← Book details Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 74

Sashe 73

Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Annur ya shafa kansa yana murmushi "idan na sami mata yanzu zanyi aure ko don kare mutuncina amma zancen yarinyar nan ka bari kawai, lokaci ne kawai zai nuna mana"
*****

Bikin Qasim ya matso sai da Hajiya ta shiga zancen Col. Ishaq ya yarda Asmau taje. Dama makaranta ma ya roketa alfarmar ta bari sai wata shekarar bayan ta haihu. A gidan Mami zasu sauka harda Bilkisu da Amatullah zasu tafi. Su Umma suma zasu je da Mama. Sunyi mota biyu lokacin Yassar yazo hutu daga NDA inda Col. Ishaq ya sama masa yana yin short service. Shine zai tuka motarsu Asmau shi kuma dreban gidan Mama Yalwa ya tuka su ita da Umma da Shemau.

Ranar da zasu tafi Asmau kamar bazata fito daga gida ba. Jikamshi ya makale mata sai mita yake zata tafi ta barshi. Ga dokoki ya kafa na kula da ciki. Ba don sai an kawo amarya Qasim ya shirya dinner a cikin Kano ba ai da binsu zaiyi ma. Sun rabu ana kewar juna suka je suka shiga mota.

Yassar ta kula baya magana sosai a motar har tana tsokanarsa ko sababbin sojoji basa magana ne. Bai ce komai ba sai Bilkisu da ta sha kunu a gaban mota tace "Anti Asmau ko zaki tambayar min su Umma na koma motarsu"

"Wani abin ne ya faru kike son canja wurin zama?"

Shiru tayi sai kuma ta soma hawaye. Nan da nan hankalin Asmau yayi mugun tashi. Shi kuwa Yassar hannunsa rawa ya soma yi ya sami gefen hanya yayi parking din motar. Asmau tana ta tambayar me akayi mata sai ji tayi Yassar yace "Bilkisu"

Ta dago kai idanunta sun kumbura sunyi jawur.
"Idan ba cewa zakayi kana sona ba ka rabu dani. Allah zai bani wani"

Asmau ta hangame baki cike da mamaki. Rashin kunya a gaban masoyi ta yarda gadon gidansu Jikamshi ne. Anya Bilkisu bata manta tana bayan motar ba. Allah Yasa ma Amatullah tayi bacci.

Yassar yace "kema kinsan ina sonki don Allah ki share hawayen kinga a hanya muke"

Ta murguda masa baki "a haka ne kana sona tunda ka tafi ba waya ba text sai na gaji na nemeka. Kuma kaki fadawa kowa balle a fara shirin bikinmu sai iya zuwa bikin wasu"

Asmau ta shiga tafa hannu a hankali tace "Bilkisu kwantar da hankalinki naji komai muna dawowa in sha Allah magana zata je gaba kinji ko. Kinsan Yassar din ne akwai tsoron mata"

Dora hannu Bilkisu tayi a kanta tare da jan mayafi ta rufe fuska. Wallahi ta manta da Asmau a motar. Haushi Yassar dinta ya bata tun bikin su Asmau da ta samu yace yana sonta bai kara waiwayenta ba.

A nasa bangaren shima wata matsananciyar kunya yaji. Ko Bilkisun ba don baya sonta yake kin nemanta ba. Shi bai san me zai rinka fada mata ba a waya ko text. Shiru suka yi su biyun Yassar ya tayar da mota Asmau tana ta dariya. Abu yayi dadi zumunci zai kara kulluwa tsakaninsu. Tsabar murna a lokacin ta turawa Jikamshi text tana fada masa. Shi dinma ya nuna farincikinsa sosai yace sai sun dawo. Bilkisu dai har aka isa Jos bebiyar dole ta zama.

