← Book details Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 74

Sashe 43

Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya gyara tsayuwarsa yana fuskantar ta "ki dena kukan nan kinji ko. Idan nace miki everything is ok nayi karya because it is not. Kinji kunyar sanar da Qasim da wuri kinga abinda hakan ya janyo. Magana kuma tunda ta hada da iyaye zan hakura kamar yadda kike so. Dazu ma naga ya kamata ya sani ne shiyasa na fada masa."

Wani kukan ne yazo mata sai zubar da hawaye take. Tana sonsa fiye da yadda take tsammani a baya.
"Jikamshi to yaya zanyi?"

Tausayi ta bashi. Asmau ta fuskanci abubuwa da dama a cikin 'yan shekaru.
"Da ace babu ni a cikin manemanki sai na baki shawara. Amma tunda ina ciki bana so a zargeni da son kai. Shawara tana gareki Asma'una. Idan Allah Yayi Qasim ne mijinki alfarma daya nake nema kada ku rabani da Safina. Atleast ko school fees dinta ku bari ya zama responsibility dina."

Meyasa Qasim bai sanar da ita iyayensa zasu zo da wuri ba. Ji tayi gabadaya auren ya fice mata a rai. Kuka kawai take yi mai ciwo. Muryarta a shake tace "To yanzu shikenan?"

Murmushi yayi mata, sai da taji shi har ranta. "Shikenan Matar Jikamshi. Maybe daga yau bazan kara kiranki da wannan sunan ba. Ki rike duk abinda Allah Ya kaddara miki da hannu biyu. Qasim mutumin kirki ne a yadda na fahimce shi. Ban taba ganin mutum mai kokarin rike amana kamarsa ba"

"Na sani wallahi, shiyasa na kasa fada masa gaskiyar abinda ke zuciyata. Ina gudun bata masa rai saboda nasan duk abinda yake yi don ya kyautata mana ne."

"Kada kiyi ja in ja da iyaye akansa. Idan shine alkhairin rayuwarki bamu da zabi da ya wuce karbar kaddara."

Juya mata baya yayi zai tafi. Yana jin sautin kukanta ya karu. Yasan yana sonta ba da wasa ba, amma duk abinda aka ce iyaye sun shiga ciki a matsayinsa na babba bai kamata ya nuna mata bijerewa alkhairi bane. Duk da kuwa yana ji a ransa kamar gobe ya turo nasa iyayen. Asmau ta wuce a kirata wani bangare na jikinsa. Shine ita, itace shi. Da haka kawai zai iya kwatanta kaunar da yake mata.

A sanyaye yaji muryarta yadda bata zaton zai ji tace "Jikamshi ina sonka" a hankali

Wannan kalmar ta tsaya masa sosai a zuciya har ya fasa tafiya. Sake juyowa yayi ya ganta durkushe tana kuka. Shima durkusawa yayi a gabanta suna fuskantar juna "Matar Jikamshi kina so na hakura dake"?

Girgiza kai tayi tana fitar da hawaye mai dumi.

"To bazan hakura ba. Jikamshi yana son matarsa. Ki tashi ki koma ciki. Gobe in sha Allah zanyi magana ta fahimta da Hajjo tunda ita ce babba. Zan fada mata bazaki iya rayuwa da kowa ba sai Ishaq. Nima da ke kadai nake son karashe rayuwata. Duk shawarar da ta bayar da ita zanyi amfani."

Tana hawayen amma murmushi take yi tana kallonsa. Yayi dariya "to dena kallona haka kada ki cinyeni kafin a daura auren"

Ta sunkuyar da kanta kasa cikin kunya. "Ba fa kallonka nake yi ba."

"Kallo na nawa kuma, a ciki ma ko kunyar Hajjo baki ji ba kika rinka satar kallona. Anya yarinyar nan baki fi karfina ba. Da ina yi miki kallon saliha amma yanzu ajinki daban ne"

Murmushi kawai tayi ta rufe fuskarta da tafukan hannuwanta tace "zama da kai ne"

"Indai nine baki ga komai ba. Kinga koma kada a fara cigiyarki. An saba maza ke zuwa zance amma yau kin kasa hakuri kin biyo ni. "

Sai da ya rakata har kusa da dakin sannan ya dawo. A daidai inda suka gama magana yaga kamar alamar mutum. Ya dan juya yaji shiru sai kawai ya tafi.

Qasim ne a wurin kuma duk yaji maganganunsu. Tun bayan fitowar Asmau ya biyo bayanta a zatonsa Col. Ishaq ya riga ya tafi. Rasa inda zaisa kansa yayi saboda a yau ya tabbatar ko kadan bata yi masa soyayya irin wadda yake fata. Duk wani tunaninsa ya kulle a yanzu shiyasa kawai ya shiga motarsa ya bar asibitin.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽44

Batul Mamman💖

A daren nan Qasim ya wuce Shanono. Abin duniya duk ya ishe shi. Dama wani lokacin baka sanin kana son abu sosai sai kaga alamun zaka rasa shi. Da gaske yake jin kaunar Asmau a ransa. Tunani yake har me ta gani a tattare da Col. Ishaq take sonsa haka. Yasan mutumin dai ya hadu amma ko babu komai shi Qasim ya fishi kuruciya. Duk da bai san komai game da Col. Ishaq ba amma yana da tabbacin da wuya idan bashi da mata daya ko sama da haka. Shi da yake da burin bata dukkan kulawa ta yadda babu wata mace mai suna kishiya da zata takura mata shine zata kai kanta cikin mutanen da basu dade da sanin juna ba. Yanzu idan ta aure shi danginsa suka wulakanta ta fa? Hawaye yaji yana neman zubo masa. Duk laifinsa ne da ya zama mugun aboki ga Abubakar. Ba don shawarar da ya bashi ba ai da haka bata faru ba. Ko Abubakar ya rasu ya tabbatar duk inda tayi aure zata tsira da mutunci da martabarta. Sai kuma tausayinsu da yaji. Asmau tayi masa halacci da har bata kalli tsabar idonsa ta nuna masa bata son shi ba. Yayi dan murmushi, dole yasan yadda zaiyi ya janyo ra'ayinta gareshi tare da nuna mata illolin da auren wanda basu gama sani ba zai iya jawo mata. Idan kuma hakan bai samu ba......kasa karasa tunanin yayi.
*****

