← Book details Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 74

Sashe 16

Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kin bani mamaki Asmau. Wannan wane irin text ne kike karantawa? Yanzu kwanciyar aure har sai wata can da baki sani ba ta koya miki? Wannan abu halitta ce wadda idan lokacin yinta yayi baka bukatar malami. Idan kuma har akayi rashin sa'a mace ko miji suka matsala ta fannin gamsar da juna to ba duniya zaki fadawa matsalarki ba. Mutum daya zaki samu cikin 'yan uwa ko abokan arziki wanda zaki iya bawa amanar sirrinki sai ki fadi matsalar a baki shawara. Amma me ya kaiki karanta irin wannan post din wanda ko matar aure ce ta karanta da wuya idan bai karya mata alwala ba saboda yadda ake bayani 6aro-6aro. Kada ki bari kawayen banza suce ya kamata a koya miki irin wannan tunda kin kusa aure. Komai yana da lokaci. Kodayake masu rubutawa sunfi kowa laifi tunda kayi rubutu ne baka san iya idanunwan da zasu karanta ba. Wayar nan yarinyar da bata fara jini ba ma tana da ita kuma akan same su a groups din manya suyi ta sakin baki a gaban 'ya'yan cikinsu. Wani lokacin sai su tura yara masu karfin sha'awa su karanta a tayar musu da hankali su fara neman mafita. Ki rufawa kanki asiri ki dena karanta abinda bazai amfaneki ba.

Abu na biyu wannan novels din da kike karantawa. Nima babarki ina karantawa amma ki sani akwai wanda har ki gama babu wani darasi da zaki dauka sai bata lokaci da tabarbarewar tarbiya. Uwa uba kuma wannan mugun son da muke yiwa labaran yana sawa mu manta da al'amuran da suka fi bukatar hankulanmu.

Tun zuwanki gidan nan na fuskanci kin canja sosai. Kina idar da sallah ko azkar baki gama ba sai ki janyo waya. Har akwai wani labari da zaisa ki kasa hakurin minti biyar ki bautawa Allah cikin nutsuwa? Mata irinki da yawa gasu nan. Sau nawa girki yake konewa ko mace ta yini cikin kazanta saboda karatun labari wanda a ciki tsafta da kula da miji ake koyarwa? Wata ma bata girkin akan lokaci sai taji mijinta ya kama kofar gida zai shigo ta ruga kicin. Wata ta bar yaro da kazanta har sai ta gama karatu. Wata kuwa da wayar zata shigo bandaki tana biyan bukatarta tana karanta labari. Idan hakane karatun labaran masu dauke da darussa bai amfanemu da komai ba sai kasala, ganda da kazanta.

Ki zama mace mai tsari a rayuwa komai kiyi shi a lokacin da ya dace. Babu abin takaici sai kinga mace da tsakar dare ko asubar fari tana cigiyar novel ga mijinta a gefe bawan Allah kila yaso ta bashi hakkinsa na aure ma amma ya hakura don kada ya takurata. Idan mara hakuri ne ayi ta samun sabani.

Asmau nasan Yaya Bara tana kokarinta a kanku. Gashi aiki yayi mata yawa duk don biya muku bukatu. Kada ki watsa mata kasa a ido da dabi'u marasa kyau kinji ko".

An tuno da Idon kuka ana mata fada tana sana'arta. A take tayi nadamar daukar shawarar Walida wanda yasa take yin abubuwan da a da can tasan basu dace ba. Kukanta ya tsananta da ta tuna tabbas irin yadda suke gudanar da soyayyarsu yanzu yana da alaka da canjin da ya fara tasowa daga gareta. Wai ita ce suke rungumar juna da Abubakar. Abubakar dinta mai riko da addini ta zama sanadiyar da suke munafuntar kawunansu da iyayensu.