Ansha biki Zulaiha ta sake bawa Asmau labarin yadda suka kare dasu Zinaru dama ta sanar da ita a waya. Asmau tace ina ma tana wurin ta ga idanun Zinaru mai son kudin tsiya. Daga nan suka koma hirar cikin Asmau da kuma Alh Najib da yake jiran Zulaiha ta gama iddah. Ita dai tace bata da ra'ayin aure tasha wahala a wancan ga yara har shida waye zai dauketa tare dasu. Shawara Asmau ta bata kada ta bari dama ta kubuce mata wurin yiwa babanta biyayya.

Ranar Asabar da sassafe suka dauko amarya suka taho Kano da ita. Washegari akayi dinner sannan aka wuce da ita Shanono inda zatayi sati sannan su tafi Zamfara da angonta.

Ranar da suka dawo Col. Ishaq kamar ya cinye Asmau. Kwanaki uku kawai ji yake kamar ya dade sosai basa tare. Itama tayi kewarsa domin kuwa duk kulawar da take samu bata kai tasa ba.
*****

Cikinta na da wata shida ya fara siyayyar kayan baby. Wani lokacin yaje da ita wani lokacin kuwa sai dai taga ya shigo da kaya. Tun daga gadon yara (cot), kayan sawa da duk wani abin amfani ya tanada. Ita har gajiya tayi da cewa ya barsu haka. Mutum mai shekarunsa zaiyi haihuwar fari sai dai a zuba ido.

Wata rana ya dawo daga aiki a gajiye yake fada mata ta hada kaya jibi zasu tafi Port Harcout an tura shi aiki na wata daya. Amatullah sun fara hutu sai a kaita gidan Umma kafin su dawo. Asmau ta zauna ta hada musu kaya washegari suka kai Amatullah gidan Umma sannan suka je yiwa Hajiya sallama.

Tunda ya fara bayanin abinda ya kawo su Hajiya ta dakatar dashi.
"Babu inda zaka je min da ita da wannan cikin. Wa kuke dashi a can da zaka kaita cikin arna ka ajiye. Idan haihuwa tazo yaya zaku yi?"

Yace "Hajiya akwai musulmai kuma da sauran lokacin haihuwar har maje mu dawo"

"Kasan Allah babu inda zata je. Ko dai ka fasa tafiyar ko kuma ita ta zauna a nan ko can hotoro. Wannan karon ba kyaleka zanyi ba irin yadda ka tabayi min har na bari kuka koma gida"

Asmau kanta na kasa Col. Ishaq yaki shiru don ba karamar cuta bace gareshi tafiyar wata daya babu matarsa. Hajiya ta dage harda kiran Umma. Itama Umman tace abinda ta gani kenan da suka kai mata Amatullah sai dai batayi magana ba. Hajiya tace ta gama magana shawara na garesu. Jiki babu kwari suka tafi gida.

Asmau tayi ta bashi baki akan yayi hakuri ya dena nuna bacin rai amma ya kasa.
"Matar Jikamshi wata daya ba sati bane. Ta yaya zanyi kwanakin nan ni kadai bayan na riga na saba da yin komai tare dake"

Idonta na shirin zubo da hawaye tace "kayi hakuri kaima kasan abinda ta fada domin amfaninmu ne. Bazaka iya fasa tafiyar ba? Wallahi bana son kayi min nisa"

Kuka ta soma yi ya rungumeta "bani da yadda zanyi ne. Umarni ne daga sama"

A ranar ko kadan basuyi bacci ba sai aikin rarrashin juna. Tayi ta masa kuka har muryarta ta dashe. Bayan ya dawo daga sallar asuba ya hada mata kaya a wani akwatin. Ko abincin kirki sun kasa ci haka suka fita ya kaita gidan Umma ya wuce office. Daga nan dreba ya kaisu airport su hudu suka tafi. Harda Hussaini wanda idan sun dawo za'ayi bikinsa da Walida.

