← Book details Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 74

Sashe 48

Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuka sosai Amatullah take yi don har dankunnenta sai da yayi tsalle. Umma da Hajjo har suna rige rigen janyota jikinsu. Umma itama ta harzuka tace "wane irin rashin hankali ne wannan Asmau. Daga tayi magana sai duka."

Hajjo tace "kuma dukan ma a fuska, tayi kuskure don ba'a so a koyawa yara saka baki a zancen manya. Amma ya zaki mata hukunci irin wannan. Ji yadda dankunne ya karce ta"

Suna kokarin jan Amatullah amma taki tsayawa. Da Hajjo ta saketa jikin Asmaun ta koma tana kuka "Ummi kiyi hakuyi na dena"

Kuka Asmau ta saka, tasan bata kyauta ba don fushinta ta saukewa Amatullah. Ga zuciyarta dama ta gama rauni. Bata samun Jikamshi shima baya kira sosai sannan Qasim yana jiran amsarta na ranar da zasu dawo. Amatullah ta sake cewa "Ummina kin hakuya?"

Cikin kuka ta rungumeta sosai a jikinta "na hakura Ama"

"To ki dena kuka nima na dena"Amatullah ta fada tana share hawayenta.

Wannan ya kara karyarwa Asmau zuciya ta cigaba da kukanta bilhaqqi. Umma da Hajjo suka tsaya kallon ikon Allah. Sai da tayi mai isarta ta dauki Amatullah suka shiga ciki.

Suna tafiya Hajjo ta rike baki "Bara'atu anya yarinyar nan bata da mutanen boye? 'yan kwanakin nan na lura tana cikin damuwa. Wannan kukan ma da biyu ko uku ma zance take yinsa."

"Nima haka nagani, bari naje naji ko menene"
*****

Dariyarsu Umma ta fara ji Asmau tana bin Amatullah tana cewa zata shafa mata dettol a wurin da dankunne ya karceta ita kuma tana zagaye gado da gudu. Umma ta rike baki kawai. Asmau da Safinanta sai Allah. Tare suka ga wahalar rayuwa shiyasa shakuwarsu take bawa mutane sha'awa.

Sakin fuska tayi ta shiga ta daga Amatullah.
"Gudu wurin Hajjo kinji yarinyar kirki."

Ta fice kuwa a guje tana dariya. Asmau kunya ta kamata ta ce "Umma kiyi hakuri don Allah".

"Bakiyi min komai ba Asmau. So nake ki fada min abinda yake damunki. Ba'a so damuwa tasa iyaye su rinka hucewa akan 'ya'yansu. Amatullah bata kyauta ba da tayi magana amma ba da haka zaki tsawatar mata ba. Ko don gaba ki kiyaye"

"In sha Allah Umma. Nagode"

Wuri Umma ta samu ta zauna tace "zauna Asmau, magana zamuyi"

Murmushi ta kirkiro "babu komai fa Umma, haushi ta bani ne"

"To na tashi kenan tunda kina da wanda zaki fadawa matsalarki bayan ni"

Daga magana kamar ance fara kuka kawai ta kwantar da kanta a cinyar Umma ta soma kuka. Tausayi ta bawa Umman ta fara rarrashinta "komai yayi tsanani maganinsa Allah. Yakamata ace kece mai fadawa wani hakan. Wa kike nema a waya har abin ya bata miki rai haka"

Muryarta har ta dan shake tace " idan mutum ya dena nemanka a waya sosai alama ce ta ya hakura da kai ko, ko kayi masa laifi"

Duk da Umma tasan wa Asmau ke so sai tace "waye baya kiranki a waya"

Rufe bakinta tayi da sauri. Maganar ce take cinta amma bata yi niyar fada ba.

Dan murmushi Umma tayi. Tun ranar da suka hadu da su Hajiya a asibiti kafin Anti Bintu ta koma Zariya ta fada mata yadda suka yi da Col. Ishaq. Ta sauke ajiyar zuciya
"Ishaq ne baya kiranki?"

Sake sunkuyar da kai tayi ta kasa amsawa. Umma tace "ki yawaita addua da neman zabin Allah nima zan tayaki."

