← Book details Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 74

Sashe 15

Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanin kanka ne yadda aure yayi tsada ni kuma ba wani abu na tara ba. To kuma ga abu mu muna so suma matan suna so. Sai a taimaki juna".

Runtse ido Abubakar yayi "ji yadda kake cewa a taimaki juna kamar wani aikin kwarai. Kana dan malam har ka manta haramcin taba jikin macen da ba muharramarka ba? Ko ka manta inda Allah SWT Yake cewa : *WALA TAQRABUZ ZINA INNAHU KANA FAAHISHATAW WA SAA'A SABILA*
(ISRA' 32)

Ma'ana _KUMA KADA KU KUSANCI ZINA DOMIN ITA ALFASHA CE KUMA HANYAR BATA_

Taba jikin budurwa da niyar gusar da sha'awa batare da kunyi abin gabadaya ba yana cikin abinda Allah Yayi hani dashi. Kallo wannan da irin maganganun nan da kuke yi duk yana ciki. Wata rana sai kaga anyi abinda ake gudu azo ana cizon yatsa."

Qasim yayi murmushi jikinsa ya danyi sanyi sai dai shaidan bai barshi ba.
"Naji kuma duk nasani to amma ka manta cewa Allah SWT mai yawan gafara ne da jinkai? Idan mutum ya aikata irin haka tuba fa kawai zanyi a kankare min zunubin. Haba Abubakar kaima kasan yadda zuciya take. Ni a haka nasan ina kokari don ban taba ketawa kowace mace haddi ba. Za'ayi abin sama sama gayyar ta watse."

Abubakar yace "Muna cikin wani zamani ne da hanyoyin gurbata tarbiya musamman masu nuni da zina suke da matukar yawa. Cartoon wannan sai kaga mage da bera suna kiss. Duk a haka ake lalata mana zukata. Na dade da sanin ina cikin maza masu karfin sha'awa shiyasa kaga na dage da yawan azumin litinin da alhamis. Idan naga abin zai dameni har sauran ranaku inayi. Manzon Allah SAW yace a lokacin da mutum yake zina fa babu imani a tare dashi. To me zaisa mu biyewa son zuciya haka kawai kana kan wata mace mala'ikan mutuwa ya ziyarce ka".

Qasim ya dubi abokinsa. Tabbas Abubakar ba tun yau ba baya cikin maza masu kallon mata. Shiyasa ake masa kallon mai kunya sosai shi kuwa yana yi ne don ya kare zuciyarsa.

"In Allah Yaso zanyi kokarin denawa sai dai fa abin sai a hankali. Bazan maka karya ba wallahi na saba sosai. Allah mun tuba."

Da haka hirar ta kare bayan la'asar Abubakar ya koma gida.

*****
Washegari lahadi Umma ta tafi da Aina'u yinin 'yar wata kawarta sai Asmau da Yassar a gida Abubakar ya kirata a waya zai zo suyi sallama don yau da wuri yake son tafiya.

Sauri tayi ta karasa girki sannan tayi wanka ta canza kaya. Kwalliya tayi sosai irin yadda take karantawa 'yan matan littafi na yiwa samarinsu. Ta saka wata doguwar rigar atampa maimakon ta daura dankwali tasa hijab ko mayafi mai mutumci yadda ta saba sai ta dauko wani karami a kayan Aina'u ta yafa rabin kanta da yasha sabon kitso duk a bude ta gaba. Falo ta koma ta zauna sai taji kunyar ya ganta a haka. Ta tashi ta koma zata canza wata zuciyar tace tayi zamanta abinda sun kusa aure kuma dai haka ake yi yanzu don ita duk abinda ta karanta har ranta gani take yi daidai ne saboda a yadda ta dauki marubuta masu buga littafi da online komai suka rubuta basa kuskure.

Sake shafa hoda tayi ta dawo falon. Tana zama Abubakar yayi sallama tare da neman izinin shigowa ta amsa masa.

Gabansa ne ya fadi da yaga Asmau. Tayi kyau sosai gashi tana da 'yar kiba sai rigar ta kamata a kirji da kugunta. Ba wai bai taba ganin yanayin jikinta ba saboda yau da gobe yakan ganta babu mayafi amma sai bisa kuskure. Yau kuwa shigar ta tsaya masa a kokon rai har ya kasa dauke idonsa daga gareta.

Murmushi tayi na nasara saboda yadda taga yanayinsa ya canza. Tunda ta fara karance karance da hirarsu da Walida taji ta matsu ko hannunta ne ya dan rike itama taji yadda ake ji.

Wani juya ido tayi duk sauran kunyar suka bace "Mine ka zauna mana."

Wani jan numfashi yayi "Asmy kinyi kyau"

Tayi masa murmushi "nagode"
"Kaci abinci ko na kawo maka? Bana son ka tafi da yunwa".

Abincin ya bukaci ta kawo masa. Ta tashi tana tafiya mai daukar hankali. Har ta shige kitchen ya kasa dena kallonta. Sai da ta bace yace _Astagfirullah_ tare da kudurta niyyar zaice ta suturta jikinta sosai.

Tana dawowa kujerar gefensa ta zauna kamshin turarenta ya bugi hancinsa sai ya fasa cewa ta rufe jikin. Yana matukar son Asmau amma yau harda wata muguwar sha'awarta ce ta taso masa. Yana cin abinci suna hira kadan kadan domin duk hankalinsa ya koma kan halittar jikinta.

