← Book details Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 74

Sashe 30

Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asmau dai kashe wayarta tayi sai tayi kamar ta saka katin guda daya sannan ta tashi ta koma gefe kamar tana waya don karfin hali harda kwatancen asibitin.

Bata san duk abinda take yi Soja na kallonta ba. Mamaki ne ya kama shi da ya fuskanci me take yi. Tana juyowa suka hada ido yayi mata wani irin kallo. Babu shiri ta sauke nata idon ta basar duk da idanunsa sun tsorata ta.

Hajiya ta tashi "to mu zamu tafi ni sunana Hajiya Lubabatu wannan jikata ce."

Bilkisu na dariya tace "Uncle kuma dan fari da ba'a fadar sunansa"

Ya kai hannu zai rankwasheta "Hajiyar tawa kike tsokana ko. Hajiyata kyaleni da wannan yarinyar zan miki maganinta."

Kana ganin Haj Lubabatu kunya take ji bata son wasa da dan nata.

Asmau tayi murmushi tace "ni sunana Asmau. Nagode sosai Hajiya Allah Ya saka muku da mafificin alkhairi"

"Amin, gobe in sha Allah zamu dawo don nasan dakyar a sallameku. Idan mutan gidan sun zo ki gaishesu"

Asmau tace to ta tashi zata rakasu Haj Lubabatu ta dan tsaya ta dauko wayarta daga jaka ta mikawa Bilkisu "bani numbarki saboda kira ko da akwai wani abu."

Duk da ta gode da taimakon da matar nan tayi mata amma bata so alakar tayi tsaho. So take yi ta koma gida asirinta a rufe. Yanzu da Amatullah babu lafiya dai bazata iya tafiya ba don bata san yaya zasu tarbeta ba, bai kamata taje musu da lalurar 'yar da suka so a zubar da cikinta ba. Number kawai ta kirkira da ka ta karanto Bilkisu ta kwafa a wayar Hajiya.

Hajiya sai sake cewa tayi "yauwa to kirata sai ta samu tawa numbar a wayarta ko."

Ji tayi cikinta ya murda kada asirinta ya tono. Sa'arta daya ta kashe wayar tace "wayar ta mutu yanzu amma zan saka chaji idan an kawo wuta"

Haj Lubabatu tayi murmushi "to babu komai. Ga abinci nan ki tabbatar kin bata yanzu. Safinatu Allah Ya baki lafiya kinji".

Daga haka Haj Lubabatu ta fita Asmau na binta da sakon addua. Shima dan nata zai fita Amatullah ta dage shi zai bata abinci ba Umminta ba. Da murmushi a fuskarsa yace mata yanzu zai dawo ba nisa zaiyi ba. Yana dago kai Asmau ya gani tana kallonsa don tabbatar da abinda yace. Wannan karon murmushin da yayi mata mai nuni da ta kiyayi dawowarsa sannan ya fita. Ai kuwa ta hau Amatullah da fada akan me zata ce ya bata abinci. Yarinya ta bare baki tana kuka, takaici duk ya ishi Asmau don ta tabbatar zai dawo tunda ya sake barin wayarsa.
*****

Har bakin mota ya raka su Hajiya tana tambayarsa yaushe zai tafi gida yace yana son lallaba yarinyar nan ne saboda kada tayiwa mamanta rigima.

Haj Lubabatu tace "Allah Sarki ai nima ta bani tausayi. Karshenta tana yarinya sosai uban ya rasu shiyasa ta damu da ganinsa yanzu. Nasan dole hakan ya rinka dagawa babarta hankali."

"Nima haka kawai naji ta shiga raina Hajiya"

Da alamun tausayi a fuskarta tace "ai na sani, kai da son yara kuma. Bari mu wuce sai ka dawo"
Bai bar wurin ba har sai da motar ta fita daga gate din asibitin sannan ya koma ciki. Hankalinsa sam bai kwanta da Asmau ba. Yana tunanin ko dai irin matan nan ne masu damfara ko kuma tana da sirrin da bata so a sani.
*****

Amatullah sai kuka take yi saboda irin fadan da Asmau take yi mata.
"Idan baki rufe min baki ba nida ke ne. Haka kawai daga ganin mutum sai ki dage shine babanki. To nan ba aljannah bane kuma na fada miki yana can. Bude bakinki ki karbi abincin...."

