← Book details Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 74

Sashe 10

Abinda Ake Gudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tare suka dawo har da Suwaiba dauke da irin filtilar nan mai batir. A kwancen dai suka same shi ya hada gumi idanunsa harda hawaye. Mama ta daga kansa ta dora a cinyarta a rude tace "ina inhaler dinka?"
Aljihunsa yayi kokarin nuna mata. Tasa hannu ta dauko ta shaka masa. Asmau da Suwaiba suna tsaye suna yi masa sannu.

Duk da haka numfashin bai dawo daidai ba. Mama tace a fadawa dreba yazo su tafi asibiti. Bayan fitarsu Asmau ta tafi gida ta sanar da Umma abinda ya faru.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽11

Batul Mamman💖

Rabe ne ya fito yasha sabuwar shadda sai kyalli take yi. Idonsa a kan Bara'atu da yanayin da ta shiga yayi dariyar mugunta. Don tsabar wulakanci yace
"A'a bazawara kune a garin? Ya hanya?"

Hawaye take yi wani na bin wani ta durkusa a gaban Hajjo
"Nasan har mijina ya rasu baku taba kaunata ba amma Hajjo wallahi cin dukiyar marayu haramun ne. Gidan nan baku da hakki a kansa to a wane dalili zaku zo ku tare batare da izini ba".

"Eh, lallai wuyanki ya isa yanka Bara'atu. Ni da gidan dana kike gaya min maganar banza." Hajjo ta amsa itama rai a bace.

"Ko kinki ko kinso zama dole muyi a gidan nan. Idan bazaki iya zama damu ba sai ki bar min yaran ki kama gabanki."

Yusuf mijin Anti Bintu yace "Anti kada ki sake cewa komai. Ai basu fi karfin hukuma ba. Kuma rabon gado ba hauka bane. Ki bari mu kwana yau gobe sai mu san abinyi."

Mikewa tayi cikin zafin nama tana kallonsu daidai. Garzali banda taba babu abinda yake busawa. Rabe da amaryarsa suna tsaye suna mata kallon banza. Hannu tasa ta share hawayenta
"Dama can saboda marigayi nake raga muku to amma wallahi yanzu an wuce wurin. Mu zuba ni daku shege ka fasa."

Yaranta ta dakawa tsawa duk suka tashi daga gaban Hajjo suka bita cikin gidan.

Hajjo da su Rabe kowa yayi tsit suna mamakin wai yau Bara'atu ke mayar musu da martani haka.
*****

A cikin gidan dakuna biyu ta samu a bude ita da Yusuf da su Shemau suka rinka shiga da kayansu. Sai cikin dare tana zaune tana kallon 'ya'yanta na bacci ta rinka kuka.

Washegari ko karyawa batayi ba suka fito ita da yaran suka hadu da Yusuf zasu tafi ofishin 'yan sanda.

Rabe yana tsaye a waje yace " kinga basai kun wahala ba a bayan layin nan akwai gidan wani babban dan sanda. Maza ku tafi ku kai kara kada kuda ya rigaku."

Basu kula shi ba suka wuce. Duk wani bayani sun gabatarwa 'yan sandan. Mutum hudu aka hado su dasu suka zo aka bukaci su Rabe su fita.

Wannan muguwar dariyar yake yi ya dauko takardun gida sai gashi sunansa ne dana Shu'aibu a jiki a matsayin tare suka gina.

Kuka sosai Bara'atu take yi tana karyata shi. Sai dai kuma bata da shaida. Bata san yadda akayi ya sami takardun gidan ba wanda a hannunta suke har akayi canje canje haka.

Dole 'yan sanda suka tafi domin basu da wata shaida.

Yusuf ya nemi ta bishi su koma Zaria daga nan ta koma garinsu da zama.

Tana kuka tace "ko zasu kashemu babu inda zamu je. Gidan nan namu ne kuma duk rintse sai ya dawo hannun masu shi."

Babu yadda Yusuf ya iya dole ya tafi ya barta. A dakin kwanansu ta sayi risho mai kai biyu da kayan abinci. Kullum suna daki tana saka yadda zata bullo musu.

A karshen sati ne abokan marigayi biyu suka zo. Anyi ta kai ruwa rana Hajjo da Rabe da sauran 'ya'yan gidan suka hade musu kai. Magana dai har wurin dan sandan dake bayan layinsu, Adamu Matawalle ashe abokin daya daga cikinsu ne. Shima ya gamsu da bayanansu sai dai ga shaida kurukuru suna gani gida na Rabe da Shu'aibu ne. Shawara suka bata akan ta koma gida kawai tace babu inda zata je.

Wani katon fili wanda gida daya ne tsakaninsa da gidan dan sandan ta nuna musu. Rabi nata ne ta siya da kudin kasuwancinta daya rabin kuma Shu'aibu ne ya siya mata. Takardun ta bawa dan sandan ta roke shi ya rike mata amana zata gina kayanta a hankali sannan su tashi daga can gidan. Duk ta basu tausayi. Wani cikinsu ne yayi cuku-cukun nema mata aiki a kamfanin sadarwa na MTN , duk wannan abu batare da sanin su Rabe ba. Tayi musu godiya kamar ta ari baki.