A nata bangaren ta lura da canjawarsa kuma taji dadi a ranta. Da ya tashi zai tafi dubu biyu ya miko mata kudin motar makaranta. A da sai ya bata sau uku bata karba ba har suyi fada wani lokacin. Amma yau kawai don taji hannunsa a nata ta mika hannun a kunyace tana kallon kasa. Tana sane tayi hakan hannunta ya kai kan nasa maimakon kudin.

Saurin dauke hannun tayi saboda wani yanayi na daban da taji (dama shaidan komai kankantar haram dada mata dadi yake fiye da yadda take don kawai a cigaba da aikata ta)
"yi hakuri ban kula ba"

Abubakar yaji dadi fiye da yadda taji domin tana taba hannunsa ji yayi kamar ya janyota jikinsa. "Dama ina zaki kula kina wani sunkuyar da kai kasa. Ni zan tafi sai friday in sha Allah. Ki kular min da Asmy na".

Tana murmushi tace
" nima ka kular min da Yayana. Allah Ya tsare Ya kaika lafiya."

Haka Abubakar ya tafi surar Asmau tana yi masa gizo. Sawa yayi a ransa idan sunyi waya zai fada mata ta dena irin shigar nan har sai sunyi aure. Sai dai yana isa bayan sallar magriba wasu hotunanta suka shigo wayarsa. Duk babu wanda tasa dankwali kanta wasu ma rigunan sun dameta fiye da rigar dazu.

Bai iya yi mata maganar da yayi niyya ba ya rasa dalili.

A haka suka kwashi wajen wata biyu. Asmau ta dena jin kunyar fita gabansa da shigar bayyana jiki indai tayi sa'a yazo Umma bata gida. Mayafin nan kullum a kafada an baza gashi ta kasan dankwali. Tun yana tsanar kansa idan suka rabu har ya saki rai yana jindadin hakan tunda yasan aurensu yana kusa. Kusa da juna suke zama yanzu ana hira sai su rinka neman hanyoyin taba hannun juna kowa yana nuna kamar ba hakan bane a ransa.

Sai yanzu Asmau ta yarda suna soyayya domin tafi jindadin alakarsu. A zuciyarta ta kwantar da hankali tunda tana da yakinin aure zasuyi kuma dai ana aure komai ya wuce. Ita yanzu babban burinta yayi kissing dinta ko sau daya ne yadda take karantawa. Ayi kiss amma sai a nuna kamar bisa kuskure ne ko kuma a nuna na komai yin hakan a addini da al'adarmu.

A nasa bangaren shima ya dena damuwa. Kullum sha'awarta karuwa take yi a ransa hakan yasa ya soma rasa nutsuwarsa. Bashi da aiki sai azumi kamar mai kaffara amma wasu ranakun shi kansa yasan a irin tunanin Asmau da yake yi na tsantsar sha'awa azumin nan baya kaiwa ko ina.
*****

Su Asmau an gama jarabawa kuma wannan karon suna dawowa makaranta idan aka sake hutu za'ayi bikinta.

Ko sati ba suyi ba da fara hutu Anti Bintu tazo Kano ziyara. Kwananta biyu mijinta yazo da zasu koma tace da Asmau zata tafi. Umma bata musa mata ba ta umarceta da hada kaya. Murna tayi sosai Aina'u kuwa ansha kuka gashi ba'ayi hutu ba.

Abubakar yaji dadin komawar Asmau Zariya wani satin da ya zagayo ko Kano bai je ba. Mama Yalwa tace ta gane dama zuwan ba nasu bane na Asmau ne.

A gidan Anti Bintu yake zuwa su sha hira wadda a hankali ya fara rungumarta da sunan zaiyi kewarta idan ya tafi. Su biyun duk sun san haramcin abinda suke yi amma sunyi nisa. Suna haduwa duk yakin da suka shirya da wannan sabuwar dabi'ar tasu sai ya rushe.

Anti Bintu ko kadan bata san me suke yi ba. Falonta take bar musu idan yazo. Nutsuwa da tarbiya irin ta Asmau da Abubakar babu wanda zai taba zargin haka tsakaninsu.

Wata rana bayan asuba karamin dan Anti Bintu Haidar yana toilet bayan ya gama ya fara kiran Asmau tazo tayi masa tsarki. Lokacin ko bakwai na safe bata yi ba duk baccin da take ji taki komawa saboda an turo cigaban wani labari da take karantawa. Ko yunkurin tashi bata yi ba tace masa tana zuwa.

Haidar ya kirata yafi sau biyar tana cewa gata nan har Anti Bintu ta fito daga kitchen tayi masa tsarkin lokacin har ya fara kuka. Duk abinda suke yi da Asmau ta ji.

Dakin nasu ta shiga Asmau tayi nisa a duniyar labari sai ganin Antin tayi a tsaye a gabanta. Da sauri ta tashi a tsorace zata fita.

"Dawo indai tsarki zaki yiwa Haidar nayi masa"

Duk sai taji kunya sannan ta gaisheta. Anti Bintu ta dauki wayar da ta ajiye akan gado ta bude ta dan karanta wani bangare na labarin. Tayi scrolling sama kuma irin sakon nan ne na kwanciyar aure.

Jikin Asmau kamar mazari don tsoro ta gama rudewa. Anti Bintu ta kama hannunta ta zaunar da ita a bakin gado sannan taja kujerar gaban mudubi ta zauna.
Chapter 15 · 0% Book details