← Book details Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 74

Sashe 54

Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da suka gama kukan ne suka bawa juna labarin irin gwagwarmayar da suka sha. Walida tayi murna da jin zancen auren Asmau sannan tayi ta kallon hotunan Amatullah a waya tana mita ba'a zo mata da ita ba. Itama ta bawa Asmau labarin irin takunkunmin da babanta ya saka mata saboda jin labarin cikin Asmau. Karshe ma ko karatun jami'ar bai bari ta kammala ba yace sai tayi aure. To gashi shekaru shida babu auren babu karatun sai zaman gida da zuwa islamiyya. Matar gidan ta sami yadda take so wurin fadawa Walida maganganu sai dai ta dena ramawa saboda yanzu babanta bai damu da lamarinta ba. Indai ba aure tayi ba shi baiga amfaninta ba. A wannan zaman gidan kannenta biyu 'ya'yan Anti sunyi aure har sun haihu. Bata yawo daga islamiyya sai gida sai kuma abinda ya zama dole. Samari kuwa kamar anyi ruwa an dauke. Babu mai zuwa yanzu.

Asmau tace "dukkanmu munga irin abinda ake gudu a waya da social media. Allah kara rufa mana asiri duniya da lahira."

"Amin Asmau, amma ai kinfini ganin tashin hankali. Kullum ina miki addua Allah Yasa kada rayuwarki ta lalace da kika bar gida. Da farko a social media na fara watsa hotunanki cigiya kafin Baba ya karbe wayar. Rabona da wayar arziki na manta"

Yini suka yi suna hira sai bayan laasar lokacin da Asmau ta tabbatar an gama taron gidansu tayi haramar tafiya. Jikamshi yayi mata waya yace to ta fara shiri sauran kadan fa ta karasa zama matarsa yana fatan za tayi shiri mai kyau kafin zuwan lokacin. Yaso zuwa daukarta ma da kansa amma kamar yadda suka faro da bin komai yadda ya kamata sai ya hakura. Wani lokacin ko babu social media idan budurwa da saurayi suka kebe su kadai a mota sanyin AC yana dan ratsasu sai shaidan ya fara kawo musu hari. Ko kadan babu burgewa kice wai duk inda zaki saurayinki shine yake kaiki ya dauko ki. Ki duba da kyau kiyiwa kanki adalci watarana ko dan yaya sai anyi abinda bai dace ba ko da kuwa taba hannu ne. Yau da gobe ai tafi karfin wasa.
******

A cikin wata daya Col. Ishaq ya dage sosai ana ta gyaran gidansa. Duk inda yake bukatar canji kamar kayan cikin toilet irinsu baho da sink an canza an saka komai sabo. Haka ma a kitchen da su kofa. Ga fenti sai da ya kira Asmau ta fadi irin kalar da take so. A bangarensu ma Umma ta tashi tsaye sosai. Daga Asmau yanzu babu kowa a gabanta sai Yassar. Su Shemau ne suka je suka gano gidan aka zo aka fara siyayya. Dole ita ma ta dage ta fito da 'yarta ta. Gado ma ready made ta siya guda biyu tare da sauran kayan gida. Shemau, Jafar, Kawu Garzali da gidan Mama duk ba'a barsu a baya ba. Kowa akwai abinda ya dauki nauyi don ganin cewa Asmau ta sami nutsuwa a rayuwarta. Ita kam sai son barka da yi musu addua.

Saura kwanaki biyar su tafi Zaria bikin Dijah. Umma da Anti Bintu basa zama kullum sai an fita siyayya saboda ana gama na Dijah da sati hudu za'ayi na Asmau.

Jikamshi yazo yiwa Asmau sallama tafiya ta kamashi Warri zaiyi sati uku. Zaune yake ya dora hannuwansa akan cinyarsa sannan ya tallabi fuskarsa dasu yana kallon Asmau. Kallon ya takurata tace "Jikamshina zan tashi fa idan baka dena kallona na ba"

"Tashi ki tafi ban hanaki ba. Amma ki sani zan je na sami 'yan matan Warri na kalla son raina"

A shagwabe tace "don Allah ko da wasa ka dena fadin haka. Kada kasa na kasa bacci yau"

"Shine kike son hanani baccin? Daga gobe fa zanyi sati uku ban sakaki a ido ba. Ji nake kamar a daura auren nan na tafi dake. Idan mun dawo sai ayi bikin, kada kice wani abu nasan kema haka kike so ko Matar Jikamshi" wannan lumshe idon yake mata. Ita kuwa ta soma dariya.

"Wane irin aure ne amarya da ango zasuyi tafiya bayan an dawo ayi biki."

Yace "to kawai idan mun dawo mu wuce gidanmu ko. Tsayawa bikin duk bata lokaci ne."

Dariya Asmau take yi kawai. Jikamshinta yau sai wani marairaicewa yake.
"Kada ka damu ni dama ba wani biki nake so ba. Zuwa za'ayi ayi ta kallona. Na fadawa Umma ayi komai a rana daya. Bayan daurin aure mata kadan su zo a kaini."

Col. Ishaq ya gane sarai dalilinta na yin haka. Yadda mata ke son biki amma tace bazatayi komai ba saboda surutun jamaa. Dena wasan yayi yace "Matar Jikamshi ko me kika yi na fada miki dole za'a sami masu magana. Bakiji ance Dan Adam mai wuyar gane hali ba. Idan kinyi biki ace baki da kunya ko makamancin haka, idan kin ki biki ace ko dan bikin nan batayi ba don kada mutane su je. A wurin Dan Adam bazaka taba fita ba. Saboda haka biki da akeyi abu na lokaci daya zukatan masoya suji dadi na makiya su fashe...."

