← Book details Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 74

Sashe 63

Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asmau ta karbi kunshin ledar da Shemau ta bata. Doguwar riga ce abaya amma ruwan madara. Rigar ta tsaru karshe da mayafinta. Bude baki tayi zata fara godiya da dan hawayenta Shemau tace "indai tayi miki kyau shikenan. kiyi sauri ki shirya kiyi sallah kada ango yazo kina daure da tawul. Mu zamu tafi ga Zulaiha nan da Walida sune kawayen naki dama. Sabira da mijinta bai kamata ta zauna ba."

Shemau bata fita ba sai da Asmau tayi sallah ta shirya. Wani turare mai maiko ta bata ta fara shafawa kafin aje ga sauran. Kamshi ne zai tarar da Jikamshi.

Bayan tafiyarsu daga ita sai su Walida suka dawo falo don ba'a son wannan zuwa har uwar daki da abokan ango. Alamun bude gate ya sa hankalin Asmau tashi. Mayafinta ta gyara kafin su shigo. Su hudu ne harda angon. Biyu abokansa da kaninsa Ismail. Bata iya ganin kowa sai muryoyi da take ji. Ba wasa suka tsaya yi ba nasiha ce dai da addua. Sai a lokacin taji muryar maigidan nata yace Amin. Daga nan suka tashi yace akwai dreba zai ajiye su Zulaiha. Abokin nasa mai dauko amarya yace shi zai je. Ashe Walida ce ta dauke masa hankali.

Tana ji ya fita rakiya ta kasa bude mayafin bare ta tashi. Lokacin da ya rufe kofar gidan kuwa zuciyarta ba karamin harbawa take ba. Anyi an gama yau ga Asmau a matsayin matar Ishaq.

Motsi da kamshinsa taji a kusa da ita ta sake kankame mayafin. Shiru bata ji ya zauna ko yayi magana ba. A hankali taji an bude gaban mayafinta ya shigo da kansa ciki. Ashe a gaban kafafunta ya durkusa. Zatayi baya yasa hannu ya zagayeta ga mayafinta ya rufe su sai kamshin turaruka da numfashinsu. Babu abinda zata iya yi sai kawai ta rufe idonta cike da kunya.

A hankali yake mata magana "Kinyi kyau Matar Jikamshi, yau so nake kamshinki ya rikita ni shiyasa zanyi ta like miki"

Sake runtse ido tayi tana jin wata irin kunyarsa tana karuwa a zuciyarta. Ya dago kanta tare da matso da bakinsa kusa da nata ga hancinsu yana gugar juna
"Ko na daukeki ne?"

A nutse ta bude ido suka sauka cikin nasa. Murmushi tayi masa yaji gabadaya ta hargitsa masa lissafi. Irin wannan farincikin a karkashin inuwar aure halattaccen zama kawai Allah Yake sako shi. Bai dena kallonta ba ya rike mata hannu suka tashi. Mayafin ya cire ya ajiye a kan kujerar ya karewa rigarta kallo. Shemau ta iya zabe. Sai a lokacin ita ma ta kula da kayansa. Yau ma harda babbar riga a shaddarsa ruwan madara kamar kayan jikinta. Hular kuwa a kasa ta ganta kusa da inda take zaune. Yana rike da ita har suka je dakinta.
"Shiga ki jirani naje nayi wanka. Kunyarki nake ji da nace ki rakani. Amma kiyi alwala kafin na dawo" Yana kashe ido tana sunkuyar da kai. Sai da ta shiga ya wuce yana murmushi.
*****

Da abin sallah ya shigo harda mayafinta na falo sanye da kayan bacci riga da wando. Ya shimfida musu abin sallar tana kallonsa sannan ya nuna mata alamun ta tsaya suyi sallah. Kira'ar Jikamshinta ta tafi da ita don nutsuwa da bawa harufa hakki. Raka'a biyu suka yi sai shafai da wutri sannan ya shiga jero addua da larabci kamar bazai dena ba. Bayan ya kai karshe suka shafa ya dawo gabanta ya dafa kanta ya sake wata sannan ya tashi zai nade abin sallar. Karatun Uwargida ta tuna ta dan matsa a kunyace ta karba ta ninke. Ya ji dadin hakan kuwa sosai.

Fita yayi daga dakin ya dawo yace ta biyo shi. Falo suka koma ya ajiye mata snacks, nama, juice da youghurt.
"Wanne kika so"

Jikinta duk ya fara sanyi ta ce ta koshi. Yayi murmushi wannan salihancin duk zatayi ta gama ne.
"Ni zanci kinga ya kamata ki zauna a kusa dani har na koshi ko"

Tace "uhmm" kamar wadda ta tauna flagyl bisa kuskure. Centre table din na gabansa ta zagayo zata zauna a kusa dashi kawai ya janyota kan cinyarsa tare da yi mata rikon da bazata iya gudu ba.
"kada kice min kunyata kike ji kin san ni dai bani da ita indai a kanki ne. Kema kuma haka nake so ki zama."

Ta rausayar da kai gefe guda tana kokarin zillewa.
"Idan ba kya so muci abincin sai mu koma inda muka fito ni bani da matsala."

Tace "To bari na matso da plate din ni ina jin yunwa"

Hancinta yaja yana dariya "ace sai da dabara zan samu kici abinci."

