← Book details Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 74

Sashe 4

Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Asmau me nayi miki zaki yi min muguwar sakayya irin wannan? Uban waye yayi miki ciki? Har kinsan ki kebe da namiji ba tare da aure ba a tsakaninku?" Tana magana tana dukan Asmau ko ta ina. Su Anti Bintu ne suka yi kokarin riketa tana fada tana kuka.

Shema'u ma gefe ta koma tana nata kukan. Wane irin abin kunya ne wannan Asmau ta janyo musu a wannan halin da suke ciki?

Umma na dukanta duk da rashin lafiyar da take ciki amma ta kasa yin kuka. Biyewa son zuciya na 'yan mintuna ya wargaza dukkan wani farinciki da ta taba sani a rayuwarta. Irin ABINDA AKE GUDU kenan. Yau asirinta ya gama tonuwa. Sirrin boye ya fito fili bata da abinyi sai yadda Allah Yayi da ita. Mama ta rike hannun Umma da take shirin sake dukan Asmau "ba da duka zamu tambayeta ba Bara'atu. Kada ki bari bacin rai yasa kiyi aikin dana sani."

Muryar Umma har ta dashe tace "akwai wani dana sani daya wuce haihuwar wannan yarinyar? Fyade aka yi miki ko kwaya kika sha da har zaki yarda da namijin da ba naki ba?"

A hankali Asmau ta sakko daga kan gadon har allurar da ake yi mata karin ruwa ta fita daga hannunta bata sani ba jini ya rinka zuba daga hannun. Ranar wanka ba'a boyon cibi. Sai a lokacin ta soma kuka ta durkusa akan gwiwoyinta a gabansu Umma.
"Tsautayi ne da sharrin shaidan. Don girman Allah ku yafe mana. Wallahi sau daya ne kawai. Idan har ina da ciki na Abubakar ne".

Cikin tsawa Mama tace "kin ma isa ki dora masa. Wallahi nasan karya kike yi saboda kinga kasa ta rufe masa ido shine zakiyi masa irin wannan mummunan kazafi?" Magana take tana haki saboda bacin rai, sai kuma hawaye.
"Yanzu kinyi masa adalci kenan? Ko kwana baiyi a kabarinsa ba kike binsa da mummunar shaida bayan kinsan mala'iku suna tsayawa karbar shaida akan mamaci. Allah Ya isa tsakanina dake. Har yaushe kika ga Abubakar din ma? Mutumin da sau biyu yake zuwa Kano a wata. A can makarantarku dai kika hadu da wanda yayi miki"

Anti Bintu ta kama hannun Asmau ta tayar da ita tsaye cikin jin haushin maganar Mama gashi Umma taki cewa komai "wannan magana bata asibiti bace. Mu bari idan an sallameta sai ayi a gida. Amma kowa yasan bata da wani saurayi bayan Abubakar."

"Babu wata magana da zamuyi a gida. Kai, ku wuce mu tafi." ta fadawa Abdulhalim da Nasiba. Dukkaninsu an rasa mai bakin magana. Tabbas Abubakar ne kadai saurayin Asmau. To amma kowa yayi shaidarsa wurin kyaun hali. Mutum ne mai kawaici da kunya. Ita kanta Asma'un ba don a gabansu aka yi komai ba sai su karyata saboda itama ko 'yan unguwa zasu shaideta da kyaun hali.

Abdulhalim yaso ya tsaya domin a kare maganar a nan Mama ta daka masa tsawa dole yabi bayanta suka fita tana ta bambami. Bude kofar dakin kenan suka hadu da mata sun kai shabiyar daga gidan rasuwar suke sun taho jin halin da Asmau take ciki. Kana ganinsu kasan duk abinda ake yi a cikin dakin sun gama ji. Mama ko kallo basu isheta ba tayi gaba su Nasiba na bin bayanta. Matan dai tunda har an gansu dakin suka shiga suna tambayar ya mai jiki. Anti Bintu tace da sauki suka tashi ko minti daya cikakke basu yi ba suka fice ana ta mayar da zance.