Sallamarsa ta sake ji cikin muryar da ta gama ganewa yanzu. Amatullah na ganinsa ta matsa daga kusa da Asmau har allurar da ake yi mata karin ruwa ta soketa ta tsala ihu. Kukanta yaji har ransa ya matsa da sauri ya gyara mata ya bi Asmau da harara, ita kuwa ta matsa gefe rai a bace.
Rarrashin Amatullah yayi sannan ya bata abincin kamar ba soja ba ya mayar da kansa yaro a gabanta. Ko sau daya bai yiwa Asmau magana ba har sai da Amatullah tayi bacci sannan ya tashi.

Wayarsa ya miko mata fuskarsa babu alamun wasa ta dan ja da baya.
"Karbi mana, numbarki zaki saka min"

Tayi kicin kicin da fuska
"Na bawa Hajiya"

"Na sani, ina son karba saboda na kira 'yata anjima".

"Da ka barshi ma, saurin mantuwa gareta kana fita zata mantaka"

Ya dan daga gira "ke kadai kike son faruwar hakan banda ni da ita. Nasan bazata manta ni ba."

Duk da haka Asmau taki karbar wayar tana adduar ya fita kawai. Tunda an biya musu kudin asibitin ba yau ta fara ba, guduwa zatayi idan dare yayi.

Ya tsareta da ido "na fa san ba numbar daidai kika bawa Hajiya ba. Kuma nasan baki kira kowa ba dazu. So ki bani numbar tun girma da arziki kafin na fara bincike a kanki."

Duk da ta tsorata harararsa tayi tana magana a dan tsorace
"A wane dalili zaka yi bincike a kaina? Daga taimako, dole ne na bada number?"

Yadda ya kalleta yasa tayi shiru. Wayarta ya dauka daga kusa da Amatullah ya kunna sannan ya saka numbarsa ya kira tasa wayar.

Mayar da wayar yayi inda take ya kama hanyar fita "saura kuma kiyi tunanin cire sim din. Na bar sojoji biyu zasuyi min gadin 'yata don kada ki gudu cikin dare".

Gabanta sai da ya fadi da ya fadi haka. Ji tayi kamar yana karanta abinda ke ranta. Ba'a fi minti biyar da fitarsa ba taji wayarta na kara. Da sauri ta dauko a tunaninta Zulaiha ce sai ta sake jin muryarsa.
"Baban Safina ne, Colonel Ishaq Muhammad Jikamshi. Na bugo ne don na tabbatar baki cire sim din ba." Bai jira tayi magana ba ya kashe wayar yaja motarsa yayi gaba.

Asmau ta tsaya tana kallon wayar cike da mamaki. Tsoro ne ya kamata don da gaske ta yarda ya bar masu tsaronta kada ta fita su bindigeta a banza. A hankali ta sake maimaita sunan nasa. Dama a jikin rigarsa ta ga inda aka rubuta I.M Jikamshi.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽30

Batul Mamman💖

Sau biyu Asmau na leka waje amma bata ga soja ko daya ba. Ga tsoro kada sai ta fita su tsareta. Haka nan ta hakura zata zauna don dole. Dadin dadawa tana so Amatullah ta kara samun sauki.

Sallah tayi ta ci abinci itama sannan ta saka kati daya a wayar ta kira Zulaiha ta fada mata inda suke. Sauran ukun kamata yayi ta sayar dasu ta fada a ranta.
****

Col. Ishaq gidansa ya wuce dake Tudun yola. Gidan da a yanzu baya son zama cikinsa saboda abubuwa da dama da yake tuna masa dasu. Dakinsa ya shiga ya dauko wasu takardu ya jira akayi har sallar isha sannan ya tafi gidan Hajiyarsa.