Anti Bintu ta cigaba da yi mata nasiha mai ratsa zuciya sannan ta tashi. A ranar ta ga canji sosai a wurin 'yar tata. Asmaunta ta da ta dawo.
*****

Abubakar na kwance a daki yana kallon wasu hotunan Asmau. Tun daren jiya da ta turo ko baccin kirki ya kasa yi. Yau da ciwon mara ya tashi irin wanda ake samu idan sha'awa tayiwa mutum yawa. Ya rasa abinda yake masa dadi ko office ya kasa zuwa. Shawara ya yanke zaije Zariya a ranar ko dan yaya yayi dan abinda zai kwantar da kwadayinsa. A yadda yake sonta bazai iya neman wata matar a waje ba. Ita dinma bashi da niyar ayi mai gabadaya ta bakin Qasim. Dan dai abinda ba'a rasa ba yadda sai samu yaji dadi. Da wannan shawarar ya tashi yayi wanka ya hau shirin zuwa Zariya.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽17

Batul Mamman💖

Kafin ya fito ya kira Asmau a waya ya sanar da ita zai zo. Jikinta a sanyaye ta amsa masa don ita yanzu kunyar ganinsa take yi. Ko ba'a fada ba daga nasihar Anti Bintu tasan cewa duk abinda ya faru laifinta ne.

Har daki taje ta sanar da Anti Bintun zai zo kamar yadda ta saba.
"Ki dora abinci dashi amma ki bar dan waken sai gobe don bazan bawa suriki dan wake ba"

Ita da Asmau duk dariya sukayi sannan ta wuce ta dora shinkafa da miya.

Wuraren karfe uku ya iso Anti Bintu tazo suka gaisa sannan ta basu wuri.

Yau Asmau hijab ta saka dogo har kasa fuskarta babu kwalliya sai hoda da kwalli. Jikinta duk babu kwari tayi nadama sosai. Abubakar kuwa tamkar ya hadiyeta da kallo. Anyi sa'a yaran gidan suna ta gilmawa a falon. Da laasar suka tafi islamiyya shi kuma yaje yayi sallah.

Ana idarwa ya dawo ya kalli Asmau dake zaune a can gefe.
"Asmy dawo nan kusa dani nafi jindadi". Ya nuna kujerar gefensa.

Tashi tayi kamar wadda kwai ya fashewa a ciki. Tana zama ya kama hannunta ya rike yana lumshe idanu. Can kasa take jin muryarsa
"I love you so much Asmy. Ina ma anyi aurenmu kiga irin abinda nake nufi."

A kwanakin baya har so take ya rike mata hannu amma yau sai taji ta tsani hakan. Tana son nuna masa kuskuren abinda tasan ya fita sani amma dole tabi lamarin a hankali kada yayi mata mummunar fahimta ko yace ta mayar dashi dan iska.

Har lokacin tafiyarsa yayi bata iya sakin jiki dashi ba. Shi kuwa gabadaya ya kasa samun nutsuwa. Bakin motarsa da ya ajiye a wajen gate ta raka shi ai kuwa yana bude motar ya rungumota jikinsa. Dama layin ba mutane sosai saboda unguwar bata gama cika ba ga duhun dare.

Wasu hawaye masu zafi Asmau taji sun taho mata ta hadiye. Dole ta sami lokaci suyi magana da Abubakar akan wannan abin. Rungumar da take jindadi daga gareshi yau bata so. Tana wannan tunanin taji yayi mata abinda bai taba yi ba. Abinda take ta mararin faruwarsa. Bakinsa ya hada da nata yayi mata rikon da bazata iya kwatar kanta ba koda tayi niyya.

Hawayen da take boyewa ne suka sakko ganin Abubakar tamkar baya cikin hayyacinsa. Abubuwan da yake mata sun fara wuce gona da iri. Ba shi ya saketa ba sai da don kansa yaji hankalinsa ya fara dawowa gareshi.

Ganin tana kuka ya soma bata hakuri.
"Asmy kiyi hakuri please. Na rasa dalilin da yasa nayi miki hakan. Ki sani ina sonki tsakani da Allah kuma in sha Allah bazan sake kwatanta miki haka ba sai munyi aure".