Bayan fitarsu Anti Bintu tace "Yaya Bara baki ce komai ba kina jin abinda Maman Abubakar take fada."

"Me zance Bintu? Kin taba ganin cikin shege yayi uba kai tsaye a kasar musulmi? Duk abinda Mama Yalwa ta fada tayi min daidai. Nima da namijin ne nawa bazan yarda a kakaba masa cikin shege ba." Hada ido suka yi da Asmau Umma ta sakar mata wani mugun kallo. Abinda yafi wannan ma tasan zata gani tunda haka ta faru. Kusa da Umman ta dawo ta sake durkusawa a kasa ga wani irin jiri da take ji, kirjinta kuma kamar ana hura wuta.

"Umma ki yafe min. Wallahi sharrin shaidan ne kuma muna ta istigifari kullum. Wallahi bazan kara ba wannan ma kaddara ce. Umma...."
Ture ta Umma tayi ta dubi inda Shema'u da Jafar suke tsaye suna hawaye "Jafar fita ka samar mana abin hawa mu koma gida."

"Asma'un fa?" Anti Bintu ta tambaya. Tamkar da dutse tayi maganar haka Umma ta shareta. Bayan Jafar ya dawo Umma ta rike hannun Shema'u saboda kafarta data rike suka yi hanyar fita. Asmau na ganin haka ta tashi tabi bayansu Anti Bintu na kiranta bata tsaya ba. Haka suka fice daga asibitin ga dare suka shiga tasi din da Jafar ya tsayar. Har suka isa gida babu mai magana a cikinsu.

Abin mamaki nasu gidan a cike suka same shi bayan tunda aka yi rasuwar aka koma gidansu Abubakar. Bacin ran Umma ya sake karuwa don tasan labari ya riga ya iske duka umguwar. Sai cewa akeyi ya jikin Asmau. Aka rasa me amsa musu tunda sun san ainihin abinda ya kawo su.

A cikin falo Umma zata wuce dakinta taji ance "Ke Bara'atu dakata." Ta gane muryar mai maganar ta san ba karamin rashin mutumci yazo yi mata ba. Alh Rabe ne kanin marigayi. Kin tsayawa tayi sai da taji muryar Hajjo mahaifiyar maigidanta sannan ta juyo. Kuka ne ya kwace mata yadda taga duk 'yan uwan mijinta a wurin mazansu da matansu ga kuma mahaifiyarsu. Allah Yasa itama akwai nata 'yan uwan wadanda suka zo biki daga Wushishi ta jihar Niger. Dangin mijinta basu taba kaunarta ba gashi Asmau ta sake shafa mata kashin kaza.

Jafar ya juya ya matan dake binsu kamar jela yace duk su fita. Surutai da gunaguni suka rinka yi har suka watse. Aina'u da Yasar ma yace duk su tashi. Yasar baiso hakan ba a ganinsa shima ya girma ransa a bace ya tura Aina'u suka shige ciki.

Kowa a zaune banda Asmau dake rakube a jikin kofa. Alh Rabe ya zare mata ido "munafuka algumguma ai sai kizo ki zauna kin wani tsaya mana a ka kamar sa'anninki."

Da sauri ta zube a wurin da take tsaye ta dukar da kanta hawaye na kwarara a kumatunta. Hajjo ta furzar da goron bakinta a kan kafet tace "hankalinki ya kwanta ko Bara'atu? 'Yarki ta janyo mana abin kunya ta bata mana suna a gari. Tun rasuwar Shu'aibu babu yadda bamuyi dake ba akan ki bari 'yan uwansa su raba 'ya'yan a tsakaninsu kika ki amincewa. Yau wa gari ya waya uhmm? Dama tarbiyar mace mai zaman kanta har wata tarbiya ce." Hanci ta tsaya fyacewa tana kukan Bara'atu ta cuce ta.