Babu kowa a falon lokacin da ya shiga shiyasa ya wuce dakin kaninsa wanda yayi aure kwanakin baya inda yanzu ya mayar nasa. Yayi wanka ya saka kananan kaya sannan ya hau gado ya kwanta. Tunanin Amatullah yake yi yana dan murmushi. Yarinyar ta tsaya masa a rai. Sai kuma ya koma tunanin mamanta. Ji yayi yana son sanin ko ita wace ce. Tunani kala kala ya rinka yi game da ita. Da ya gaji wayarsa ya dauko yana karanta sakonnin da aka turo masa wasu ya share wasu ya bada amsa.

Sunan da baiyi tunanin gani bane ya dauki hankalinsa da sauri ya bude sakon. Sallama tayi masa sai hoton baby da ya biyo baya. A kasan hoton ta rubuta _Alhamdulillah mun sami baby boy_.
Da kyar Ishaq ya iya hadiyar yawu don tashin hankalin da ya tsinci kansa a ciki. Har wani guntun zazzabi ne ya nemi rufe shi. Ya tashi ya fita zai je wurin Hajiya a daki sai yaji muryarta a falo.

Labarai take kallo ita kuma Bilkisu tana zaune a kasa suna hirar sanyin Jos da mai aikin gidan Hinde. Motsinsa yasa Hajiya kallon kofa tace "yaushe ka shigo gidan ban sani ba?"

"Dazu ne bayan Isha"
Ya zauna akan kujerar kusa da ita tare da mika mata wayar. "Kin gani Badar ta haihu"

Hajiya ta kalli su Bilkisu "ku dan bamu wuri"

Tashi suka yi Bilkisu sai da ta waiwayo ta kalli Kawunta tana mai tausaya masa.

Bayan sun wuce Hajiya ta karbi wayar ta kalli hoton jaririn tayi guntun murmushi "Allah Ya raya" ta gyara zama sosai tana fuskance shi
"Mai sunan Alhaji, nasan irin damuwar da kake ciki amma ina so ka sani ba'a yiwa Allah dole. Duk yadda kaso Allah bai nufa zaku kare rayuwarku da Badariyya ba. Duk kuma yadda kuka nemi haihuwa kasan wani baya haifar dan wani."

Kansa a kasa yace "na sani Hajiya. Yanzu na tabbatar mun rabu har abada kuma kamar yadda Mami take yawan fada ya tabbata nine bana haihuwa" a yadda yake ji a wannan lokacin gara yayi kuka ko zaiji sauki a ransa. Tausayi ya bata sosai.
"A matsayinka na musulmi ka sani cewa babu abinda bawa zai samu a rayuwarsa sai wanda Allah Ya kaddara masa. A bisa tsari da hikimarSa *Yake azurta wasu da 'ya'ya mata, wasu da 'ya'ya maza, wasu Ya hada musu duka biyun, wasu kuma Ya barsu haka* duk inda Allah Ya jarabceka da fadawa kasan babu wayo ko dabararka. Ka zama mai hakuri wata rana zaka ci ribarsa".

Ajiyar zuciya yayi ya gamsu da bayananta wanda ya sani dama.
"Nagode Hajiya, bari naje na kwanta"

"Abinci fa"

"Bana jin yunwa. Sai da safe"

Tasan halin da zai shiga kenan shiyasa tun tana Jos shekaranjiya da maman Badariyya tayi mata waya ta sanar da ita haihuwar bata fada masa ba.

*****
Sake kwanciya yayi yana tuno rayuwarsa ta baya. Auren soyayya suka yi da Badariyya suna zamansu lafiya. Har suka shekara biyu da aure ko batan wata bata taba yi ba. Gashi Allah Yayi shi da son haihuwa tun bata fara damuwa ba ya matsa su je asibiti. An duba su aka tabbatar musu duk lafiyarsu kalau su jira lokaci.
Chapter 30 · 0% Book details