Da har ta fara kwalla sai yanzu tayi dariya. Shima biye mata yayi.
"I am a soldier Matar Jikamshi. Dole nayi aure irin na sojoji. Su Safiyya suna can suna tsare tsare kamar yadda su Ainau suke yi. Zamuyi aure da biki kamar kowa kinji ko. Duk wanda ya fada miki mara dadi ki rinka tuna ranar asabar din da zaki tare a gidana. Ranar da Jikamshinki zai nuna miki matsayinki a rayuwarsa. Wannan ya isheki maganin duk wani bacin rai. Look forward to being Mrs Jikamshi a zahiri." Gyara zama yayi bayan ya gama maganar yana son ganin yanayinta. Kasa take kallo tana wannan murmushin da ta saba idan tana jin kunyarsa. Bai barta haka ba sai da ya tabbatar mata lallai bikinsu za'ayi taro kamar na kowa. Masu farinciki da 'yan saka ido kowa ana gayyatarsa. Addua zasu cigaba Allah Ya kare duk wani tashin hankali da abin ki har ayi a gama lafiya.

Da zai tafi Asmau harda kuka. Tana ta cika masa baki sati uku ba komai bane zata iya jurewa ko basu hadu ba akwai waya. Hoto ya rinka daukarta fuska a kumbure saboda kuka. Da ya shiga mota ya tayar tace "Jikamshina don Allah kada ka kalli kowace mace. Ai ni kadai na isheka ko?"

Ya murmusa "anya kuwa? A haka kinsan bazan tabbatar ba sai nan gaba. Idan rabon na hadu da kishiyar matar jikamshi ne a can sai ki tayani addua"

Ranta a bace ta zamo dankwalinta ta kasan mayafin da ta lullube kanta ta jefe shi dashi. Dariya yayi mata ya dauki dankwalin ya dora akan fuskarsa tare da rufe idanu. Muryarsa can kasa yace
"Ina son kamshinki"

Kunya taji ta mika masa hannu "don Allah ka bani"

"Haba yarinya, dama ba roka nayi ba kika bani. Yanzu kuma yazo kenan. In sha Allah ke dashi sai a gidanki. Love you, kiyi min adduar tafiya"

Tana kallo ya rataya dankwalin a wuyansa yaja mota kamar baya jin magiyar da take masa. Dafe kai tayi tana tunanin me zata ce idan aka tambayeta dankwalin. Tayi sa'a babu wanda ya kula. Kafin ta kwanta ya turo mata hotunansa ya ware dankwalin akan fuskarsa ya rungume da hannuwansa. Ranar har tayi bacci shi take tunani.

Da sassafe ta kira shi bayan sun gaisa tayi ta jero masa addu'o'in neman tsari da sa'ar tafiya. Dadi kamar me haka ya rinka ji yana saka mata albarka. Haka suka yi ta waya yana hanya har suka isa.
*****

Kwanci tashi sun je Zaria an sha biki lafiya. 'Yan uwansu na Wushishi sun zo sosai suna cewa saura zuwa Kano bikin Asmau. Bayan an kai amarya Kaduna da suka dawo da daddare kafin su kwanta Anti Bintu ta kirata dakinta. Ita dama bata je kai amarya ba kamar yadda al'adar bahaushe take. Wata jarka karama ta dauko ta bawa Asmau.

"Ga wannan zuma ce da aka yi mata hadi mai kyau. Kullum a kalla kisha cokali biyu. Kada ki sakata a gaba kiyi ta sha da yawa. A hankali zata ratsaki." Ta hado mata da wasu kullin magani duk na sha ne. Tace da kanta ta hadasu kayan amfanin jiki ne.

Tunda ta fara bayani kan Asmau a kasa. Da farko kunya take ji daga baya sai hawaye. Anti Bintu ta rude "menene kuma Asmau?"

"Anti yanzu a matsayin budurwa fa zanyi aure amma ....."

Fadawa tayi jikin Anti Bintu ta rungumeta tana kuka. Itama ta biye mata tana kukan tana rarrashi. Umma dake bakin kofa tana jinsu itama da nata hawayen. Babu wani abu a duniya da zasu bawa Asmau ya dawo mata da budurcinta. Shi kam idan ya tafi ya tafi kenan. Shiyasa ake so mata mu kiyaye. Kada ki sayar dashi a waje wasu suci kudinki da sunan zai dawo. Halittar Allah da 'yan dabaru na mutane basa taba zama daya.

"Ki dena kuka Asmau. Shima Ishaq din yasan komai ba yaudararsa kika yi ba. Amma dole ki gyara jikinki saboda rayuwar aure zakiyi yanzu. Ki cire yawan tunani don Allah. Bashi da fa'ida. Yawan kukan nan tamkar baki godewa Allah ba da ya ni'imtaki da samun masoyi. 'Yan mata da zawarawa nawa ke kwadayin irin wannan sai gashi ke Allah Ya kawo miki don Ya saukaka miki matsalolinki na baya."

Haka ta dauki jakar da magungunan jiki a sabule. Yadda 'yan mata ke rawar kafar shan magani idan bikinsu yazo sai gashi ita jin abin take kawai wani iri. Yanzu haka za'a daura auren budurwa mai 'ya. Allah abin godiya.
*****

Sun fi sati da dawowa Kano sannan Col. Ishaq ya dawo. Yana zuwa gida wanka kawai yayi tunda yayi sallah ko abinci ya kasa nutsuwa yaci ya fice. Hajiya ta girgiza kai, Allah Ya kara hada kawunansu su zauna lafiya.
Chapter 54 · 0% Book details