Umma tayi shiru kawai, tun dazu da aka aika musu da rasuwar Abubakar babu wanda yazo cikinsu. Yinin bikin ma cewa suka yi tayi a gidanta suma zasuyi nasu ko babu amarya. Sai yanzu da wannan abu ya faru shine duk suka taho. Harda Yaya Abu da babu abinda ta halarta na bikin wai tana ciwon wuya.

Alh Rabe ya doka tsaki "dama me kike tsammani daga mace irin wannan Hajjo? Saboda na taimaki rayuwar 'ya'yan dan uwana fa har shahada nayi nace zan aureta duk da yadda nake kyamar mayu 'yan garinsu amma taki. Yanzu ta fada muku shegen da ya dirka mata cikin ko kuwa saboda samarin sunyi mata yawa bata san waye uban ba?"

A kufale Jafar yace "Kawu nayi tunanin zama akayi na maslaha akan matsalar nan ba bakaken maganganu ba."

Umma ta watsa masa harara don yayi shiru amma duk da haka sai da Yaya Abu ta hado masa ashar ta kunduma masa. Sannan ta dubi Asmau "to karuwar cikin gida wadda ake nuna mana kunfi kowa tarbiya. Cikin na waye don ko ni ban yarda na yaron nan bane Abubakar bawan Allah. Gara da Yalwa taki karba zaku gurbata musu asali."

Jin batayi magana ba har Hajjo ma ta sake tambaya yasa Kawu Rabe yayi kanta yana haurinta da kafa. Tun tana zaune har sai da tayi kasa yana tattaka ta. 'Yan uwan Umma suka tashi aka rike shi sannan suka janyeta. Umma dai sai kukan zuci. Duk abinda aka yi musu a yau Asmau ce ta janyo mata saboda haka bata da bakin magana. Kallonsu take yi suka ci gaba da caba musu bakaken maganganu 'yan uwanta suna karewa sannan suka tashi. Hajjo tace "ki shirya sati mai zuwa ki turo min Yasar da Aina'u gara nasa su a gabana don bazan bari zuri'ar Shu'aibu ta gama lalacewa ba ina raye.

Ranar gidan Umma ansha kuka kala kala. Shema'u duk yadda suke da kanwarta ko inda take taki kallo. Asmau ta bata kunya sosai. Anyi ta tambayarta kuma taki magana tunda sunki yarda cikin Abubakar ne. Abu dai har tsakar dare suna dakin Umma ana ta magana daya. Asma'u kuwa babu wanda ya shigo dakinta. Kawayenta da suke gidan gabadayansu bata san inda suke ba har da aminiyarta Walida wadda take ganin kamar bazata gujeta ba a wannan yanayin.
ABINDA AKE GUDU 🙆🏽5

Batul Mamman💖

Zaune take kan abin sallah tana addu'a tana zubar da hawaye. Bata taba tsammanin ganin rana makamanciyar wannan ba a rayuwarta. Babu Abubakar ga cikinsa a jikinta batare da aure ba. Yau da cikin aure ne bata san irin soyayya da gatan da Umma da Mama Yalwa zasu nuna mata ba. Ashe haka ake ganin bambancin rayuwar wadda aka shafa fatiha akanta da wadda ba'a shafa ba? Gashi dai duk abu daya suka yi, amma mai aure sai ta zama tauraruwa har idan batayi ciki ba ayi ta korafi ko aji tausayinta. Ita gashi kuskure sau daya tak, tayi cikin da bata bukata gashi hatta mahaifiyarta tana nuna mata kyama. Aure ibada ne, zina kazanta ce. Wani kukan ne yazo mata da taji cikinta na kukan yunwa. Yanzu idan taci abinci abinda ke cikinta ma zai samu? A hankali ta shafi cikin zuciyarta na kuna.

"Wayyo Allah, Ya Allah Ka jikan Abubakar Ka karbi tubanmu" abinda ta fada kenan cikin raunanniyar muryar da ta gama dashewa don kuka. Akan abin sallar bacci ya saceta tana rungume da AlQur'ani.
Chapter 4 · 0% Book details