Bayan sun gama ta kwashe komai ta kai kitchen din da bata gaji da gani ba tun da su Walida suka nuna mata. Da ta dawo ya kashe duk kayan wuta suka shiga ciki. Dakinta zata shiga yace "muje namu dakin ki saka masa albarka"

"Brush zanyi"

"Can ma akwai duk abinda zaki bukata" hannunta ya kama suka tafi. Ni'imtaccen kamshi da sanyi ne suka doki hancinta. Komai na dakin sabo ne. Dama dakuna hudu ne a gidan. Aka saka mata gado a biyu dayan aka mayar mata karamin falo. Nasa dakin ya dauki hankalinta. Ya shiga bandaki ta tsaya dube dube. Wani bakin abu mai santsi ta gani akan gadonsa ta dauka. Baki ta bude da ta gane ko meye. Rigar bacci ce mai kyau da ta dace da amare.

Tana jin zai fito ta ajiye sai dai ya ganta. Ya zo ya rungumeta ta baya "rigar tayi miki kyau ko? Hmmm nifa ban ganewa kamshin nan naki ba. Ji nake kamar na mayar dake jikina"

Asmau ta janye jikinta kai a kasa. Rigar ya mika mata yace taje ta shirya yana jiranta don yaga taki sakewa a nan. Idan ta wuce minti goma zai biyo baya. Dakinta ta koma tana mayar da numfashi kamar wadda tayi tsere. Sai juya rigar take yi a hannu. Karshe dai ta sake shiri ta saka ta dora zani ta fito.

Daga bakin kofa ya tareta ya dagata sai kan gado. Sai dai kuma yana ajiyeta ta soma hawaye. Zuciyarta tayi mata nauyi sosai. A take ya rude yana tambayarta ko me ya sameta. Duk yadda zaiyi Asmau taki magana sai kuka har yaji babu dadi a ransa. A sanyaye yace
"Kin tuna Abubakar ne? Addua ya kamata kiyi masa ba kuka ba"

Tayi saurin girgiza kai. Idan ya tabata kuma jikinta rawa yake sosai. Ganin taki magana sannan kamar tana tsoronsa sai kawi ya kwantar da ita yaja bargo ya lullubeta tare da yi mata kiss a goshi "kiyi hakuri idan nayi miki abinda bakya so ne. Just sleep bazan dameki ba"

Daya gefen ya koma ya zauna yana kallonta. Asmau ta juya baya tana kuka mai tsuma zuciya da tada hankalin mai saurare. Dole tayi kuka a wannan rana ko taji sauki a ranta. Yana gefe yana jin kukan har ransa amma ya rasa me take so.

Sai da tayi mai isarta yaji tana ajiyar zuciya. A zaune ma yake jingine da pillow yana kallonta ya rage hasken dakin sai fitilar gefen gado.

Baiyi fushi ba ya matso kusa da ita ya sanyata cikin jikinsa. Fuskarta duk hawaye ta matsa kusa dashi itama don kokari harda zagaye hannuwanta a jikinsa ta kwantar da kanta a kafadarsa tana mayar da numfashi.

Hankalinsa ya dan kwanta da yaji ta a jikinsa ya shafa mata kai "kukan me kika yi, dama akwai abinda zai saka ki kuka ki zabi yinsa ke kadai ki kasa fada min?"

Saukar hawaye mai dumi yaji a kirjinsa tace "Jikamshina don Allah da gaske kana sona?"

"Kinfi kowa sanin amsar tambayarki"

Ta dago kanta tana fuskantarsa kunya sosai a tare da ita. Muryarta ce take nuni da rauni da ciwon dake cikin ranta "a yau na kara tsanar kaina da biyewa zuciya, nayi aure a matsayin budurwa amma na dade da rasa wannan darajar. Ban san na gama cutar kaina ba sai yanzu, lokacin da duk wata mace take jin ta isa a wurin mijinta idan ya sameta cikakkiyar budurwa. Na rasa wannan damar, bazan taba yi maka tinkaho da abinda bani dashi ba. Ina jin kunyarka ina jin kamar na cuceka ma...."

Allah Sarki, tausayinta yaji ya kama shi sosai har tasa zuciyar ta raunana ya hanata karasa maganar ta hanyar da yasan dole tayi shiru. Sai da ya gama kissing dinta ya sanya yatsansa a saman bakinta. Tana kallonsa da fuskarta mai hawaye "ba karya kika yi min ba game da rayuwarki. Nasan komai kuma duk da haka Allah Ya sanya min sonki a zuciyata. ASMAU yarda da kaddara shine cikar musulunci. Abinda kika rasa bazai taba dawowa ba. Tunda kinsan baki da iko akansa babban abinda zaki yiwa kanki gata dashi shine hakuri da dangana. Mata da yawa suna aure a irin wannan yanayin kuma wasu sai kiga asirinsu ya rufu. Ke da naki ya fito fili kin zama misali ne ga sauran mata. Kinyi nadama kin tuba, kuma wannan ake nema daga dukkan musulmin kwarai. Allah Ya kara kare sauran mata daga haduwa da fadawa irin wannan sharrin."

Wani kukan mai karfi yazo mata tace "wallahi sau daya ne...sau daya tsautsayi ya fada mana. Ka yafe min don Allah."

Rungumarta yayi sosai a jikinsa duk dauriya irin tasa sai da yaji hawaye ya zubo daga idonsa. Ya Allah Ka nesanta mu daga tarkon zina. Mai zubar da kimar mai kima, ta zubar da girman babba, ta wulakanta mai daraja. Idan aka yita Allah zai iya yafewa wanda ya tuba amma wallahi tayi tambari kenan a rayuwar wanda yayi.
Chapter 63 · 0% Book details