Yadda yake maganar sai ya bawa mutum tausayi. Tabbas baya son abinda yake yi sai dai karfin sha'awarsa da tsananin rudin shaidan yasa ya kasa hakuri.

A hankali ta share idonta "Yaya Abubakar don Allah mu dena irin wannan abin kaga babu kyau."

"Na sami Asmy, ni kaina na rasa gane yadda akayi muka fada ga wannan masifar. Ki share idonki kinji matar Abubakar".

Kafin ya tafi sai gashi ta sake sosai hankalinta ya kwanta. Suka rabu zuciyar kowa tana nata sake saken.
*****

Abubuwan da suka gudana tsakanin Abubakar da Asmau su suka rinka yi masa yawo a kwakwalwa. Yayi tunanin zaiji saukin sha'awar dake damunsa sai abin yayi tsanani sosai. Kullum cikin mafarkinta yake yi. Baccin kirki ya gagare shi sai tunanin yadda zaiyi ko dai a matso da aurensu ko ya kashe yunwarsa ko sau daya ne.

A nata bangaren hatta hirar da suke yi a waya yanzu tana kame bakinta daga hirar da bata dace ba. Ta tarkarta tunaninta kaf zuwa lokacin aurensu ko sa sami nutsuwa da kwanciyar hankali saboda tasan duk su biyun yanzu a matse suke da ganin wannan lokacin.

Bayan kwana biyu ya sake zuwa wannan karon ko waya baiyi mata ba. A hirarsu da Anti Bintu ya nemi izinin ranar asabar da Asmau zata tafi zai zo ya kaita da kansa a cewarsa baya so ta shiga motar haya.

Anti Bintu tayi shiru na dan lokaci saboda ba haka sukayi da yayarta ba. Dama tasha za'a kaita ta tafi saboda motar Kawu Yusuf tana gareji wurin makanike. A duk dan tunaninta bata hango wata matsala ba duba da irin siffa ta kamala da suke dashi su biyun.

Asmau kanta bata ji komai ba saboda yau hirarsu duk irin ta da ce. Cikin nutsuwa da kiyayewa. Soyayya mai tsafta irin wadda masu yinta basa son rabuwa da juna.

Kwanaki ukun da suka zo kafin tafiyarsu Abubakar yaji babu dadi. Har wani zazzabi ne ya kamashi saboda ji yake tamkar ana hura masa wutar sha'awar kasancewa da mace. A yadda yake ji ko ba Asmau bace wannan karon zai iya nema.

Ranar da zasu tafi wurin karfe goma ya iso. Asmau da yaran harda dan kukansu na rabuwa.

Suna mota ita da Abubakar babu wata hirar kirki don basu taba kadaicewa a mota haka ba na tafiya mai nisa.

Hanyar cikin gari ya nufa ya kashe motar a gefen titi. Asmau ta kalle shi zata yi magana sai ta kasa ganin idanunsa sunyi wani iri kamar wanda yake cikin tashin hankali.

A raunane yake dubanta har sai da tsigar jikinta ta tashi don tsoro da ya dora hannunsa a kan nata.

"Asmau"

Yaushe rabon da ya kirata da sunanta haka. Gabanta na dukan uku-uku ta amsa.

"Idan na rokeki alfarma zaki yi min?"

Ita fa Yaya Abubakar tsoro yake bata da yanayinsa na yau.
"in sha Allahu idan baifi karfina ba".

Gwauron numfashi ya ja.
"Asmy ina cikin matsala kuma ke kadai ce zaki iya yi min maganinta. Ko sati ba'ayi ba da muka amince mun dena taba jikin juna.."

Bugun zuciyarta ne ya karu tana ganin kamar ta fara fahimtar inda zancensa ya dosa.

"Ni mutum ne mai yawan bukata, ina tsammanin baki san me hakan yake nufi ba."
Chapter 16 · 0% Book details