← Book details Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 74

Sashe 45

Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kukan Bilkisu suka ji Hajiya ta tashi da kanta sai dai kafin ta fito Bilkisu ta koma dakinta tana kuka. Bata taba sanin wannan labarin ba. A iya tunaninta baban Amatullah ya rasu ne ko ya saki Asmau. Tsoro ne ya kamata saboda akwai wani saurayinta da suke chatting a facebook. A hankali ya fara sako mata zantukan banza tun bata amsawa har ta dan fara sakewa yanzu. Wai har ya iya tambayarta ta kwatanta masa kayan baccinta da daddare. Tayi saurin dafe kirji, yanzu idan da abin yayi nisa kila itama ta shiga sahun masu bawa samari jiki. Kuka take sosai tana tausayawa Asmau kuma har ranta tana fatan Uncle Ishaq ya aureta ko don ya rufawa rayuwarta asiri. Sabon saurayin da suke dan satar kallon juna dashi ta kira a waya tana sheshshekar kuka. Numbar ma a wayar Uncle ta dauka batare da saninsa ba. Da sallamarsa ya dauka cikin muryar da ta dashe da kuka tace "Yassar ne?"
ABINDA AKE GUDU🙆🏽45

Batul Mamman💖

Mamaki ne ya kama Yassar, kamar ya san muryar amma bashi da tabbas.
"Da wa nake magana don Allah?"

"Bilkisu ce"

Tsorata yayi, shima yana neman numbarta amma yanzu da ta kirashi da alamun kuka sai yaji hankalinsa ya tashi.
"Bilkisu me ya faru?"

To me kuma zata ce masa? Tausayin kawunta take yi amma tana tsoron yi masa shishshigi. Uncle Ishaq yana da dadin sha'ani amma babu mai son ganin bacin ransa. Fasa maganar tayi na son ta roke shi ya lallaba yayarsa kada ta ki Uncle dinta tace "babu komai, anjima zamu zo duba Amatullah" tayi masa sallama ta ajiye wayar.

A ransa yasan don zasu zo ba shine dalilin kiran ba. Tashi yayi ya shirya ya tafi asibitin. Zai jira su zo ya sami damar tambayarta. Ko dai ta lura da yawan kallonta da yake yi ne? Yayi murmushi, tun zuwansa gidansu na farko ranar da kare ya biyo Asmau ya fara jin wani abu game da Bilkisu. Sai dai duk hayaniya ta Yassar bai taba yin budurwa ba. Ta nan bangaren tsoro ne dashi kamar farar kura.
*****

Col. Ishaq na shiga dakinsa ya fada kan gado ko takalmi bai tsaya cirewa ba. Kansa ne yake wani irin ciwo kamar ana buga masa kusa. Ga zuciyarsa ta gama tafasa da bacin rai. Wai yau shine kannensa har da Mussadiq dan karamin cikinsu suke fada masa magana son ransu. A gidansu akwai tsari na girmama na gaba sosai. Sun tashi da so da kaunar juna. Lalurar kowa tare suka haduwa suyi maganinta. 'Ya'yan Ismail biyar duka maza karamin ma bai shekara ba. Amma saboda yadda suke bashi girma duk shi yake sakawa yaran suna. Haka yaran Dahiru guda uku. Gidansu gwanin sha'awa baka ce babansu ya dade da rasuwa ba. Amma yau akan auren Asmau duk sun ture wani girmamawa da shakuwa kowa ya fadi son ransa. Da akanta kadai suka tsaya ya tabbatar da har yanzu yana dakin suna cacar baki. Sai gashi saboda irin rayuwar Asmau ta baya har gori Ismail yayi masa. Gori da abinda yafi so a rayuwarsa, haihuwa. Shi da kullum yake kwantarwa da yayansa hankali. Kafin rabuwarsa da Badariyya ma yaransa biyu manyan a wurinsa suke. Dumi yaji a idonsa yayi saurin mayar da hawayen dake neman zubo masa. Duniya ta Allah ce kuma ba wurin tabbatar bayi ba. Da ace babu lahira sai yace rayuwar Asmau ta wuce abinda ake gudu domin komai daren dadewa sai an ambaceta ko 'yarta a matsayin mazinaciya ko 'yar zina. Ya tabbatar ko shugabar malaman duniya Asmau ta zama sai kaji mutane suna cewa
"Wance kamar ba ita ce tayi cikin shege ba"
"Ji yadda take nuna mana ita ta Allah ce kamar bamu san tarihinta ba"