Cikin dan lokaci ta saba da iyalin Adamu sai dai kullum a gida take barin 'ya'yanta idan zata je wurinsu. Tana tsoron surutun yara kada su fada a gidan. Makaranta ta samar musu a nan cikin unguwa. Saboda yanayin aikinta ta koyawa Shemau da Jafar girki ko da bata dawo da wuri ba. Zagi da surutu har su Hajjo sun gaji da yi wai tana yawon bariki. Bata kula su ba sai dai bata bari 'ya'yanta sun raina kakarsu ba.

Wata rana ta fito suna sauri zata kai yara makaranta ta wuce wurin aiki ta nemi motarta bata gani ba. Rai a bace ta koma ciki ta tambayi Sagira. Sai da ta gama yaukinta sannan tace ban sani ba. Itama Hajjo amsar data bata kenan.

Tasan aikin Rabe ne sai tayi kamar ta hakura. Har wani gadara yake yi yana cewa motarsa. Na tsawon sati biyu ta dauke kanta daga kan motar sai dai a bayan idonsa ta sami wani abokin aikinta ya samo mai siya.

Ranar Juma'a Rabe na kwance a daki mai siya yazo yaga mota aka gama ciniki ta bashi mota da takardunta. Shi kuma yayi alkawarin kawo kudin ranar litinin.

Sam Rabe bai san me ake ciki ba sai washegari ya gama shirin zuwa daurin aure. Ganin babu motar kuma yasan Bara'atu nada mukulli ya tafi kofar dakinta yana ta bugu iya karfinsa. Yaranta duk bacci suke yi ta fito da dogon hijab a jikinta tana murmushi don tasan me ya kawo shi.

"kinga ba wasa bane ya kawoni ina kika kai min mota"?

"Hmmm, karfin hali barawo da sallama." Ta fada tana tafa hannuwa.

Hajjo da Sagira suka fito suka sakata a gaba.

Bara'atu ta yatsina fuska "mota dai tawa ce kuma na sayar na cinye kudin. Shikenan ko."

Ran Rabe a bace ya zabga mata mari. Hajjo tace kayi min daidai.
Bai ankara ba Bara'atu ta kwashe shi da mari shima tana harararsa.

"Dani daku a gidan nan daga yau an shata layin rashin mutumci. Na gaji na kai wuya duk abinda zakuyi kuyi. Banda rashin tsoron Allah komai na gado sai mun raba ni daku? To mota dai tawa ce ni kadai"
Tsaki taja ta shige dakin ta banko kofa.

Hajjo ta kalli Rabe a dan tsorace." Anya yarinyar nan bata shan kwaya kuwa? Kada tasa a koremu fa."

Rabe ya dafe kunci "barni da ita Hajjo sai na nuna mata bata da wayo". Sai dai har kasan ransa bazai iya ba saboda son da yake mata.

Haka suka cigaba da zaman doya da manja a gidan. Tsakanin Bara'atu da su sai kallo. Yaranta kuwa ta wajabta musu zuwa gaishe da Hajjo safe da dare duk da bata amsawa. A haka har suka shekara daya da rabi tana ta gininta a hankali, sannan duk da tana aiki bata dena kasuwanci ba.

Wata ranar lahadi tana daki ta jiyo hayaniya a falo. Yaya Abu ce da Lami suka zo yini da 'ya'yansu. Su Shemau na son zuwa wurin sauran yaran suna tsoron Ummansu. Murmushi tayi tace su je amma banda tsokana.

Da gudu suka fice tunda da sauran kuruciya basu gama bambamce masu sonsu ba. Iyayen dai babu wanda ya amsa musu gaisuwa da 'yan uwansu yara suke ta wasa.

Kamilu babban dan Yaya Abu ne ya shigo ya soma rungumar kannensa kamar yadda ya saba. Yana rungume da Shema'u yana tsokanarta Bara'atu ta fito idonta ya fada kansu. Mantawa tayi da mutane a wurin tace
"Kamilu wane irin wasa ne wannan? Shema'u ban hanaki wannan rungume rungumen ba?"

Dena hirar su Hajjo suka yi suka tsaya kallon Bara'atu tana yiwa dansu fada.

Lami ta watso mata harara "To kinibabbiya kin fito ne ki fara rashin da'ar taki? Menene aibu don ya taba kanwarsa, yaro da muharramarsa ma sai an nuna musu iyawa" mtws.

"Bani da matsala don Kamilu ya taba kanwarsa sai dai Shema'u ba muharramarsa bace shiyasa na hana. Daga shi har ita babu karamin yaron da ba'a budewa littafi ba".

"Ya Sayyada manya....indai Yaya Shu'aibu ne uban Shemau to baki isa ki rabata da Kamilu ba domin kuwa iyayensu uwa daya uba daya suke. Kinga sun zama muharraman juna".

Kallon Lami kawai Bara'atu tayi ta girgiza kai zata koma ciki Hajjo ta dakatar da ita.
"Sai kin fada min dalilin son raba min kan jikoki tunda kin gama fetsare kafafunki".

"Hajjo ni ba rashin kunya nazo yi miki ba. Wannan abu ba fadata bace. Da yawa mutane muna jahiltar abinda ake nufi da muharrami. A musulunce duk mutumin da ko ku kadai kuka rage a duniya aure ya haramta tsakaninku shine muharrami."

Yaya Abu tace "to ina kuma alakar jini da take tsakaninsu? Ita kuma an datse ta kenan?"
Chapter 10 · 0% Book details