Abinda yake ta cin ranta ta kasa boyewa "cewa yayi zaiyi magana da Hajiya, ina jin saboda Amatullah bata amince ba. *Umma nayi kuskure ne da ban zubar da cikin ba na haifeta*?

Wannan karon Umma ma sai hawaye "ko kadan Asmau. Haihuwarta shine maslaha gareki damu baki daya. Mun so bin son zuciya da muka dage sai kin zubar da cikinta. Ki duba ki gani yadda Allah Yayita mai kokari da ladabi. Kema kinsan ba iyawarki bace kawai tasa kike da yarinya mai tarbiya kamarta. Mata da yawa da iyayensu sukan gujewa kunyar duniya su zubar da ciki ko a yar da jariri. Sai anje lahira kuma ido ya raina fata. Ga laifin zina ga na zubar da ciki ko kashe jinjiri. Ko ki sami miji ko kada ki samu ki sani cewa rayuwarki ibada ce. Hakuri da tawakkali shine ginshikin farincikin dan adam. Batun Ishaq kuma kada ki damu zai nemeki da kansa ku kare magana. Da shi da Qasim wanda duk Allah Ya zaba miki ko waninsu sai mu ce Alhamdulillah.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽47

Batul Mamman💖

*Maman Farida mai Hanyar Ruwa. Ina gaisuwa da fatan alkhairi. Ga naki shafin yar uwa*

*Amina Yau, Jikamshi yana gaisheki da kyau.*

*Shafaatu mai masaukin baki a gidan Batul ina godiya*

*Masu sakonnin gaisuwa bazan taba mantawa daku ba. Allah Yayi mana jagora*

Sai yanzu Asmau ta dan sami nutsuwa a ranta. Tun da Jikamshi ya dena kiranta sosai ta fara tunanin ko Hajiyarsa ce bata amince ba. Amma yanzu Umma ta kwantar mata da hankali. Zata sake nemansa daga yau zuwa gobe. Idan taji shiru to zata bar komai ga iyayenta. A yanzu dai Umma da Mama Yalwa sun riga sun san da maganar Col. Ishaq. Mama har fada tayi da basu fada da wuri ba sai a asibiti ta ganewa idonta. Asmau ta san bazata bar maganar ba dole ta fadawa Baba.

Bayan fitar Umma tashi tayi ta dauko Al-Qur'ani tana karantawa. Neman sauki kawai take a zuciyarta da ke kitsa mata abubuwa da yawa. Adduarta bata wuce idan Jikamshi bazai aureta ba zata mayar da hankali ga karatu, idan kuma iyayenta sun zaba mata Qasim duk da a yanzu sun san bata son shi to bazata yi musu ba. Fatanta bai wuce ta sami juriya wurin karbar duk wata jarabawa da tazo mata ba.
*****

Washegari Umma ta gama shirin zuwa gidan Mama suyi magana ta karshe da Alh Adamu sai ga Garzali ya shigo yana ta fara'a suka hadu a bakin kofa. Umma tace "kanina mijin 'yata irin wannan fara'a haka. Ko dai Zubaida ta haihu"

Yana murmushi yace "yanzu daga asibitin nake. Ko awa daya bata yi ba. An sami namiji."

Umma sai murna ta koma ciki tana mita akan me bai fada musu ba tun lokacin da suka tafi asibitin. Sai da suka je dakin Hajjo bayan ta fada mata kyakkyawan labari tace "ina kuka kai su Walid?"

"Kai Yaya Bara'atu sai faman fada kike yi. Tsakar dare fa ta fara nakudar. A makota na ajiyesu muka tafi."