Amatullah kuwa ita ma bazata tsira ba. Komai kyawun rayuwarta sai an ce "kaga wance kamar ba shegiya mara uba ba" "wance fa da kuke gani babu aure aka haifeta"
Irin haka da maganganun da suka fisu zafi mutane zasu fada a kansu. Babu ruwan kowa da yaya tsakaninta yake da Allah. Shin ta tuba ko kuwa. Zina ta zama mugun tabo mara gogewa.

Tashi yayi ya zauna tare da daga hannuwansa sama. Hawayen da baya son yi ne suka zubo masa
"Ya Allah Ka karbi tuban baiwarKa Asmau da sauran al'umma da suke cikin hali irin nata. Allah Ka basu rayuwa mai albarka su ji dadin tuban da sukayi bisa laifukansu, Ya Allah Ka bata miji nagari wanda zai zame mata alkhairi kuma mai wanke mata bacin rai da bazata taba dena fuskanta ba a dalilin kuskurenta na baya. Ya Allah Ka karemu da sauran musulmi daga fadawa alfasha kowace iri ce. Amin"

Sai yanzu yaji saukin kuncin zuciyarsa ya tashi zaiyi wanka kafin a kira magariba. Abu daya ne a ransa yanzu, shine hakuri da Asmau da zaiyi. Ba karamin so yake mata ba amma dole ya barta ta auri wanda zata iya haihuwa dashi. Zafin soyayya ya rufe masa ido har ya manta yana da nakasa a rayuwarsa. Tunda baya haihuwa bazai cutar da kuruciyarta ba ta zauna da 'ya daya.

Wanka ya shiga ya fito ya sanya riga da wando na yadi mara nauyi. Ya saka hula kalar adon rigar ya sha turare sai gashi ya fito a Jikamshinsa. Idan ka ganshi bazaka ce yana da damuwa ba saboda tunda yayi adduar nan babu abinda yake sai tasbihi ga Allah. Wannan ne ya saukaka masa damuwarsa yaji kwarin gwiwar niyarsa ta rabuwa da Asmau idan suka koma gida. Kafin ya fito text dinta ya shigo wayarsa. Yaa budewa yaga ta rubuta _missing Jikamshina_. Wani sabon sonta yaji ya ratsa shi. Kasa yi mata reply yayi ya tura wayar a aljihu.

Yana fitowa ya tarar da kannensa jugum a falo domin kuwa Hajiya tana gama basu labarin Asmau tace su fice mata daga daki. Da ya fito duk da ransa babu dadi haka ya basar ya dubi mazan
"Kuzo mu wuce masallaci"

Suka tashi jiki a sanyaye. Mami tace "Yaya don girman Allah kayi hakuri da abinda Ismail ya fada. Wallahi duj don bama so ka auro wadda zata gurbata mana dangi ne"

Suma sauran suka soma bashi hakuri. Ismail kuwa ko kallon yayansa ya kasa yi. Murmushi yayi wanda dukkansu sun san irinsa yake idan ransa ya baci
"Magana ta wuce, bazan auri Asmau ba kamar yadda kuke so. *Amma ba don kun nuna rashin amincewarku bane, don baku isa ba*. Saboda kaddara ta fada mata ba zan ce sai na aureta ba duk da ni din bana haihuwa ko Ismail?"

