← Book details Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 74

Sashe 70

Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya sauketa "bari nayi miki a hankali saboda baby na. Amma fa idan Hajiya bata bari mun tafi gidanmu ba to za'ayiwa babyn nan kani ko kanwa a gidanta"

Murmushi tayi na jindadi Jikamshinta ya dawo. Shi kuma ya janyota yana bin fuskarta da kiss ko ta ina.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽59

Batul Mamman💖

Jin taku kamar na Hajiya yasa Col. Ishaq ya sauke Asmau. Gani yake kamar a da can ba sonta yake ba saboda yadda yake jinta a ransa yanzu. Ita din ma shi take kallo cike da so. Bata da abinda zata saka masa dashi face addua da kuma tsantsar kulawa irin wadda ta dace da miji.

A haka suna wannan kallon kallon da murmushi a fuskokinsu Hajiya ta karaso dakin tace ya wuce gida ya daukowa Asmau kaya kamar na sati daya. Ramarta tayi yawa tana so ta zauna har ta mayar da jikinta. A take murmushin dake fuskar Col. Ishaq ya bace. Asmau ta gimtse dariya don da gaske ya bata rai. Hajiya ta saka shi a gaba suka fita tare. Bata kyale shi ba sai da taga ya shiga motarsa ya tayar.

Suna fita Asmau ta kwashe da dariya. Tsakaninta da Allah itama tana kewar mijinta. Amma yanayinsa ne yasa tayi dariya don tasan akwai rigima a gaba. Yana iya cewa me yasa da Hajiya tace zata kwana bata nuna bata so ba.

Har ya isa gida tunanin yadda zaiyi da Hajiyarsa yake. Ko don bata san yaushe rabonsa da su yiwa juna kallon kirki bane shi da Asmau. Yau da ta kasance ranar farinciki sosai garesu, sun shirya ga kuma babbar kyauta shine zata hanasu celebrating. Shawarar da yasan zata fishshe shi ya yanke sannan ya koma gidan.
*****

Tuwon masara Haj Lubabatu tayi da miyar kuka wadda taji naman rago da wake. Tana yi zuciyarta fes ciki da farinciki. Ba karamin tausayin Ishaq take ba gashi dama ance mahakurci mawadaci. Ta san irin yadda rashin haihuwa ya dame shi sosai. A dalilin hakan babu irin bacin ran da bai gani ba saboda yana da sa abu a rai. Ko yaya aka fadi maganar haihuwa mai kama da gori sai ka gani a fuskarsa.

Duk yadda Asmau taso taya Hajiya aiki hanata tayi tace ta koma daki ta kwanta. Yadda take ji da ita da cikin jikinta ai bazata yi sake wani abu ya faru ba duk da komai na Allah ne. Da Bilkisu ta dawo daga makaranta ne ma ta tayata har suka karasa. A falo suka zauna su ukun suna hira Bilkisu ce mai yin fiye da rabin zancen. Hajiya ta sa ta zubawa Asmau tuwo mai yawa tace kuma sai ta cinye. Zuwa lokacin hankalinta ya fara tafiya ga inda Jikamshinta ya tsaya gashi har anyi isha bai dawo ba kuma wayarta tana gida. Haka ta rinka cin tuwon a hankali sai taji sallamarsa. Wani sanyi taji ya ratsata amma ta basar ta cigaba da cin abinci tana kallon plate a dole bata so ta kalle shi kada Hajiya ta gani.

Wata jaka ce yar madaidaiciya ya shigo da ita mai dauke da kaya. Bilkisu ta gaishe shi sannan ta karbi jakar ta kai dakin Hajiya kamar yadda ta bata umarni. Hajiyan ma tashi tayi
"Bari naje nayi sallah duk kunyi kun barni. Ki tabbatar kin cinye tuwon nan kafin na dawo. Kai kuma sai da safe nasan kila kafin na idar ka tafi"

Col. Ishay yace "to Hajiya Allah Ya bamu alhairi" a ladabce

Tana tafiya ya dauke plate din gaban Asmau sannan yaja hannunta. Ta bude baki zata yi magana taji ina zai kaita ya marairaice fuska "please Matar Jikamshi magana zamuyi kafin Hajiya ta fito"

"A ina?" Ta tambayeshi tana waigen kofa. Bai bata amsa ba ya ja hannunta suka bi wani korido suka je wani daki. Dakin a share yake kamar ana kwana sai dai ko ba'a fada mata ba ta gane dakinsa ne na da kafin aurensu. Bakin gado ya zaunar da ita ya janyo kujera irin ta aiki a gaban wani tebur gabanta ya zauna shima
"Har abinci kike iya ci tun dazu baki ganni ba amma ko a jikinki"

"Allah Sarki Jikamshina kalli ka gani kadan naci saboda na rasa inda ka tsaya gashi babu waya a hannuna"

Murmushi yayi mata yana kara godewa Allah wai Asma'unsa ciki gareta.

"Yanzu dai ki bani abincin nan yunwa nake ji. Amma gaskiya bazan yarda ki rinka bawa baby na tuwo ba."

Ta dan sha kunu cikin wasa "sai na fadawa Hajiya kuma ka tashi ka tafi gida kada dare ya kara yi"

Wani kallo yayi mata mai nuni da zancenta wasa ne "babu inda zani, ke yanzu sai ki kwana a nan ba tare dani ba?"