Col. Ishaq yana zuwa gida ya kira Asmau. Jin wayar a kashe yayi dan murmushi. Ya fuskanci tana cikin matan da basa bawa waya mahimmanci. Yau ta kashe gobe tace wayar tana daki ne. Sai da yayi wanka yaci abinci sannan ya tafi dakin Hajiya.

A zaune ya sameta a kasa Bilkisu tana matsa mata kafafu. Ya zauna a gefenta ta dan janye jiki ita a dole ga dan fari. Dariya Bilkisu tayi ya rankwasheta a ka don yasan tsokanar Hajiya take yi, sannan ya fuskanci Hajiyar.
"ciwon kafar ne ya tashi,akwai maganin ko ya kare?

"Na sha ma bayan naci abinci dazu. Yau ina ka tsaya daga cewa zaka ganin abokinka"

"Asthma din Safina ce ta tashi suna asibiti an kwantar dasu."

Cikin tausayawa Haj Lubabatu tace "Allah sarki, ciwon yaro babu dadi bare ciwo irin wannan. Da ka fada mana tun dazu ai sai Sabo ya kawo mu kafin ya tafi gida. Ya kamata su hada mata da maganin gargajiya, zan tambayi Kawunku suna masana a bangaren. Kasan ciwon yana bukatar kulawa"

Yaji dadin yadda mahaifiyarsa ke nuna damuwarta akan abinda yake so duk da bata son fada. Bilkisu yasa ta tashi hado masa abinci ya samu ya sanar da Hajiyan duk abinda ya faru a yau bayan zuwansa asibiti. Haj Lubabatu ta kalle shi cikin damuwa
"Yanzu kai bazaka hakura da ita ba tunda iyayenta sun fi son wancan yaron?"

"Hajiya itama bata son sa. Kuma don ban gabatar da nawa magabanta bane da wuri. Kin sanar da su Kawun kuwa?"

Ta girgiza kai tana mamakin wannan soyayya da danta yake yiwa Asmau.
"Na fada musu don Yaya Auwalu ma yace zai kiraka kuyi maganar. Ni dai bana so azo a sami matsala daga iyayenta gara kawai tunda har an fara batun kawo kudi ka janye."

Dan murmushi kawai yayi "Hajiya idan kina kyamar aurena da Asmau ki fada min. Nasan hakan zai iya zuwa ranki saboda irin yanayin data tsinci kanta a baya. Kin sani duk yadda nake son abu bazanyi batare da izini da neman albarka daga gareki ba"

Akwai shi da iya tsara zance da ladabi shiyasa take sonsa.
"Ko kadan bana kyamar aurenku. Kuma ni wacece da zanki karbar kaddara. Ka sani babu wata uwa a duniyar nan musulma da zata ji farat daya hankalinta ya kwanta idan danta ya nemi auren macen da ta taba haihuwa a wajen aure. To amma kowa da abinda Allah Ya tsara masa. Yarinyar nan kana ganinta kasan ta fito daga gidan tarbiya sai gashi tsautsayi ya fada mata ta tsinci kanta a irin wannan yanayin. Bazan ki ta ba don da Allah Yaso da daya daga cikin nawa 'ya'yan za'a buga misali. Idan Asmau matarka ce fatana Allah Ya baku zaman lafiya da hakuri da juna"

A take fargabarsa na kin amincewarta ta gushe daga zuciyarsa. "Nagode Hajiya Allah Ya kara lafiya. In sha Allah zan nemi Kawu Auwalun idan ya bukaci naje Jikamshin sai naje. Ina so su zo da wuri ne."

Yanaa tashi Bilkisu ta shigo da abincin ta ajiye a gabansa tana murmushi "Uncle albishirinka"

"Goro maigadon zinare"

Ta danyi tsalle kamar karamar yarinya "gobe Mami zata zo"

Dena zuba lemon da yake yi yayi yace "da gaske" fuskarsa na nuna farincikinsa.

Hajiya tace "to sarkin surutu. Ke da tace kada ki fada masa sai da ya ganta kika fasa kwan saboda kina murna mamanki zata zo ko?"

Bilkisu ta turo baki "kai Hajiya nifa ba haka nake nufi ba"

Col. Ishaq yace "Hajiyar tawa kike turawa baki. To na mayar da goron albishir din banji abinda kika fada ba"

Tashi tayi ta bar dakin tana buga kafa yana mata dariya. Ya juya ga Hajiya cikin murna "gara tazo taga yayarta kuma kanwarta"

Mami ita ce 'yar Haj Lubabatu ta biyu. Shekara daya da rabi Col. Ishaq ya bata. Ba karamin shakuwa suka yi ba kamar ba sako da sako ba. Komai nasu tare suke yi. Hatta zancen Asmau ya fada mata ya sami wadda yake so amma sai tazo Kano ko shi yaje Jos din zasuyi maganar sosai. Ita kanta murna da doki ya isheta saboda ta matsu yayi aure. Tun bayan rabuwarsu da Badariyya bata kara jin yayi zancen mace ba sai yanzu.
******
Chapter 43 · 0% Book details