikansa"

Asmau ta dago kai tace "Amin" wani hawayen yana fita a idonta.

Sun iso Kano garin da hadari ga kura. Tana kokari daukar kayansu ne ta ga Amatullah ta dafe kirji numfashi baya sauka. A gigice ta saki jakar ta rungumota tana kuka. Yau kam ta tabbatar asthma gareta saboda yadda take kokarin numfashi yaki sauka.

Wannan matar da wasu maza suka taho wurinta. Dreban da yazo daukar matar yana zuwa tace Asmau ta tashi su tafi asibiti. Kuka take yi kawai ga Amatullah ta sandare.

Wani asibitin kudi suka je aka karbi Amatullah. Tana ji matar tana waya tana sanar da wani inda suke.

Bayan kamar awa daya an samu Amatullah ta dawo hayyacinta suna wani daki Asmau sai godiya take yiwa matar taji an turo kofar dakin tare da sallama. Wani daddadan kamshi ne ya mamaye dakin kafin ta kula da mutumin da ya shigo cikin shigar sojoji masu babban mukami.
Amatullah dake kwance ta tashi zumbur tace
" Ummi wannan ne baban nawa?".
ABINDA AKE GUDU🙆🏽29

Batul Mamman💖

Dan tsayawa yayi yana kallon kyakkyawar yarinyar. Tana daga zaune harda ware hannuwa ta dan bata rai "Baba bazaka yi min oyoyo ba? Nima bazanyi maka ba. Shine ka taho aljannah ka barmu ni da Ummi."

Asmau kunya ta isheta ta kai hannu zata hana Amatullah sai matar ta girgiza kai.

Taku yake mai cike da kamala da kuma kwarjini ya karasa daya barin gadon ya zauna yana murmushi. Asmau ta kasa daga ido ta kalle shi. A kan gadon ya zauna ya janyo Amatullah ya dorata akan cinyarsa.
"Oyoyo baby din Baba. Kiyi hakuri bazan kara tafiya na barki ba kinji"

Amatullah ta kankame shi ya dago kai ya kalli mahaifiyarsa yana murmushi. Juyowa yayi inda Asmau take zaune suka hada ido ba shiri ta kara sunkuyar da kanta. Mutumin ba karamin kwarjini yayi mata ba. A kalla zai kai shekara arbain. Kayan jikinsa sun kara masa kyau. Shi kuwa mayar da hankalinsa yayi ga Amatullah yana shafa mata kai. Girmansa da matsayinsa bai sa ya kyamaceta ba. Muryarta ya sake ji tace "Baba idan anje aljannah ba'a zuwa gida ne. Kullum ni da Ummi bamu ganka ba. Kuma Zinayu sai tayi ta dukana baka zuwa ka yama min".

Sake hada ido suka yi da Asmau ya kula da kwallar da ta cika mata ido. Wani tausayinsu ne ya shige shi a lokaci daya. Ko ba'a fada ba yasan baban yarinyar nan ya rasu. Wannan ne dalilin da zaisa yarinyar ta rinka ambaton an tafi aljannah an barsu.

Tana daga jikinsa yace "daga yau duk wanda ya sake tabaki sai na rama miki kinji."

Matar da tayi masa waya tace "ai wannan Zinayu taga ta kanta. Tun dazu ake kawo kararta."

Amatullah tace "Zinayu nace fa ba Zinayu ba".

Daga matar har danta sai da suka yi dariya sosai. Asmau ta gaishe shi ya amsa fuskarsa a sake yana kallon Amatullah. Yarinyar ta shiga ransa lokaci guda.

Matar ya kallo yace "Hajiya gara kizo ku tafi gida nasan kin kwaso gajiya da yunwa. Munyi waya da Falalu za'a janyo motar gobe. Da kinyi min waya tun kuna hanyar ai da na turo mota daga Jos din."

Murmushi tayi "kai babu komai fa. Na tura Bilkisu da Shafiu a siyo musu abinci ne kafin mu tafi."
Ta dubi Asmau "kin kira 'yan uwanki kuwa? Ya kamata a san halin da kuke ciki kada suji shiru"

Shiru Asmau tayi, to ita wa zata kira bayan yanzu bata da numbar kowa a gidansu. Ta sunkuyar da kanta kasa kawai ta sako karya "babu kudi ne a wayar, amma nasan zasu kira idan suka ji shiru."

Hajiya ta dan bata rai "haba ke kuwa, me ya hana tun dazu kiyi min magana da tuni an siyo ko na baki tawa ki kira. Kai taimaka a samo mata kati ta kira gidansu. Wane layi gareki?"

Ba karamar kunyar taji ba. Tayi karya sun dauka gaske ne. Duk da dai kudin wayar dama bai wuce flashing ba tace "MTN".

Cikin ladabi ya mike zai fita Amatullah ta riko masa riga kamar zatayi kuka "Baba zan bi ka"

Wata waya da Asmau ta tabbatar mai tsada ce ya zaro daga aljihunsa ya mika mata "gashi ki rike min yanzu zan dawo"

Bata so ba haka ta sake shi ya fita. Kafin ya dawo Bilkisu ta shigo dauke da ledojin take away na abinci. Shima mutumin sai gashi ya dawo ya mikawa Hajiyarsa katin ta bawa Asmau. Na dubu daya da dari biyar ne guda hudu duka matar ta bata. Tayi ta godiya a son ranta daya ma ya isa.

Bilkisu ta durkusa har kasa tace "Uncle ina wuni"

"Lafiya kalau, ya gajiyar hanya?"

Ta amsa masa da lafiya, ya shiga tambayarta kanwarsa dake Jos wadda ta kasance mahaifiya ga Bilkisun.
Chapter 29 · 0% Book details