Sai da ya kusa sati sannan ta warware ta dena zaman daki. Umma tayi dariya kawai. Safe, rana da dare aiki yana yi masa sauki sai waya. Kafin su kwanta kullum sai anyi video call yana kallonta da cikinta da kuma princess dinsa.
****

Kwanci tashi saura kwana biyu ya dawo gida. Ita da Sabira suka je ta tayata gyaran gidan domin tayi nauyi sosai. Harda kitso da kunshi Jikamshi zai dawo. Ranar da zai dawo kuwa karfe tara na safe ta gama shiri zata tafi gida. Umma ta rinka ja mata rai tana dariya a ranta yadda Asmau take ta kallon agogo. Sai goma da rabi ta fito ta ajiyeta a gida ta wuce office. Amatullah tana gidan Nasiba tana karasa hutunta.

Karfe daya taji motarsa ta bude kofa da sauri. Col. Ishaq ya tsaya yana kallonta. Ciki yayi girma sosai. Ita ma shi take kallo har wani jiki ya danyi ta fasa rungumeshi taja da baya. Rufe kofa yayi yana binta "haba Matar Jikamshi kada kiyi min rowar kanki. A tausayawa bawan Allah"

"Shine kayi kiba duk da baka gani na ko"

Ya janyota yana murmushi "yau 'yan rigimar suna kusa ne? Bayan wata daya not even a kiss sai korafi zan samu. Bari na koma tunda bakiyi murnar dawowata ba"

Kin sakinsa tayi ta rungumeshi sosai tana kuka "bazaka kara tafiya irin wannan ka barni ba. Kullum da kyar nake bacci"

Yayi kissing dinta yana kallon fuskarta "na sani my sweet Asmau. In sha Allah next time kafata kafarki."

Daki suka je zai shiga wanka yaga tana dan runtse ido ya tambayeta ko meye tace kafarta ce ta dan rike. Ranar sallah kawai ke fitar dashi daga gida. Kowa yana kokarin nunawa dayan irin yadda yayi kewarsa. Makale suke da juna kamar ranar aka kawo masa ita. A haka kuma tana ta dan jin ciwo daga mararta zuwa baya amma tana cijewa don tasan akwai wurin sati uku kafin lokacin haihuwarta.

Cikin dare suna bacci taji ciwon ba mai daukewa bane ta tashi ta fita a hankali. Ita kadai take ta kai kawo a falo ciwo yana ta gaba gaba har taji tafiya tana neman gagararta. Da jan kafa ta dawo dakin ta zauna a bakin gado. Sai da ta zauna ta fara cewa "Jikamshina" ta kira sau uku yana baccinsa. Wani ciwo taji sosai bata san lokacin da tace
"ISHAQ" da karfi ba.

Tashi yayi ya rasa daga ina take kiransa. Ciwo yayi ciwo ta sake cewa Ishaq, fitila ya kunna ya ganta a bakin gado sai gumi take. Ya rude sosai yace me kike yi a nan.

Tambayar ma haushi ta bata ta cije dai tace "nakuda nake"

Rigarsa ya nema ya saka ya fara neman mukullin mota. Ciwo na cinta tace "Jikamshina bazan iya tashi ba. Haihuwar ta matso. Ka dauko sabuwar reza a waccan drawer din"

Ya zaro idanu a tsorace "inyi me da reza?"

Tana wash wash tace "yanke cibiya"

A take jikinsa ya fara rawa.
"Kiyi hakuri na kaiki asibiti don Allah kada ki haihu a gabana wallahi bazan iya gani ba suma zanyi. Ko ta awaki bana son gani" yadda yake maganar kasan a tsorace yake sosai.

Durkushe yake a gabanta ta daure ta rike masa hannu "Jikamshina kafin muje asibiti ko wani yazo zan iya haihuwa. Ka daure ka duba min ko baka son baby din"

Jikinsa a sanyaye yace "ina so"
Chapter 73 · 0% Book details