Asmau ce ta shigo dakin daga kitchen bayan taji muryar Kawu Garzali. Tayi murna sosai tace bari ta dora ruwan zafi sannan ta hada abinci. Kawu Garzali yace ta barshi makociyarsu duk tayi wannan. Yana jin bazata dade ba za'ayi sallama. Tace to bari tayi wanka sai su tafi. Tana tafiya Umma ta soma fada masa halin da suke ciki ga Qasim kuma da yake jira a sake basu lokaci. Hajjo tace
"Allah mai iko, wallahi idan aka ce min yarinyar nan zata sami manemin aure sai in karyata. Gashi yanzu an samu har an rasa na zabe. Ni dai shawarata kada ayi mata dole. Yaron nan Qasim dan mutumci ne gaba da baya amma bana son ayi auren dana sani. Asmau ba kankanuwar yarinya bace da zaa ce bata san me take yi ba. Kai Garzali mu zamu je asibitin. Kaje ka sami Alhaji kuyi magana. Idan za'aji ta bakin Ishaq din ne ya kamata a hanzarta. Idan kuma da Qasim din ne ma duk yadda akayi babu matsala."

Umma ta dan sassauta murya tace "Bintu fa ta fada min shi Ishaq din yace ya janye saboda baya haihuwa."

"Baya haihuwa?" Hajjo ta fada tana daga murya.

Umma tace "Asmau bata sani ba. Yace zai fada mata da kansa. Nima ban nuna mata na san wani abu ba"

Kawu Garzali ya shiga jimami. Zubaida ta fada masa irin yadda ta ga Col. Ishaq da Asmau suna son juna ranar da taje yini a gidan. Anya akwai ranar da Asmau zata ga haske a rayuwarta kuwa. Daga wannan matsalar sai wannan.
"Wai ya taba aure ne ko tuzuru ne shi Ishaq din"

"Kaima dai Garzali in bai taba aure ba yaushe zai san da matsalar rashin haihuwar. Shekararsa shadaya da matarsa ta farko"

Gefen gado Hajjo ta samu ta zauna "ni dai kaina duk ya kulle. Haihuwa ba abin wasa bace duk da mutum baya bawa kansa amma kowa yana so. Muje dai wurin maijegon, kai kuma duk yadda kuka yi da Alhajin ka fada mana. Ai ita shawara tana da dadi. Bana son azo ana cizon yatsa nan gaba shiyasa cikinsu babu wanda zan ce lallai sai ta zabe shi."
*****

A nan suka bar zancen su Umma suka wuce asibiti daukar Zubaida. Kawu Garzali ya tafi gidan Alh Adamu.

Bayan sun gaisa ne Alhajin yace "ina Hajiya Bara'atun? Tace zata zo. Ashe tare ma kuke"

"Ni kadai ne Alhaji. Sun tafi asibiti mai dakina ta sauka dazu bayan asuba"

Barka Alh Adamu yayi masa sannan suka fara tattauna abinda yake gabansu. Zancen Col. Ishaq ma sai da Alh Adamu yayi ya ce Mama ce ta fada masa. Ashe shiyasa yaga shi da mahaifiyarsa da 'yan uwansa sun zo duba Amatullah. Daga Shanono kuma jiya ya sami waya suna bukatar a sake basu lokaci.

"Alhaji wannan abu duk mai sauki ne. Yanzu nake ji cewa shi Ishaq din yace zai janye saboda yana da lalura ta rashin haihuwa. Idan haka ne kaga Qasim ya kamata ta aura"

"Banki taka ba Garzali. Duk abinda aka riga aka sani yafi sauki idan za'a tunkare shi. Amma menene tabbacinmu na cewa shi Qasim yana haihuwa ko ita Asmau zata sake haihuwa? A zahiri nafi sonta da Qasim saboda kusancinsa da Abubakar. Gani zanyi kamar dana ne ya aureta. Sai dai kuma bana son mu saka son zuciya a cikin al'amarin nan. Tana gida ne yanzu?"

"A'a tare suka fita dasu Hajjo" Garzali ya bashi amsa.

"Idan ta dawo kace ina nemanta jibi bayan azahar in sha Allah. Zan je daurin aure ne gobe Gashua. Tambayarta zanyi don kada abin yazo da daukar alhaki. Wanda ta zaba sai mu duba mu kuma muga dacewar hakan. Aure ai ba'a yi masa garaje. Rashin karasa karbar kudin wancan karon ma daga Allah ne."
Chapter 48 · 0% Book details