Ta girgiza kai "da Hajiya tace kayan sati sai da zuciyata tayi tsalle.....amma na murna"

"Zakiyi bayani ne. Ni dai bani abinci naci."

Da hannun ta rinka bashi itama tana ci. Sunyi kusan minti shabiyar saboda cin tuwon ma wani sabon salo ake masa. Idan ta bashi sai ya lashe mata yatsu ko ya cijeta. Tayi ihunta a hankali tace zata rama sannan su cigaba. Bayan sun gama ta wanke hannu a bandakin dake cikin dakin shima yazo suna kuskure baki don brush dinta yana cikin jaka. Ya rike fuskarta da hannuwansa yana shirin kissing dinta suka ji kamar muryar Hajiya.

Nan da nan Asmau ta rude ta rasa yadda zatayi. Shima uban gayyar yau dai ya rasa abinyi don kuwa duk abin sa Hajiyarsa yana jin kunyarta. Idon Asmau harda hawaye da taji Hajiya tana tambayar Bilkisu ina ta shiga daga cikin korido din. Taku kadan zasu kara su iso dakin. Duka ta kaiwa Col. Ishaq a kirji
"Duk laifinka ne da ka jawo ni dakin nan. Yanzu da wane ido zan fita don Allah"

"Kinji ki da wani zance, ba fa daukoki nayi ba da kafarki kika taho ke dadi miji. Ai da sai ki fada min ba dadewa zatayi a dakin ba"

"Yanzu laifina kake gani, ba a gabanka tace mana sallah zata yi ba." Sosai ta gama rudewa.

Col. Ishaq ma dai ya rasa mafita don bai san yadda zaiyi ba idan Hajiya ta bude kofar dakin nan.

Ganin sunyi tsuru ga Bilkisu tana ta kiranta yasa ta saddakar kawai. Gara ta fita da tayi ta zama tana tsoron su bude ayi zaton wani abin ma suke yi. Bude baki tayi tace "Haji..."

Yayi maza ya toshe bakin da hannunsa yana magana a daidai kunnenta duk ya riketa saboda tana kokarin kwacewa "tona mana asiri zakiyi kuma"

Ta soma cizon hannunsa yana runtse ido yau ba na wasan da ta saba bane da gaske mai zafi take masa.
"Matar Jikamshi zan rama kuma kada ma kiyi tunanin zan hakura idan kika fara wannan hawayen karyan"

Tana ji ya saketa bayan takun su Hajiya ya bar wurin ya soma tsokanarta "kunyar karya ma kike yi, kin gama saita baki zakiyi kissing Jikamshinki shine daga jin muryar Hajiya kika wani rude bayan kinfi kowa sannin a gidanta kike"

Duk yadda suke dashi har yanzu wani abin idan yayi ko ya fada sai taji kunya. Ta rufe idonta tayi hanyar kofa batare da ta amsa masa maganarsa ta farko ba tace "sai da safe"
Ai kuwa ya rikota yana bata hakuri kada ta fita yanzu.

Bayan dan lokaci kadan ya fita wai zai duba mata idan Hajiya ta kwanta sai taje ta kwanta kawai itama. Jinsa kawai take amma da wane ido zata kalli Hajiyan da safe.

Shigarsa falon ke da wuya ta fito ya sunkuyar da kansa kasa. Yi tayi kamar bata gane me yake ba tace "kaje dakina ka dauko jakar Asmau ka kai mata ko akwai abinda take bukata. Kuma ka rufe gidan. Sai da safe" daga nan ta juya ta koma ciki. Yafi minti uku a tsaye sai da ta sake kiransa tana cewa zata rufe kofar dakinta idan bai zo ya dauka ba. Ya shiga kamar salihin gaske ya dauko ya fita. Hajiya tayi murmushi kawai. Yaran zamani sai addua. Basa kunyar idon manya idan suna son juna.
*****

Asmau na kai kawo a tsakar dakin ya shigo da jaka yana murmushi. Bai zata Hajiya zatayi saurin barinsa da Asmau ba amma dama niyarsa ya kwana a gidan don nasa kayan na mota. Idan ta ga yaki tafiya yasan zata barsu su koma nasu gidan.
"Bukatarki ta biya Hajiya tace ki kwana a nan."

Ta zaro ido "da gaske? Jikamshina ka gama dani. Daga yau bazan kara fita daga dakin nan ba. Ranar da zan tafi ma sai Hajiya bata nan zan fito"

Ya soma dariya "ke dai kinji dadi kawai. Bari naje na dauko nawa kayan dama da shiri nazo. Ki kunna mana heather sai muyi wanka duk zafi ya isheni."

Harara ta wurga masa ya fice yana mata dariya. Da ya dawo duk suka yi wanka ta haye wata doguwar kujera da yake kwanciya ya huta da. Yace ta dawo gadon ta noke kafada "da kunya fa, Hajiya na gidan nan na kwanta kusa da kai"

Tasowa yayi daga gadon ya dawo ya hau kujerar ya matseta a karshe don tayi musu kadan. Cikinta ya shafa yana lumshe idanu "duk yadda kike so haka za'ayi, iyaka dai gobe muce ba kwanan gado muka yi ba na kujera ne"

Hannu ta kai zata tureshi ya sureta gabadaya sai kan gadon yana fada mata irin yadda yayi kewarta.
******
Chapter 70 · 0% Book details