Ismail ji yayi kamar yayi kuka. Idanunsa tuni sun canja launi. Yayansu yana da kirki matuka, bai san yaya akayi shaidan yaja shi yayi wannan katubarar ba.
"Yaya ka yafe min, wallahi Hajiya yau har zagina tayi bayan fitarka. Yanzu ma cewa tayi zamu rakata asibiti duba yarinyar Asma'un daga nan kowa ya fice mata daga gida. Hatta Mami Hajiya tayi rantsuwa bazata kwana a gidan nan ba."

Col. Ishaq ya kara murmusawa "to ai babu damuwa Mami ga kannenki nan sai kibi daya daga cikinsu ki kwana a gidansa"

Mami ta saki baki don batayi tunanin haka zai ce ba. Tayi zaton zaije ya bawa Hajiya hakuri. Duk sun san bacin ranta yafi karfi akan gorin haihuwar da aka yi masa ne.
"saboda Allah ya zaayi naje gidan kannena na kwana da girmana"

"To bari mu dawo daga masallaci sai na baki key din gidana. Babu datti sosai saboda karshen sati maigadi yana min shara. Sai ki tafi da taki 'yar Bilkisu ta tayaki kwana" yana gama magana yayi gaba kamar bashi ya fada ba. Sun san sun tabo soja yau sai yadda ta yiwu kuma. Bayan fitarsu masallaci Mami da Safiyya suka zauna suna ta magana akan lamarin auren Asmau da kuma karin laifin da Ismail ya janyo musu.

Bilkisu dai shiryawa tayi a daki ta fito ta zauna jiran zuwa asibiti don tasan dole aje da ita tunda mai aikinsu bata nan.

Tare suka dawo daga masallacin su Dahiru suna ta bashi hakuri ya nuna musu komai ya wuce. Wurin Hajiya ya je ta shirya ita ma tace motarsa zata shiga su tafi.

Suka fito falo Bilkisu tabi bayansu suma sauran suka fito. Bilkisu na gaban motarsa Hajiya a baya Safiyya tazo ta kama daya kofar zata bude ya juyo ya watsa mata harara ba shiri ta saki kofar.
"Ki koma kibi motar 'yan uwanki masu haihuwa. Ni Hajiya zan dauka da 'yata."

Tayi saroro tana kallonsa. Dahiru da yaji ya dan matso wurin motar "Yaya don Allah kayi hakuri ka manta da zancen nan. Kuma ka yarda ta biku ko Mami ta shigo. Kaga sai ayi saving din mai mu tafi da mota biyu"

Col. Ishaq ya wani kankance ido ya kalli Bilkisu "toshe kunnenki kinji mai gadon zinare" ta kuwa tura yatsu a kunne tare da sunkuyar da kanta.

Hajiya tasan karshenta wata maganar mara dadi zai yabawa kaninsa tace "a gaban 'yarku zaku nuna min hali ko, kai kuma Dahiru kusan yadda zakuyi ku taho"

Col. Ishaq ya mayar da kansa ciki albarkacin Hajiya suka ci. Dole mota biyu suka yi don daya zata matsesu saboda Dahiru da Safiyya duk akwai jiki.

Yana soma tuki Hajiya tace "kai"

"Naam"

"Kayi hakuri da abinda suka yi maka don Allah kada kuyi min gaba. Aure kuma da kaina zan sami kakar Asmau muyi magana in sha Allahu. Tun farko na fada maka dole zaka fuskanci kalubale ta ko'ina saboda wannan abu fa ba wanda ake iya saurin kawar da kai bane a kansa. Ni dai ina sonta kuma na baka goyon baya ka nemi aurenta. Allah mai yawan gafara ne da jinkai. Idan bama iya kawar da kai ga kuskuren mutane to bamu san da wane laifi mu kuma Allah zai kamamu ba"

Allah Sarki Hajuyarsa akwai zurfin tunani.
"Hajiya nagode sosai amma ki bar maganar auren. Asmau bata cancanci ta kare rayuwarta bata haihuwa ba. Nima daga yanzu bana fatan kara neman aure. Mu bari kawai tabi shawarar iyayenta a zauna lafiya."
Chapter 45 · 0% Book details